← Book details Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 61

Sashe 23

Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwana uku ya d'auka yake shigowa yi mata allura sau biyu a rana.
duk sanda yazo da kuka ake karewa, idan ya shammaceta sai dai taji shigar allura jikinta, idan kuma ta ankare haka zai matseta sai ya mata.
sannan ya saketa yayi tafiyarsa.
zuwa lokacin jikin ta ya warware sosai.
tun da yayi kwanaki uku yana shigowa yi mata allura kuwa bai kara shigowa ba.
har ta cika sati guda a sashin Aunty.
a ranar da ta cika satin ya shigo da daddare, suna tare da Aunty, fitowarta daga wanka kenan, tana zaune a kan gado d'aure da towel,
tana cin cake d'in da Aunty ta kawo mata.
Aunty na ganin sa ta mike ta fita bayan ta amsa gaisuwar da ya mata, kansa a kasa.
Feeryal ko fuska ta kwab'e tana kokarin zamowa bakin gado tagudu taji ya ruko hannunta.
ya maida ita.
murya na rawa ta ce
"Ni bana so kar kayi min allura."
"Ki natsu na gani idan ba haka ba allurai goma zan baki yanzu."
yayi maganar yana gimtse fuska.
yana tsaye daga bakin gadon ya turata ta kwanta da baya.
kana ya sa hannu guda yad'an danna ta ta inda bazata iya tashi ba, d'aya hannunsa kuma ya kamo kasan towel d'in jikinta yayi sama da shi.
wani irin zabura tayi, da sauri ya kuma danneta yana fad'in
"Wait, don't argue with me."
ido ta waro da karfi ta rirrike hannunsa tana fad'in.
"Aa Sahab dan Allah karka yi min wayyo Ammieee."
ta karasa da kiran Aunty da karfi.
yatsa ya d'aura kan lips d'in sa tare gimtse fuska sosai murya ba wasa ya furta
"Shut up Stupid!."
hannu takai ta to she bakin ta jikinta na rawa ta rumtse idanunta da karfi tana jin yadda yadad'a rirriketa yake ware kafafunta.
ya kunna flash d'in wayarsa ya haska hole d'in ta.
d'inkin yayi kyau saura kad'an gurin yagama warkewa.
da sauri ya janye idanunsa da yake jin suna wani irin fisga numfashin sa yana fita da sauri-sauri.
ya ja towel d'in ya rufe gurin. kana ya juya ya fice da sauri.
tana jin fitarsa ta juya takifa fuskarta jikin katifa takasa iya bud'e idanunta bare ta mike......!

Tun da yazo yaga d'inkin bai kara zuwa ba.
ranar da ta cika kwanan goma Daddy ya umurci Aunty ta mai da ita d'akin ta.
tun da Feeryal ta sami labari hankalin ta ya tashi.
tayi ta kuka tana fad'in ita bazata koma ba.
Aunty ta sata gaba tayi ta rarrashi.
da misalin karfe 8 na dare Aunty ta sako ta gaba bayan ta sha fama da rarrashi.
ta kaita har d'akin ta, da kyar Aunty ta zame jiki ta koma nata sashin, dan kuka Feeryal ta saka mata, shigowar su bedroom d'in ta.
gaba d'aya d'akin mugun tsoro ya bata,
dan nan take ta tuna da irin azabar da ta sha a cikin sa.
ta rab'e bakin gado ta rakub'e guri guda, ta rumtse idanunta da karfi bata son ta rika tunawa da abun da ya faru.

Motar Abdulrahim ne yayi hon a babban get d'in gidan.
security suka bud'e masa, yana sako hancin motar ciki kiran Mommy na shigowa wayarsa.
dan haka a babban parking lot d'in gidan ya paka motar ya fito ya nufi sashin ta.
yana shiga ko zama bata bari yayi ba, ta rufe shi da bala'i
"Nayima zuru na zuba ma ido naga gudun ruwan ka kai bakasan zuru ba ko,
tome kake jira har yanzu baka saki yarinyar can ba,
an mai da maka ita yau sabo da har yanzu burinsu bai cika ba,
an maida ita ta karasa aikin da bata kammala ba,
bokan su ya basu sa'a, sai sun ga bayanka kafin su hakura,
to ni ce nan na haife ka,
wato ni ban isa da kai ba ban isa nace ma ga abun da yakamata kayi ba,
uban ka ne kad'ai ya isa ya saka ya hanaka, ni uwar data rike cikin ka tsowon wantinni tara, nayi fad'i tashi babu kalar wahalar da ban sha a rike cikinka zuwa haihuwar ka da rainon ka har ka mallaki hankalin kanka ba,
amma ni ce na zamo banza ban isa na tsarama rayuwar da ta kamata da kai ba, sai ka bijere min,
sabo da ban isa da kai ba, na haifawa Hajiya Fatima da mayyar aljanar ruwa kai,
wato duk abun da na fad'a ma kan yarinyar nan baka ji ba sai da ka kusance ta,
wani jaraba ne zai kai ka ga wannan yarinyar?, to wlh ina mai tabbatar maka ni banshirya had'a jini da aljanu ba, tun da jarabarta ya kamaka tun marmaza kaje ka yi mata implant wlh bazaka tab'a had'a jini da ita ba,
sai nabi ta inda Hajiya Fatima ta bi na karya duk asirin da ta maka, bazata mallake ubanka ta mallakeka ba, ban haifa mata kai ba wlh,
tun marmaza kaje ka mata implant,
idan kuma bakayi abun da nace ba to ban yafe ba duniya da lahira."
yana tsaye ya kalmashe hannu a kirji, bai furta ko kalma d'aya ba,
ganin ta gama maganar ta yajuya ya fita.
yana jiyo ta tana kuma fad'in
"Ni dai na gaya maka idan bakayi abun da nace ba, Allah ya isa ban yafe ba,
yanzu kaje kayi mata idan ka bari gari ya waye ma ban yafe ba, kaji na gaya maka ke nan."

Yana shiga Bedroom d'in sa ya rage kayan jikin sa, ya shige bathroom yayi wanka yafito ya saka gajeren wando da singlet ya haye gado.
ya janyo laptop nasa.
11 ya rufe laptop d'in yayi addu'a ya kwanta.
idanunsa a lumshe maganganun Mommy suka shiga amo cikin kwakwalwa da kunnuwan sa.
gefen lips d'in sa ya taune, kana ya mike zaune ya zamo bakin gadon, yaja drowa yad'an bincika yad'au abun da yake bukata ya fito ya nufi gefen ta.
a hankali ya turo kofar, tana rakub'e a haka bacci ya d'auke ta.
a sannu ya tako cikin d'akin, ya iso bakin gadon.
ido ya d'an zuba mata idanunta a lumshe tana sauke numfashi a hankali, sai dai da kaga baccin zakasan a cikin tsoro tayi shi.
tsayuwar sa ya gyara sannun ya d'an rankwafo kanta, yad'an jan rigarta batare da yaja wandon baccin jikin ta kasa ba ya nitsa allurar dake rike a hannunsa ta saman wandon ta.
wani irin zabura tayi yayi saurin matse suwan allurar a jikin ta kana ya zare.
hannu takai ta dafe gefen mazaunnan ta tana ja da baya tare da binsa da kallon tsoro,
da kyawawan idanunta da suka cika tab da kwalla har suna walkiya.
idanunsa a kanta gaba d'aya ta daburce sai yarfe hannu take, d'aya hannunta kuma na dafe da inda ya mata allurar.
kai ya d'auke yana mai gimtse fuska, kana ya juya ya fice a dakin.
yana fita ta mike da sauri ta duro a gadon wani irin jiri me kamada bacci taji ya d'ibeta,
ba shiri ta koma ta zube kan gado kafafunta yana rito a kasa, a take idanunta ya rufe bacci ya yi gaba da ita.
20min da faruwan haka ya shigo.
ya gyara mata kwanciyarta kana ya zauna bakin gadon, yaja hannun rigarta zuwa can saman kafad'ar ta, sannan ya mata allura a in da ya dace daya sa mata implant d'in, mintuna kalilan ya d'auke sa ya saka mata sannan ya kwashi abubuwan da yayi amfani da su ya fita yaja mata kofar.

Daddy da Abbie da Dad ne zau ne a parlour Hajiya.
Daddy na rike da waya a kunnen sa yana magana
"Kun bincika ko wani club da hotel baya can?."
daga cikin wayar akace
"Allah ya taimaka babu hotel da club d'in da babu bincika ba a garinnan baya nan, amma mun dad'a fad'ad'a bincike dan mu gano ko ya sallaka ne yafita a garinnan ko wajen kasar nan, a bamu daga nan zuwa fad'uwar rana zamu gano inda yake."
Daddy ya jinjina kai yana kashe wayar.
Hajiya data zuba masa ido tana son taji shin an ga Zaraddin d'in ne ta ce
"An gano in da yaje?."
Daddy ya ce
"Aa ana dai kan bincike."
Hajiya ta ce
"Yanzu shi wannan yaro Zaraddin ya kyauta wa kansa ke nan, yatafi mil ya b'ata shiru babu waiwayan gida, ba gara shima ayi masa auren ba kawai a huta, amma ace yatafi kwana da kwanaki, baka tunanin ma kana da iyaye wani hali zasu shiga idan suka nemeka suka rasa, yaran yanzu da rashin tausayin iyaye yayi musu katutu, 'ya'yan da dako layi aka zana aka ce kada ka ketare baka isa ka ketare ba,
Shamsuddin ya gaya min wai har giya ya fara sha,
a cikin gidan nan ace wai an sami mashayin giya,
wani irin musifa ce wannan iye, duk ya gama karad'e gari da shaye-shaye da biye-biyen matan banza, ana samo shi ku had'ashi aure da Saddiqa, itama ranar Bilkisu take fad'a min wani yana zuwa d'aukar ta, to kafin su cigaba da shafa wa gidan nan bakin fenti gara a had'a su aure kawai a huta."

Dad ya ce "Wlh Hajiya narasa yadda zanyi da yaron nan, duk abun da zan fad'a masa bashi zai sa yaji ba, so yake mu yafe shi mu kore shi cikin 'ya'yan mu."
da sauri Daddy ya ce
"Korin shi a jikin mu bashi ne samun maslaha ba, tamkar mun bashi tiket na dad'a gurb'acewa ne, mu jashi a ajiki mu nuna masa abinda yake yi ba dai-dai bane, Allah zai taimake mu ya shirya mana su,
abun da Hajiya ta ce shine kawai za'ayi, idan ya dawo za'a d'aura musu aure da Saddiqa insha'allah hakan zai zamo silar shiryuwan su duka."
Abbieh ya jinjina kai ya ce
"Haka ne dama duk musulmi mai imani, Allah sai ya jarafcesa, ta hanyar dukiya ko 'ya'ya ko mata ko lafiyar sa,
wannan jarabawar mu ce Allah ya bamu ikon cin jarabawa, ya shiryar mana zuri'a baki d'aya."
duk suka amsa da amin amin.
taro ya watse Dad ya nufi gefen sa, yana sakar zuci, ga dukkan alamu dai zuciyarsa abu biyu take karonto masa yarda da had'a auren, dakuma son bijirewa yana tunanin kada had'in ya ruguje masa shirinsa.
Chapter 23 · 0% Book details