Sashe 19
Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yarasa sallah dole a gida ya yi sallah.
yana idarwa ya haye gado wani bacci mai dad'i ya d'auke sa.
karfe 7 dai-dai ya farka kamar an tashe sa.
yafita ya nufi gefenta.
in da yabarta nan ya taddata.
ya karaso bakin gadon da sauri, yana mamakin har lokacin bata farka ba, bayan allurar da ya mata wanda zai taimaka ne wajen dawo da ita hayyacin ta.
jijjigata ya shiga yi amma har yanzu shiru.
ya fita bai jima ba yado da sauri da wani allurar yayi mata.
ya tsaya na mintoti biyar idanunsa a kanta.
nan ma bata mo matsa ba, yad'an girgizata a lokacin har yafara tuninin karfa mutuwa tayi.
da sauri yaruko hannunta agogon hannunta yana bugawa.
da sauri ya sunkuya kanta ya d'aura bakinsa kan nata yashiga hura mata iskar bakinsa cikin nata yana yi yana danna kirjin ta.
numfashi taja da karfi ya cire bakinsa kan nata,
kara ta sake mai karfi tana fad'in
"Wayyo Ammie na, kizo Ammie zan mutuuu."
idanunta yakuma yin sama numfashin ya d'auke.
da sauri yakuma maida bakin sa yana kuma hura mata iskar.
yunkuri tayi kamar zatayi numfashi sai kuma ta koma kamar d'azu.
tayi haka yakai sau uku.
ya zaro bakin sa ya d'ago yana kallonta.
still har yanzu dai bata farka ba.
kugu ya rike yana furzar da huci, yarasa ma me zaiyi gaba d'aya kwakwalwarsa ta tsaya, kamar ba shine Dr AA FIYA d'in nan ba,
likitan da turawa da kansu suka bashi lambar yabo.
A parlour kuwa Baba Rabi ta shigo da breakfast d'in da Aunty tayiwa Feeryal alkawarin ita zata yi mata har da abincin dare.
kamar jiya yauma ihun Feeryal a kunnen ta.
yau kam lamarin tabata tsoro ko dai ba abun da tayi zatonsa jiya bane ke faruwa da ita.
idan kuma shine wani irin rashin imani yake aikata mata haka tun jiya har yau.
ta yi sauri kwab'ar kanta tana kallon kofar bedroom d'in ta, anya ba wani abu ke faruwa da yarinyar ba.
a matsayin ta na 'yar'aiki bata da damar shiga in da ba'a umurceta ba.
ta juya da sauri ta fita da gudu-gudu dan taje ta sanarwa Aunty abun da ke faruwa, ko dai wata matsalar ce tazo ta gani..
Tafito da sauri sosai tana alla-alla ta isa ta shaidawa uwargijiyar ta abun da ke faruwa.
Umma Karima da Siyama dasuka fito zasuyi sammakon tafiya gurin bokanta, ta hango Baba Rabi tafito daga side d'in Abdulrahim,
ganin saurin da take tana waige ta fahimci da wata a kasa.
Umma Karima ta tsaya har sai da ta kusa da get d'in Aunty sannan ta kirata tazo inda take.
Umma Karima ta hura hanci tana yamutsa fuska ta dube ta ce
"Ke Rabi wai saurin me kike ina kika fito?."
gaba d'aya Baba Rabi ta mance wace ce Umma Karima, sabar damuwa da fargaban abunda ke faruwa da Feeryal,
data barwa ranta aljanun ta ne suka tashi suke wahalar da ita.
ta ce "Wlh Hajiya Feeryal ce ina ga bata da lafiya ne tun daren jiya har yau nake jiyo kokan ta a d'aki."
Umma Karima ta kwalalo ido
"Kuka kuma tun jiya da daddare har yau, to ina Abdulrahim d'in ko shine a d'aki?."
Baba Rabi ta ce
"Wlh kuwa Hajiya tun jiya ban dai san ina yake ba."
ta juya da sauri ta nufi sashin Aunty.
Siyama ta d'aga murya ta ce
"Baki duba kinga mene ne ba."
"Ke dalla kyale idan kuwa yaje mata ne lallai akwai babbar matsala."
Umma Karima data daskare dan mamaki zuwa can kuma ta mulmulo wani uban ashar tana fad'in
"Tabd'i jam! duk san da nayi kokarin tufka sai ta warwane."
ta juya da sauri ta nufi sashin Mommy, Siyama tabi bayan ta.
ko da suka shiga Mommy bata nan tana sashin Daddy, Umma Karima ta nimi guri ta zauna bayan ta tura a je a kirata.
Baba Rabi tashiga ta sanarwa Aunty abun da ke faruwa,
hankali Aunty yatashi.
ta d'aga waya tayi ta kiranta yana shiga ba'a d'agawa.
ta tuna da daren jiya ta kirata an d'aga amma bataji maganar ta ba, daga baya kuma aka kashe wayar.
A b'angare Abdulrahim rasa me ma zaiyi sai kawai ya fita ya tafi sashin Hajiya.
a can ya tadda Ajmaal suna hira da Hajiya.
dan ba'in sashin ta duka suka tafi jiya, Goggo Bishira ce kad'ai ta rage tana d'akin ta dake sashin Hajiya tana bacci.
yana zama Ajmaal yashiga gaishe shi, ya amsa, kana ya gaida Hajiya a takaice.
Hajiya ta bishi da ido tana fad'in
"Abokin turawa an shigo, ya fuskarka tayi fayau tayi haske kamar wanda yayi zazzab'in dare."
beyi magana ba sai wayarsa daya zaro ya soma latsawa.
Ajmaal ya ce
"Kwana biyu ana sanyi da yawa fa."
shi dai baiyi magana ba sai wayarsa daya cigaba da latsawa.
Ajmaal da Hajiya suka cigaba da hirar su.
yana zaune tamkar baya gun.
zuwa can ya d'an gyara zaman sa tare da furta.
"Hajiya Beauty ba lafiya."
da sauri ta ce
"Wata biti kuma?."
Hajiya ta gwalalo ido tana dafe hannu a kirji.
bai kuma magana ba bai ku ma d'ago ba idanunsa na kan waya.
Ajeemal yad'an dubi shi, yasan sarai yaji tambayar da Hajiya tayi masa, amsar ne dai bazata samu ba.
"Kai ina tambayar ka kayi burus, wani shed'anin ne ya ce ka gaya min wani ba lafiya da kasan bazaka fad'i ko wane ne ba, salon ka data min hankali, wace ce bitin."
kai Ajmaal ya girgiza ganin ko a jikin sa baisa ya fad'i ko wace ce d'in ba,
lasa wayar sa kad'ai ya ke.
Ajmaal ya ce
"Hajiya Beauty a kace ba biti ba,
Beauty me kyau ake nufi kyakkyawa ba, matarsa ce FEERYAL ke nan ba lafiyar."
"Yo dan sabar iyashege da tsiyar hali ina tambaya ya yi banza da ni,
an fad'a maka kyan nata dama na lafiya ne, ai wannan kyan nata mu sifa ce ta had'a jini da aljanu ne,
to ni me zan mata, kake fad'a min bata da lafiya kana likita, sai kaje kayi ta fama da jinyarta, tun da haka uban ka ya zab'a ma, ya jonaka da damuwa, sai kaje kayi ta mata allurai."
Mikewa ya yi yana wani ciccin magani ya had'e gira, sai da ya taka yakai tsakiyar parlour'n batare da ya juyo ba ya ce
"Ina ganin wannan ciwon bana allura bane."
yana kaiwa nan ya nufi kofar fita.
Hajiya ta d'aga murya tana fad'in
"Ai dama bazai ji allura ko magani ba sai hayaki, yarinya mai gagga-gaggan aljanu a kai,
ai da gani uwarta mutum ce ubanta aljani, ta had'a jini da su,
sai kaje ka fad'awa uwar da tayi gayyar ta taje ta tarota tun kafin ta b'alle, taje ta kirawo masu gadi su taimaka mata dan babu wan da zai iya da fadan aljanu,
kai ma da kake iya tinkarar su har ka iya rike su, akwai ayar tambaya a kanka dan wannan halin miskilancin banzan naka da alama akwai bahagon aljani a kanka."
waje yayi yabar Hajiya tana ta surutu.
Ajmaal ya ce
"Hajiya ki bar maganar haka mana tun da ya tafi,
kije ki duba ta tun da kikaga ya fad'a to ciwon babba ne."
Hajiya ta waro ido
"Waa ni ina ni ina taron aljanu, ai shi daya fara sai ya karasa, yaje ya fad'a wa Fatiman datayi laman ta,
ko uban naku da yaji yagani sai da ya had'a ta da shi."
Ajmaal ya ce
"Haba Hajiya amma kinsan dai bazai ji dad'i ba tun da yatako yazo ya fad'a miki, yakamata kije, kinsan idan yayi fushi fa bazai sake zuwa fad'a miki komai ba."
Hajiya ta mike tana fad'in
"Gayyar tsiya ina ga irin ta tun ba'aje ko ina ba, anfara kalen fitinan jinya."
tayi ta bambami harta fita...
Umma Karima na zaune Mommy dawo daga sashin Daddy da Umma Karima ta tura a kirata.
tun kan Mommy ta zauna Umma Karima tashiga fad'in
"Hajiya Halima kin fa tafka babban kuskure a rayuwar ki,
tun wuri kafin lokaci ya kure miki yakamata ki d'au mataki,
kika tsaya sanya har sai da sukayi nasara asirinsu yaciwu,
to gashi can tun daren jiya ake jiyo kukanta har yau, ta makalkale shi a d'aki sai tagama tsotse masa ruwan jiki tas,
kinyi sake Hajiya Halima."
Mommy ta mike zumbur tana fad'in
"Me kike fad'a ne wai Hajiya Karima."
Umma Karima ta ce
"Rahoto dai yazo ga dukkan alamu Abdulrahim yaje wa yarinyar nan, dama taya za'ayi ace yana kallon yarinya kamar wannan ya kyale ta, ai dole sai yaje mata,
bare ma ba sai yaje mata ba su da suke son ganin komai ya dawo karkashin su,
ai sai ta san yanda tayi ta jawo shi yazo,
tuntuni kid'auki mataki kin saya sanya."
Mommy ta ce
"Hajiya Karima karki gamin wannan zance ni Abdulrahim zai wasawa kasa a ido, bari naje na ganewa idona, idan kuwa ya tabbata sai naci mutuncin sa."
"Gara dai kam ina shi ina tarayya da aljana."
Umma Karima tayi ta ingiza Mommy suka d'unguma sukayi side d'in Abdulrahim.
A b'angaren Aunty kasa nutsuwa tayi mata miss call yafi 20 bata d'agawa.
hankalin ta bai kwanta ba sam kira d'aya take yiwa Feeryal ta d'aga.
da sauri ta lalub'o lambar Ammah ringing d'aya ana biyu ta d'aga.
bayan sun gaisa Aunty ta ce
"Ammah'n Miemie, fito dan Allah ki rakani side d'in Feeryal inaga ba lafiya ba, nayi ta kiranta bata d'aga wayar."
Ammah tayi salati ta ce
"To gani zuwa."
Aunty tad'au mayafi tayi waje da sauri.........!