Sashe 20
Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mommy da Umma Karima suna kokarin shiga bedroom d'in Feeryal. Aunty da Ammah suka shigo parlour'n.
ganin su yasa Aunty d'aga kafa da sauri suka bi yanasu.
ganin Feeryal kwance babu kaya a jikinta sai bargo dake rufe a jikinta daga cinyarta zuwa kirjinta, tana kwance da alamun bata motsi.
Aunty tayi saurin wucesu da sauri ta isa bakin gadon.
ta girgizata da karfi tana kiran sunan ta, tashin hankalin Aunty d'aya kada ace aljanu ne suka tashi a kanta.
ta d'agota da karfi ta rungume ta tana kiran sunan ta da karfi a cikin kunnenta.
Ammah ta karaso da sauri tana dafe kai idanunta akan gadon da yayi kaca- kaca da jini musamman in da take kwance.
Ammah tayi saurin janyo bargo ta gyara tarufe matajikinta, lura da babu kaya a jikinta.
Mommy ta tsaya a tsakirayar d'akin,Umma Karima ko sai da ta karo har bakin gadon, dan ta tabbatar da zargin da take.
Hajiya tun daga hanya take bombome har ta iso side d'in mai gadin get d'in ya bud'e mata bata fasa ihun masifa ba,
har ta shigo parlour'n Feeryal
ta nufi bedroom tana fad'in
"Ina abokin turawan yake, ai dama masifa aka had'a ka da shi, yanzu zanje nasami uban naka, shi da yaji ya gani sai yazo yatare ta tun kafin ta b'alle, kai da kake shan gaban aljanun ma yau baka iya ba sai uban wa zai iya, zancen banza kai wlh bazai yuwuba tun wuri ya sama ma lafiya ya rabaka da damuwa."
Hajiya ta shige d'akin ganin su Mommy ciki ta karaso tana fad'in
"Abun ya gawurta ke nan, to mu ina zamu iya muna mata, wanda maza masu gadi hukuma masu rike da bindiga da suke bakin get ma basu iya da ita ba,
ina yake shi iliya d'an mai karfin ba shi yake iyawa da ita ba, aje a had'a mutum da masifa, kai abokin turawa wazai iya maka da ita kai zakazo ka tare ta."
Hajiya ta karashe maganar tana waige-waige ko yana d'akin.
Kuraiba data shigo da sauri jin hayaniya yaki karewa, itama taja ta tsaya.
bata bukatar samun amsar meke faruwa dan tashin farko ta fahimci, abun da ke faruwa,
ranta ya jagule a yadda ta ganta tasan taji ta maza,
to yaushe ne Abdulrahim d'in yazamo haka ko jinya yake a b'oye yasa mi sauki,
bakinciki ya lullub'eta,
dama b'oye mata kansa yake,
ko kuma da gasken saukin ya samu.
taji wani kololon bakinciki ya kuma tokare mata zuciya.
da karfi Aunty takuma kiran sunan ta cikin tashin hankali.
"Feeryal! innalillahi wa innailaihirraji'un!."
takuma fad'i a cikin kunnenta.
fizgo numfashi tayi tare da kankame Aunty cikin muryar tsoro gami da galabaita ta ce
"Wayyo wayyooo Allah
Kayi hakuri Sahaaab zan mutu akwai zafi wayyoooo Ammie na."
jikinta yana kokarin kuma sakewa.
da sauri Ammah ta bud'e fridge ta d'au ruwa mai sanyi ta wasa mata a fuska.
Hajiya ta rike baki ta gwalalo ido.
"Yoo wannan yaro hauka yayi ne zaiyi irin wannan aikin, ke Safiyya juye ruwan a tsakiyar kanta, duka zata kuma komawa suman."
Ammah tayi saurin ta yuye ragowar a tsakiyar kanta.
wani nannauyan numfashi ta sauke tare da sakin kuka, ta kankame idanunta da karfi, tana dad'a rirrike Aunty,
cikin muryar kuka take fad'in
"Dan Allah kayi hakuri na tuba."
jikin Aunty yayi sanyi, murya a sanyaye ta ce.
"Feeryal bud'e idanunki."
da sauri ta ware idanunta jin muryar Ammie'n ta.
takuma sakin kuka ta rungume ta tana cewa
"Ammie ki tafi da ni."
da sauri Mommy ta juya zata fice a d'akin.
Ammah ta ce
"Allah sarki sannu 'yar halak yau kin goge wa kowa tantamar sa."
da sauri Mommy tayi waje Kuraiba da bakinciki ke kokarin hallaka zuciyarta ta bi bayanta.
Umma Karima ko kallon banza ta wurgawa Ammah sannan ta juya tayi waje, suna joyota tana fad'in
"Karyan banza duk wannan shiri ne."
Hajiya ta dubi Aunty tana fad'in
"To kin sata gaba tana kuka, tashi zakiyi kije ki kinyata ta, bari na aiko muku da gabaruwa da lalle da gishiri."
tayi waje tana cibaga da fad'in
"In banda jaraba irin na 'ya'yan yau, me zai kaika had'a shinfid'a da yarinyar da take aljana-aljana mutum-mutum."
Kuraiba na tsaye parlour'n tana ta cika tana batsewa, wani dogon tsaki taja ta ce
"Wani shegen rakin karya da son a sani, aikin banza kawai mutane sun taru kamar wani abu."
taja dogon tsaki.
Hajiya tabita da kallon shekeke ta ce
"Zancen banza kai ke meyasa baki tara mutanen ba lokacin naki, ko tarin ki bamuji ba, babu wanda ya shaida ranar farkon ki, ko banza ita yanzu taci tukuici."
Hajiya tayi gaba tana bombomi.
bakinciki ya dad'a turnike Kuraiba tabi bayan Hajiya da kallon banza tana fad'in
"Tsohuwar nan baki sanni nane."
ta koma gefen tanajin bakinciki na dad'a shigarta.
Siyama takasa zaune ta kasa tsaye, tana zaman jiran Umma Karima ta dawo taji me yake wakana.
tana ganin tanin yadda Umma Karima ta shigo a hargitse, ta tare ta tana fad'in.
"Aunty Karima lafiya? Allah yasa aljanun sun jata sun tafi da ita."
Umma Karima ta ce
"Ina an kuma samun gaggarumar matsala, Abdulrahim ya kusance ta, banci ta zama ba yanzu zanje na sanarwa boka, ya duba yaga me zai faru nan gaba, kar aiki ya kara wargaje wa,
na barta can tana ta narkewa sai kace a kanta aka fara kai budurci gidan miji."
Siyama ta dafe kirji
"Ya kusance ta!?."
fifita ta soma da hannunta jin wani zafi ya shige ta.
A can gefen Feeryal kuwa, tana rirtike da Aunty, taki sakin ta sai kuka take.
hankalin Aunty duk gaba d'aya ya tashi.
Feeryal sai fad'i take
"Ammie mu tafi Ammie kar ki barni."
sosai ta dage tana kukan da fad'in ita dai su tafi.
wayar Aunty ya yi kara ganin Daddy ke kiran nata tayi saurin d'agawa.
Daddy ya ce Fad'imatu ina kika shiga ne na shigo ban ganki ba?."
Aunty ta ce
"Daddy gani a side d'in Abdulrahim."
kafin ta rufa baki yajiyo kukan Feeryal da sauri ya ce
"Me yasami Feeryal d'in?."
Aunty tad'an yi jim.
Daddy yakuma fad'in
"Fad'imatu me ke damin ta?."
ta ce
"Am bata da lafiya ne kuma wai sai lallai mun taho da ita."
d'an shiru Daddy ya yi yana son nazartar shirun da Aunty tayi,
da sauri ya ce
"Ku taho da ita bari na kira Abdulrahim d'in."
Daddy na kashe wayar yakira sa.
baya gidan tun shigowar su Mommy ya fice a mota.
yana ganin kiran Daddy ya d'aga da sallama, Daddy amsa gaisuwar da yake masa sannan ya ce
"Nasa Aunty'n ku ta d'auko Feeryal ta maido ta side d'inta, idan ta sami sauki za'a mai da ita."
shiru ya yi baiyi magana ba, Daddy ya kashe wayar.
Aunty ta dubi Ammah dake kokarin shiga bayi ta had'a musu ruwan zafi, ta ce
"Ammah'n Miemie Daddy ya ce mu tafi da ita."
Ammah tace
"Yauwa hankalin ta zaifi kwanciya ma, bari a wanke bedsheet d'in."
Aunty tad'an d'agata aka zare zanin gadon Ammah ta shiga dashi bathroom ta wanke kana tayi amfani da Wishing machine wajen busar da shi.
a d'akin kuma Aunty ta d'auko mata doguwar riga tasaka mata, tana ta mata sannu da sanya mata albarka.
Feeryal ko kuka har yanzu yaki karewa sai masar kwalla take tana yayyarfe hannu.
Ammah ta fito da bedsheet d'in a goge kamar ba shi ba.
wajen tafiya Feeryal ta gagara, Aunty ta ruko hannunta ta tashi su tafi tana mikewa ta koma ta zauna da sauri, hawaye na zuba.
Ammah ta ce
"Ammie'n Feeryal kamar fa bazata iya tafiyar nan ba, a kira direba kawai yazo."
Aunty ta ce to, ta kira direban ta batare da b'ata lokaci ba ya iso.
suka tallafe ta da kyar ta iya takowa farfajiyar gidan, tana matsar kwalla da yarfe hannu.
a tsakiya suka sata direba yaja.
har kusa da kofar parlour Aunty direban ya kaisu kamar yadda Aunty'n ta umurce sa.
suka tallafe gefe da gefen kafad'ar ta suka shiga da ita.
d'akin ta dake side d'in suka shige da ita.
a gyare yake tsaf kamar da mai kwana cikin sa, dan kullum sai Aunty ta gyara shi.
suna zaunar da ita bakin gado.
Ammah ta ce
bari taje side d'in ta ta dawo.
Ammah nana fita,
Aunty ta shige bayi ta had'a mata ruwa mai zafi sosai cikin Bathtub ta fito.
ta dube ta tana kwance a bakin gado ta ce
"Taso muje d'iyar kirki ga ruwa na had'a a gasa jikin zakiji dad'in jikin."
fuska ta kwab'e zatayi kuka, Aunty ta ruko hannunta ta mikar da ita zaune.
rau-rau tayi da ido sai ga hawaye sharr.
wayar ta yayi haske alamun shigowar sako, Aunty ta mika hannu ta janyo watar.
number ne babu suna ta bud'e message mai kunshe da sako kamar haka
("Karkiyi amfani da ruwan zafi mai zafi sosai a kwai d'in ki a jikin ki, magani zakisha.")
Aunty tarika juya maganar a ranta, ta kalli da tausayin ta ya kamata, sai kuma ta yi saurin kawar da komai cikin ranta ta aje wayar tana binta da murmushi gami da lallab'i.
"Taso muje 'yammatan Ammie kiyi wanka."
tayi ta lallab'a ta taimaka mata ta mike suka shiga bayi.
batayi mata amfani da ruwan zafi sosai ba kamar yadda ya fad'a.
tasa tayi wankan sarki suka fito. tana sa kaya ta kwanta dan jikin ta yayi zafi sosai.
Aunty ta shiga kitchen dan sama mata abun da zata d'an tab'a.