← Book details Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 61

Sashe 36

Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mommy tafito daga ciki motar da sauri rike da yaran a hannunta.
da sauri ta nufi bakin gab'ar ruwan tana fad'in
"Zo ku koma in da kuka fito, bazaku zauna cikin jinsin mutane kuna aljanu ba, ku ko ma can in da kuka fito."
da sauri direban ta ya fito ganin abun da take shirin aikatawa ya biyo ta yana cewa
"Hajiya dan Allah kiyi hakuri kar ki aiwatar da abun da kike shirin aikatawa."
tsawa ta buga masa ta ce
"Ka tsaya a matsayin ka na direba, kada ka sake ka shiga lamarin cikin gida."
ai ko ya ja ya tsaya ya nad'e hannu jiki na rawa cike da d'inbin fargabar abun da take shirin aikatawa.
ta dad'a matsowa bakin gab'ar.
ta d'aga d'aya ta na kokarin wurgashi a ruwan, dai-dai san da motar Abdulrahim ya sharo kwana in da suke iya hango tekun.
wani irin wawan burki ya taka dai-dai sanda ta jefa d'aya yaron cikin kogin.
direbanta ya d'aura hannu a kai yana salati.
da karfi ya b'alle murfin motar ya duro kasa batare da ya kashe motar ba.
a hargitse Ajmaal ya zare sit belt d'in jikinsa ya yi azaman ruko sitiyarin ganin motar tana kokarin gangarawa cikin ruwan.
yayi kwana da ita ya kashe motar.
wani irin gudu Abdulrahim yake cike da zafin nama yake taka kasa, cikin wani irin murya mai nuni da tsantsar tafasar zuciya gami da amon sauti, mai fita da karaji,
ya ke fad'in
"No! Mommy kada kiyi haka!."
yana daf da isowa inda take tayi saurin dad'a masowa bakin ruwan, ta d'aga zata kuma jefa d'ayan.
ya mika hannu yana fad'in
"Aa Mommy a'aaaaaa!."
bai rufa baki ba kaji bundun, ta jefa shi yaron ya calla kara.
yana wutsil-wutsil kamar yadda d'anuwan sa yayi kafin ya nitse a daina ganin sa.
da gudu ya wuce ta zai yi tsalle ya dira cikin ruwan.
Ajmaal da direban ta sukayi hanzarin ruko shi ta baya.
Ajmaal da tuni hawaye yashiga wanke fuskarsa ya ce fad'in
"Aa Ya Abdulrahim kada ka shi ga."
"Yellab'oi ruwannan da zurfi sosai tanan gefen kada ka shiga."
da jarfi ya fizge yakuma yunkurin shiga suka juyo muryar Daddy a bayan su
"Ka dakata Abdulrahim!."
Daddy ya yi maganar cikin d'aga murya.
wani irin durkushewa yayi da gwuiwowin sa a bakin gab'ar tare da cusa hannanyen sa cikin gashin kansa da karfi ya yi wani irin ihu mai kara gami da karajin gaske,
yana yamutsa gashin yana wani irin huci tamkar namijin zakin daya kwana baiciba.
Daddy ya nufo su da sauri mai kama da gudu, in da direban sa shima ya rufa masa baya.
Ajmaal ya juyo yana hawaye murya na rawa yake fad'in
"Daddy Mommy ta kashe su ta jefa su a ruwa, ta kashe su Daddy!."
ya fashe da kuka kamar karamin yaro.
Daddy ya karaso ya dafa kafad'ar Abdulrahim dake durkushe yana bubbugawa, yayin da idanunsa ke kan ruwan da babu alamun yaran a ciki.
idanun Daddy suka kawo kwalla sai ga Daddy na hawaye da idanunsa.
kan kace me aka nimi Mommy a gurin aka rasa, ta zame ta shiga mota tasa direba ya juya da ita gida.
tana ji a ranta ta raba su da fitinar aljanu.

Nan da nan Daddy yasa aka kirawo masana ruwa, aka shiga jirgi akayi ta yawo cikin ruwan ana nima,
amma ko gawarsu ba'a samu ba, daga karshe aka samo abun d'aukar d'aya jaririn.
ma'aikatan suka bawa Daddy tabbacin gawarsu baya kusa, ruwa ya tafi da su amma zasu tura sanarwa a tare su acan rariya idan suka isa can za'a neme su.

Jiki ba kwari Daddy ya juya gurun Abdulrahim, ya ruko hannun sa da tun d'azu ya masa ya zauna gefe kan wani dutse ya sunkuyar da kai kasa.
Ajmaal da tun d'azu ya kasa tsayuwa guri guda ya zo gon d'an'uwan nasa ya koma bakin ruwan yana lekawa ko za'a ciro yaran.
ya taho da sauri sanda Daddy yake mikar da shi tsaye.
tausayin d'anu'wan nasa ya kuma baibaye shi.
idanunsa sunyi jajir jijiyoyin jikinsa sun mike rad'a-rad'a,
zufa yana gangarowa daga cikin sumar kansa zuwa fuskarsa.
Daddy ya dubi d'an nasa da d'inbin tausayawa dan yasan yakai makura a b'acin rai ko bai furta ba, basai ya furta ba yasan wannan halin nasa tun yana d'an karami,
idan yana cikin b'acin rai haka zufa zatayi ta karyo masa daga cikin sumar kansa yana gangara fuskarsa, jijiyoyin jikinsa zasu mike rad'a-rad'a.
sai dai na yau yafi na duk sauran lokutan dan kuwa yau karkashin jajayen idanunsa sai da sukayi damshi alamun ruwa nason fita daga cikin su.

Daddy ya damke hannunsa da kyau ya dube shi yana fad'in
"Ka yarda da Allah kayi imani da kaddara mai kyau ko mara kyau, muje gida Abdulrahim."
ya janyo hannunsa motar Daddy suka shiga shi da Daddy gidan baya,
direba ya ja su.
Ajmaal ya shiga motarsa da suka zo da shi yabi bayan su suka nufo gida.

Su Shamsuddin da Faisal da suka d'auko hanyar zuwa, bayan sunyi waya da Ajmaal ya sanar musu abun da ke faruwa, kafin su fito suka sanar a gidan, tuni gidan ya d'auki labarin.
suna hanya suka kuma kiransa ya yi musu kwatance, ya ce su juya gida gasunan suma dawowa.

Wani irin gud'a Umma Karima ta rangad'aga, tayi tsalle ta tafa hannaye, tamkar anyi mata albishir da aljanna.
"Hajiya Halima kinyi abun da ya dace, da baki farka ba da ni zan mike dan ni bana bacci."
Bilkisu data kawo mata labarin ta ce
"Umma wai murna kike wlh ni jikina yayi sanyi, ko da bani son Feeryal amma 'ya'yan nan na Ya Abdulrahim ne shi kuma yayan mu ne,
ai bazai so ace yau ayi masa haihuwa a yau d'in kuma yana ji yana gani akashe masa yara ba,
gaskiya Mommy bata kyauta ba, kashe rai ai musifa ce, ranma na jarirai wanda yau aka haifesu basu d'auki hakkin kowa ba haba dan Allah."
Bilkisu tayi waje tana Kuma fad'in rashin kyautawar Mommy.

Tun da suka hau hanya Daddy ke bubbuga bayan hannunsa da hannun nasa ke rike a hannun Daddy alamun rarrashi, duk da shima yana jin kuna da b'acin ran a tare da shi.
har suka karaso gida.
suka sauko a motar ya zame jiki ya wuce side d'in sa.
Daddy ya nufi sashin Mommy rai b'ace, a tsaye ya tadda ita a parlour Mommy tana ganin sa ta b'ata rai.
tana fad'in
"Haka kawai a dukeka a hanaka kuka, a wani dalili aljanu suje can su karata."
bata yi aune ba yana karasowa ya wanke mata mari cikin kakkausar murya ya ce
"Allah wadai da hali irin naki Halima wlh nayi nadamar kasancewar ki a matsayin uwar 'ya'yana,
kije na sake ki, kuma bazan kyale ki ba sai nayi shari'a da ke akan jikoki na da kika kashe!."
muryar Hajiya suka jiyo a bayan su tana fad'in
"Mai da ita yanzu nan maza ka mai da ita, in dai ina numfashi baka isa ka saki Halima ba, 'yar uwar taka ko me tayi maka banyar da ka sake ta ba,
yara kuma sunzo kan lokaci ne dama ba masu rayuwa bane su, ka mai da ita na ce ko ka biyani nono na!."
Hajiya ta karaso tana kuma fad'in
"Ka mai da ita nace."
Daddy ya ce "Amma Hajiya."
da sauri Hajiya ta tari numfashin sa
"Ka mai da ita na ce, duk shari'ar da zakayi da ita kuyi tana d'akin ta."
Daddy ya ciza yatsa tare da fad'in
"Na mai da ke amma kar ki sake kizo in da nake."
ya juya yafita cikin matukar b'acin rai.
Mommy dake dafe da kuncinta da alamun jikinta ya yi sanyi.
Hajiya ta dube ta ta ce
"Yanzu ke Halima bakiji ko d'ar ba, da har zaki iya kashe kikokinki da hannunki?
yau ko bare ai bazata aikata hakan ba,
bare ke da kike jinin Abubakar,
ai 'yar nunel ta nuna basai an fad'a ba, da ka kalli yarannan kallo d'aya kaga Abokin turawa,
ko makaho ya shafa yasan 'ya'yan nan na abokin turawa ne,
yo zance ya kare tun da har yabi dare yaje ya had'a shinfid'a da ita,
ai dole mu karb'i 'ya'yan nan, bare ga babban shaida da sukayi kama da uban su,
wannan ai niman jawa mutane magana ne."
Hajiya tayi waje tana bombomi.
Mommy ta zauna kan kujera jiki a sanyaye.
Chapter 36 · 0% Book details