Sashe 10
Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Sati guda Aunty ta d'auka tana aiko musu da abinci.
safe da rana da yamma,
kullum kuwa zai shigo da kansa ya d'ibi abin da yake bukata.
abin da ta lura yana matukar son Sudan tea dan flask d'in gaba d'aya yake d'auka.
sai dare ya dawo da shi yakuma d'aukar wani da Aunty ta sa a kawo.
wani lokacin har ya fita tana jin motsin sa bazata fitoba,
har sai ya gama ya fita.
wani lokacin kuma suyi kicib'us a parlour zata tsaya sai ya d'au abin da zai d'auka yafita kafin ta wuce tayi abinda zatayi itama.
ranar da ta cika satin kuwa Aunty ta kira Feeryal a waya ta video call, ta d'aga cikin yanayin ta mai sanyi da muryarta mai fita da yanayin shagwab'a, ta soma gaida Ammie'n tana,
yayin da ta sako shagwab'ar a zahiri irin yadda d'a yake idan yaga uwansa.
daga cikin wayar Aunty ta ce
"Feeryal kuna lafiya dai ko?."
fuska ta marairai ce cikin yanayin ta mai sanyi ta ce
"Ammie ba kin ce kar nazo ba, kuma ni ina so na ganki."
murmushi Aunty tayi ta ce
"To Feeryal ba gani muna ganin juna ba, karki fito batare da izinin mijin ki ba kinji."
rau-rau tayi da ido.
Aunty ta kuma murmushi mai sauti ta ce
"Kina jina ko Feeryal?."
baki ta turo tare da gyad'a kai.
Aunty ta ce
"Amsa mana d'iyar kirki."
ta ce
"Ina ji Ammie."
"Yauwa bacci mai tsawo ya kare daga kan yau, dan daga yau na sake miki ladarki, ke zaki cigaba da hidima da gidan ki, idan gari ya waye banda nisan bacci Feeryal ki tabbatar da kin tashi kinyi breakfast kin aje a kan dinning, abincin dare da rana kar ki bari ko d'aya ya wuce ki, ba kinga yadda nake yi ba ko Daddy baya nan side d'ina bana tab'a yanke yin girki, to kar ki sake kiyi wasa da samin wannan ladar ko da wani bai ciba, ke kika ci zaki sami lada,
karkiyi wasa da gyaran sashin ki, nasan duk abin da na fad'a miki kin iya dan duk na koyar da ke su,
yanzu ne zaki bud'e iyawar taki kiyi amfani da shi a gidan ki, kada kiyi wasa Feeryal ladabi da biyayya girki gami da tsafta shine mace, dan haka ki kula,
a kwai komai na amfanin girki a kitchen da store d'in ki,
ki d'aura aniyar farawa da bakisan ranar dainawa ba."
kai ta jinjina.
Aunty tayi murmurshi ta ce
"Ko so kike naci gaba da kwasar ladan duka?."
kai ta girgiza ita ma tana maida mata murmushin.
"To ayi rige-rigen tara lada aga wa zai riga tarawa da yawa."
Aunty tayi ta mata nasiha da jan hankali cikin dabara ta yadda zaifi yin tasiri a gareta a 'yan shekarun ta, daga bisani sukayi sallama......!
"Babu editing ban sami damar yi ba zaku had'u da kura-kurai da yawa*
Washegari karfe 10 na safe kiran Aunty yashigo wayan Feeryal
da ke bacci. sai da tayi mata miss call 5 kafin ta farka.
Aunty tana jin muryarta cike da bacci ta ce
"Feeryal bacci kike kar dai a ce baki tashi ba?."
hannu takai ta mussuke idanunta cikin muryar bacci ta ce
"Um."
Aunty ta ce "Feeryal bacci har karfe 10, me kike samu cikin baccin da baki tashi kin girkawa mijinki abin kari ba?
kin sane da cewa baya cin duk wani abincin da zai fito daga hannun masu aiki, haka kikasa ya tafi gurin aiki batare da ya karya ko ya tafi da abin karin ya yi breakfast d'in a can ba?
wani dad'i zakiji mijinki ya fita tare da yunwa,
haka kikaga nake yi? ko sau d'aya ban tab'a hutu wajen yiwa Daddy girkiba, dan nasan babu in da zai je yaci sai a nan, Feeryal karki sake haka ina jiya mukayi maganar nan da ke, ki aje wannan cikin kwakwalwarki shine abu na farko kuma na gaba-gaba a cikin gidan ki da zaki fara d'aukarsa da muhimmanci,
kar ki sake yin sake wajen wasa da yin girki, kina jin abinda nake fad'a ko?."
kai ta gyad'a tare da cuno baki ta ce
"Eh."
Aunty ta ce "Maza tashi kije ki kula da gidan ki, kar ki sake bari hakan ta faru,
karki yi sake wajen shiga kitchen kar kice dan jiya kinyi yau kinyi gobe bazakiyi ba,
kiyi girki ko da wani bazai ci ba,
Feeryal Abdulrahim gadon Daddy yayi kamar yadda shima Daddy'n ya gado mahaifin sa,
basa cin abinci wata idan har sunan ta 'yar aiki ce,
da jajircewa wajen ganin Daddy bai wahala wajen samin abinda yake so daga abinci ba ake cewa na mallake sa, kar kiyi wasa ki kula sosai."
kai ta kuma gyad'awa kamar tana gaban ta kana ta mike sanda Aunty ta kashe wayar.
Kallon agogo tayi taga goma har ya gota, ta shiga bayi ta wanko bakinta ta fito ta nufi parlour da kayan baccin jikin ta.
tun da tazo bata tab'a shiga kitchen ba bata ma san ta ina kitchen d'ina yake ba, nan ta soma niman ta in da yake,
nan ta gano wasu bedroom na alfarma guda uku cikin parlour, wata kofar da ke kusa da dinning ta nufa ta bud'e nan taga ashe shine kitchen d'in.
kitchen mai girman gaske da ya tara kayan da duk ake bukata na amfani a kitchen, har da wanda ma bata san da su ba, sai da da yawa ko mai a rubuce yake.
daga cikin kitchen d'in taga wata kofa, nan ta bud'e taga makeken store ne, shake da kayan abinci kala-kala.
ta d'ibi duk abin da take bukata ta dawo kitchen.
ta bud'e freezer tad'au kaza guda d'aya da suke cike ciki a gyare duk sunyi kankara.
ta saka a roba ta zuba masa ruwan zafi da ta d'aura kan gas.
ta matso da fulawan da ta d'ibo ta soma sarrafashi cikin kankanin lokaci ta had'a cake d'in ta na musamman, ta saka shi a oven.
bayan kankaran jikin kazar nan ya narke ta yayayyanka ta wanke shi saf ta zuba a tukunya bayan ta d'aura a gas.
ta zuba mishi kayan kamshi da na d'and'ano gami da kayan yaji d'an dai-dai ta sulala mai dai-dai kima, ta rufe ta rage wuta.
ta fere dankali ta zuba mai a wuta tasoma suya.
tana gamawa ta fasa kwai da kayan Spices da sokar kifi,ta soya.
a gefe guda kuwa ta wanke hanta ta zuba a tukunya ta d'aura a wuta, batare da ta tafasa shi ba,
ta sulala masa mai ta zuba masa kayan kamshi da nikakken kayan miya, gami da kayan d'and'ano.
tarika d'an jujjuyashi har sai da ya soyu shi da kayan miyar, suya mai kyau kana tad'an zuba masa ruwan zafi yasake jikin sa, ta barshi ya turara kad'an sannan ta sauke.
nan da nan sashin nata ya kaure da dadad'an kamshin girkin.
a gefe guda kuwa ta d'aura Sudan tea a wuta.
karfe 11 da rabi ta kammala komai ta kwasa ta shirya su a kan dinning.
kana ta dawo ta tsaftace kitchen d'in.
ta kunna masa turare sannan ta koma d'aki.
tayi wanka ta shirya cikin riga da wando Arabian dress rigar mai fad'i tsawon sa ya wuce guiwarta, wandon ma daga kasa tana da fad'i.
tayi rolling na gyalen kayan tafito tamkar balarabiyar asali.
wani irin dad'i kuma sassanyar kamshi ne ke tashi a jikin ta.