← Book details Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 61

Sashe 12

Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

"Deen kabar kanka ya huta mana, 8 days kana narkawa kanka kwayoyi da barasa,
tun da anfi karfinka bakasamu lu'ulu'un nan ba, ka hakura mana, ka fantama cikin gari da wajen kasarnan zaka sami kamar ta ko wacce ta fita ma,
mttss naso ace kai ka auri yarinyar nan ka bani aron ta na more kayan alatu,
amma brother naku ya yi tsawon kafa ya yi gola ya tsare,
wannan ba karamin kaya yake d'iba ba."
Zaraddin ya janyo kwalbar giya, ya kafa a bakin sa sai da ya sha rabi kafin ya d'aga kwalbar ya yi wurgi da shi sakiyar parlour'n Ziyad kwalbar ta tarwatse.
ya shiga dukan table d'in gabansu yana fad'in
"Bazan bar masa ita ba! dole ya sake ta na aure ta!."
ya mike zumbur yana cigaba da fad'in
"Abdulrahim dole naji abin da kake ji a jikinta, yazama dole kuma kasake ta na aure ta."
ya d'aga kafa yana kokarin fita Ziyad ya taro sa yana cewa
"Deen me zakayi kabi ko mai a hankali fa, dan wannan Dr d'an zafin kai ne kar aje a sami matsala."
cikin hargagi da ihu ya ce
"Yau nine zan kwana da ita ba shi ba, daga nan zuwa gobe kuma idan bai saketa ba, sai na kashe shi na aure ta."
da sauri Ziyad ya rike hannunsa ya ce
"Deen ka dakata, kajira ka sauka a network kayi tunanin hanyar da zakabi wajen d'aukar wannan mataki, kaga yanzu a shaye kake, wannan lamari ba irin sauran da muka saba tinkara bane, katsaya kwakwalwar ka tagama caji, nima ina goyon bayan yasaketa mu samu, idan kuma ba haka ba mu sace ta."
hannunsa ya fizge yajuya da karfi yayi waje yana fad'in,
"Bazan bari sai gobe ba yau zan aiwatar da komai." yashiga motarsa da gudu yabar gidan, ya nufi AA FIYA STREET.

Ana idar da sallar isha yana isowa gidan a babban parking lot yayi parking.
ya zauna cikin motar bai fito ba, idanunsa a hanyanyar wucewa yana kallon matasan gidan da suka fito daga masallaci suka wuce side d'in su.
yakai minti 10 a zaune kafin yaga shigowar Abdulrahim.
sai da yakusa da side d'in sa kafin yafito a motar
a hankali yake tafiya yana d'an waige-waige, yana ganin shigewar sa dide d'in ya d'aga kafa da sauri.
yana isa bakin get d'in side d'in.
yatura karamar kofa,
mai gadi nazaune ya yi saurin mikewa, ganin d'an gida ne sai ya koma ya zauna, dan zaton shi tare suke da Abdulrahim d'in ganin yanzu shigowarsa.
ya ce
"Yallab'oi ya wuce gefen sa."
kai Zaraddin ya jinjina kana
yasa kai yanufi gefen Feeryal yana d'an waige-waige.
sai da ya iso bakin kofar gefen nata yaja ya tsaya.
yakuma waigawa, yaga mai gadi ma sha'anin sa yake, hankalin sa nata wani gurin.
ya kai hannu kan handle duk da bai sammace kofar a bud'e take ba, sai ko yajita a bud'e.
ai ko da sauri ya murd'a handle d'in yasa kai cikin hanzari ya shige.
yana shiga ya maida kofar ya rufe tare da murza key.
tsayuwa ya yi yana kalle-kalle, sai kuma da dauri ya nufi cikin parlour'n, yabud'e kofofin bedroom's guda biyu bai ganta ciki ba, ya juya da sauri ya nufi kofar da take ciki.

Tana tsaye gaban wardrobe fitowarta daga wanka ke nan.
towel ne kad'ai d'aure a kirjin ta, babu ko d'ankwali a kanta.
da sauri ta waiga a kuma razane jin an bud'o kofar da karfi.
ganin wanda ya shigo d'akin da yanayin yadda ya fad'o d'akin nata, tashiga mamaki kwarai da gaske.
murmushin karfin hali ta sake,
da sauri ta mika hannu tana kokarin janyo hijabi, tare da fad'in
"Ya Zaraddin kai ne inayini."
wani irin mayataccen kallo yake binta da shi yasoma takowa yana fad'in
"No no no! basai kinyi wahalar rufa wannan kyakkyawar jikin ba, yau kwana zanyi ina kallon sa."
a razane ta dube shi, ganin yana dumfarota gadan-gadan, tashiga ja da baya tana cewa
"Me kake fad'a ne Ya Zaraddin?."
bata kai ga rufa baki ba taji ya damko hannunta, wani irin sauti yaja
"Ahhh hannu kawai da irin wannan laushin, ina kuma dana lume cikin wannan kyakkyawa had'add'en jikin, baki gane yaren ba ne, shi wancan da kike kwana da shi bafa wani abu yafini ba,
yau zaki gane ni jarumi ne sai kin raina jarumtar sa."
wani irin bala'in tsoro ne ya kamata, da iya karfinta tayi kokarin kwatar hannunta.
sai ji tayi ya rungumo ta.
kara mai karfi ta sake
a take wutan side d'in ya d'auke gaba d'aya.
tsaoro mai tsananin ya kuma lullub'e ta, tashiga ihu da musu-musun kwatar kanta.

Da karfi aka banko kofar ji kake kyass! karan yanka wani irin gigitaccen kara Zaraddin ya sake ba shiri ya sake ta.
tayi baya a tsorace, duk da bata ganin abun da yake faruwa d'akin duhu sai hasken screen d'in waya da mai ita ya shigo, wanda bazata ce ko waye ba, tsoron da ya shige ta yanzu ya girmi na farko.
jin ta shige lungun wardrobe tadad'a makalewa tana b'ari.

Wani irin duka yashiga yiwa Zaraddin kamar zai rabashi da ransa.
tun yana ihu har ya dawo yin wani irin gurnani.
Feeryal ta kankame idanunta gam-gam a cikin duhu jikinta na kakkarwa, tana kuka da kiran sunan Ammie'n ta.

Janyo sa ya yi yafita da shi a d'akin, bai fasa bugun sa ba har ya fita da shi, daga gefen nata gaba d'aya.
ya yi parking lot da shi ya bud'e bot ya turashi ciki sannan ya rufe.
yajuyo yana huci, mai gadi ya karaso gurin da 'yar tocilan sa da sauri yana fad'in
"Yallab'oi haka kawai wutan ta d'auke, nayi iya kokarin gyarawa yaki."
baiyi magana ba ya soma tafiya, ya shige gefen sa yana shiga wutar ta kawo.

Wuta na kawo wa Feeryal ta kuma wani irin zamura ta mike, jiki na rawa.
a matukar razane takuma yin baya ta garu da jikin garu, jiki na kyarma.
ganin jini malale a kasan d'akin, ga kuma wuka a gefe.
takai hannu da karfi ta toshe bakin ta, nan da nan taji kanta na juya mata, a hankali ta sulale kasa, bata kuma sanin abunda yake faruwa ba...

Da sauri ya fito ga yadda yake taka kasa zaka fahimci tsagwaran b'acin rai tare da shi.
ya isa parking lot ya yi wa motar key, da sauri mai gadi ya bud'e masa get yafita.
tun kafin ya kara babban get yake hon,
a guje security suka wangale masa get, ya fice da mugun gudu.

Can gidan gona ya nufa yana isa ya bud'e yafito, yazo ta bayan bot ya bud'e ya janyo shi ya fado kasa.
ihun wahala yayi can kasan wuya, ko kansa baya iya d'agawa, sai juya fuskarsa yake akasa.
su Jaq da Tag suka karaso da sauri suka ciccib'eshi suka shi ga da shi ciki.
suna shiga suka sake shi kasa.
Abdulrahim ya sunkuya a gabansa fuska a shinfid'e da tsagwaran b'acin rai.
hannu ya mika musu tare da fad'in
"Kawo kayan d'inki."
da sauri Jaq ya je ya had'o kayan aiki ya miko masa.
wasu lafiyayyun maruka biyu ya d'auke sa da shi,
cikin kakkausan murya mai nuni da zallan b'acin rai, ya ce
"Zan jinyataka kafin nayi maka hukunci dai-dai da laifin da ka aikata!
kar ka d'auki wannan a matsayin hukinci zanyi ma hukunci bayan ka warke."
ya mirgina sa ta baya yankan da ya yi masa a baya sai fidda jini yake, yankan ya shiga kuma ya yi girma.
yasa hannu yakara yaga rigarsa ya masa allurar tsaida jini, dan tun a gida jinin yake zuba har kuma yanzu.
nan ya soma kokarin dinke gurin daya yanka shi.
Zaraddin sai juya kai yake ba bakin magana.

Ya b'ata lokaci wajen yi masa d'inkin, kafin yagama.
yana gamawa yasa su d'aga shi su shiga dashi cikin wani d'aki mai duhu, bayan ya yi masa duk abin da yakamata.
kana ya fito yashiga motar sa ya juya gida......!

Koda ya isa gida gefen sa ya shige, yarage kayan jikin sa, yabar gajeren wando da singilet.
har yakai kofar bathroom sai kuma yaja ya tsaya, gajeren tsaki yaja kana ya juya yafita ya nufi gefen ta. yana shiga ya tsaya daga a bakin kofar bedroom d'in.
ganin in da d'akin yayi kaca-kaca da jini.
idanunsa ya sauka a kanta, tana kwance a kasa, kusan rabin jikin ta a bud'e yake dan towel d'in daga kasa ya bud'e amma ba duka ba, yanayin fad'uwar da tayi shi ya baiwa towel d'in damar bud'ewa ya zamo ta gefen cinyarta.
daga sama kuma ya kunce sai dai bai zame daga kirjin ta ba.
bata ko motsi da alama dai suma tayi.
gefe yabi yataka ya isa in da take.
ya sunkuya ya mika hannu ya ciccib'ota.
a hankali ya had'a ta da kirjinsa.
wani irin harbawa zuciyar sa tayi, ba shiri ya rumtse idanunsa da karfi, sai kuma a sannu ya bud'e su a kan fuskarta.
a hankali ya soma d'aga kafarsa idanunsa a kan fuskarta bai janye ba, har ya tako bakin gado.
ya sauke ta a hankali ya kawar da kansa gefe tare da mika hannu ya gyara towel d'in yadad'a rufe mata jikin ta.
ya share jinin ya goge gurin tass kamar komai bai faruba.
Chapter 12 · 0% Book details