← Book details Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 61

Sashe 31

Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kuraiba kuwa hauka ne kawai batayi ba, data sami labarin.
ta shiga mota tayi gidan su,
hankalin mamarta ma ya bala'in tashi, Hajiya Luba ta dubi d'iyar tata ta ce
"Wai ina cikin da kika ce min a kwai? shi wata nawa bai nuno kansa ba."
Kuraiba ta turo baki ta ce
"Ai zuban jini nake kullum dana je naga likita ya ce min wai zuban jinin da nake ne yasa cikin yake komawa baya, amma yana nan ina jin motsin shi."
"To tashi maza muje asibiti, na kai musu shaidar kina da ciki, taya zakiyi sake har wata tazo ta riga ki yin ciki,
kullum ina ta zuba idon jin kyakkyawan labari, sai kuma naji shiru, ai yanzu ya ci a ce cikin nan ya baiyana kansa,
Kuraiba kar kiyi wasa kar ki bari cikin nan ya fita, akwai babbar matsala fa, ta shi maza mu tafi."
"Mom ni gaskiya bazan je wani asibiti ba, ai ba a b'oye bane kowa yasan ina da ciki,
ki kira Mommy ki ce mata bazan zauna nan gaba akawo d'an shege gidan ace d'an Abdulrahim bane, tama san yadda zatayi tun da wuri."
"Ke dalla tafi can tashi muje na karb'o shaidar cikin ki, ba kiranta a waya zanyi ba, da kaina zanje na tabbatar mata nan gaba bazai yuwu a had'a sunan d'aki da d'an shege a matsayin d'an uwa ba, gara tun wuri ta sani."
ta zari mayafi ta ce
"Muje maza."
da fari Kuraiba taso bijerewa tafi asibin, Hajiya Luba tace fa sai sun tafi.
suna zuwa asibiti,
ana gwada ta aka ce bata da komai.
Hajiya Luba dake tsaye cikin d'akin gwajin ta ce
"Sake gwajin nan likita ciki fa a kwai shi tun ba yau ba."
"Hajiya ki kalla scanning dai baya karya, hasali ma mahaifanta bai tab'a d'aukar ciki ba, sannan akwai matsala ma a mahaifar nata, wanda bincike ya nuna yawan shashayen maganin hana d'aukar ciki barkatai ba'a kan ka'ida ba, shi ya kawo wannan matsalar, da kamar wuya ta iya d'aukar ciki."
Hajiya Luba ta shiga fifita da bakin mayafinta.
Likitan ya sallame su, suna fita Hajiya Luba ta ce
"Amma kin cuceni Kuraiba, kin ruguza min mafarkin dana jima nake yin sa,
wanda shi yasa nayi ruwa nayi saki wajen ganin kin zamo surukar Hajiya Halima sabo da na nuna mata iyakarta,
naci alwashin sai na mallaki dukiya dan na kuntata mata kamar yadda a duk san da na ganta nake shiga kunci,
sabo da tana auren mijin daya ninka mazajen mu dukiya shi yasa take fankama a cikin mu kawayenta, tana nuna ita mijinta mai dukiya ne,
shi yasa naci alwashin sai na mallaki dukiyar da take takama da shi, ni zan zamo mai dukiya ba nama son na kasance a karkashi wani,
shi yasa na zab'i had'a ki da d'anta dan na cimma burina, sai gashi kin ruguje min duk wani abin da na dade nake buri."
fuska Kuraiba ta yamutsa ta ce
"Lallai ma Mom wani irin tunani ne wannan da ke, to ni na auri Abdulrahim ne dan shine irin mijin da nake buri, bawai dan wani dukiya ba, duk da ban samu abun da nayi sammani tare da shi, ban damu ba dan gari da fad'i,
idan kayi ihu wani baiji ba wani zai jika,
ni kam dai nayi gidan mijina, ni nasan yadda zanyi na kwato 'yanci na, Mom ki aje wannan tunanin ma."
Hajiya Luba ta bud'e baki da hanci tana kallon d'iyar tata data wuce bakin get ta tari abun hawa ta hau ta tafi...

A cikin gidan gona ya gyara parking, kamar ko da yaushe Jaq da Tag suka iso gurin shi, bayan sun bud'e masa mota ya yo gaba suka biyo bayan shi.
suna shiga ciki yaja kujera ya zauna ya ce
"Ku fito da shi."
da sauri suka bud'e d'akin da Zaraddin ya ke ciki.
da sauri ya kare fuskarsa da tafin hannunsa, sakamakon hanken da ya zoyarcin cikin d'akin, wan da ya ke duhu babu ko kyallin haske, yana kwance a kasan turb'aya babu riga a jikin sa sa, sai gajeren wando kad'ai.
"Kai taso muje."
Tag ya fad'a yana janyo shi daga kwancen, ya mike tsaye ya tura shi waje.
suna isa gaban sa ya durkusar da shi kasa ya zube gaban sa.
ya mika hannu yana fad'in
"Miko min bulala."
da sauri Zaraddin ya mike yasa gwuiwowin sa a kasa yana fad'in
"Dan Allah Ya Abdulrahim kayi hakuri Wallahi na shiryu kar ka duke ni yau, d'azu ma sai da suke ni, kuma duk ayyuka na na gama akan lokaci,
ka tambaye su ko minti 20 banyi ba na share gidan gonan nan tas na nome in da ciyawa suka fito,
na canza ruwan kifi na wanke dem, na kwashe kashin kaji na zuba musu abinci da ruwa da magani, na share kashen shanu da raguna na zuba musu abinci da ruwan sha, zabbi da d'awesu da jimina Wallahi suma sai da na share gefen su na zuba musu abinci, kuma gasu nan ka tambaye su, kuma ka tambaye sauran ma'aikatan ma, daga nan kuma malam yazo ya koya min karatu, muna gamawa aka mai da ni d'akin nan ko minti 30 banyi da komawa ba yanzu haka."
ido ya zuba masa fuskarsa a mirtuke.
Zaraddin ya juyo ya kalli su Jaq yana cewa
"Ku gaya masa da gaske duk abun da na lissafa nayi, dan Allah Ya Abdulrahim ka taimaka ka mai dani gida, na rantse maka bazan sake aikata ko mai ba wlh na daina,
Wallahi tallahi ka tambaye su gaba d'aya na gama shiryuwa, ni nake fara fad'a musu lokacin sallah ya yi, ka tambaye su kafin su tashi suyi sallah na riga su,
ni nake buga kofar nan idan naji malam ya tada sallah sai su zo su bud'e min,
lokaci biyar akan lokaci baya wuce ni, ka taimaka ka mai da ni gida idan na sake aikata wani abun na yarda ka yi min hukuncin da yafi wannan, ni da shaye-shaye da 'yammata munyi hanun riga, har da abokan banzan ma har abada bazan sake ba, wlh na dai na kayi hakuri."
"Kira min malam."
Abdulrahim ya fad'a yana duban Tag.
da sauri Tag ya fita ya nufi gefen da sauran ma'aikatan gonar suke, batare da b'ata lokaci ba suka dawo da wani dattijo.
malamin ya mikawa masa hannu suka gaisa kana ya dubi malamin yana cewa
"Ya kai izu nawa yanzu."
da sauri Zaraddin ya ce
"Wallahi nafi ashirin saura kad'an na haura izu talatin."
"Ban tambaye ka ba."
ya fad'a fuska ba wasa.
Zaraddin
yayi saurin kunshe bakinsa yana tsilli-tsilli da ido, ya kwantar da kai kamar maraya.
malamin ya ce
"Eh yana daf da kaiwa izu talatin, kuma yana ganewa sosai yanzu."
kai ya jinjina sannan ya ce wa malamin
"Zaka iya tafiya."
malamin na tafiya ya mai da dubansa ga Zaraddin ya ce
"Idan ka kai izu sittin ka shirya zaka ko ma gida."
yana gama fad'in haka ya jefar da bulalan hannunaa ya mike ya fita.
Zaraddin kamar ya fasa ihu yana ji yana gani suka jashi suka maida shi d'akin duhu suka kulle shi......!

"Feeryal yi sauri ki fito ki shirya mana mu tafi, sai juya jiki kike duba kiga 11 har ta gota, sai azahar kike so mu tafi."
cewar Hajja Umma data ke ciro mata kayan da zata saka, su tafi asibiti don yin awu.

Feeryal ta fito daga bathroom d'aure da towel, tana gyara zaman towel d'in da yaso kasa mata sakamakon cikin ta daya tosa, watannin cikin biyar ke nan.
Hajja Umma ta ciro mata doguwar riga tana d'ago rigar, magani ya zube kasa.
Hajja Umma ta aje rigar bakin gado ta sunkuya ta tattaro maganin tana fad'in
"Me kuma ya kawo magani nan."
ta kwaso magungunan tana kallon su
"Wannan ai maganin da masu ciki suke sha ne,
wannan ne ma ban san amfanin sa ba, Feeryal maganin ne bakya sha kike tarasu anan, ko ba su bane?."
Feeryal ta zauna kan kujerar Morro tana fad'in
"Ina sha fa Hajja Umma ba ke kike bani na sha ba."
"To ai shine nima nagani to ya akayi wad'an nan suka zo nan."
mai ta d'auka ta soma shafawa tana cewa
"Wannan maganin fa Sahab ne ya bani ranar daya dawo da ni d'in nan, wai narika sha kullum ni kuma nasan lafiya ta kalau shine na ajiye."
Hajja Umma tayi shiru a ranta take fad'in
"Yama san da cikin, kafin mu mu sani ke nan ma."
a fili kuwa cewa tayi
"To yi sauri ki shirya, mu tafi bari na zo."
tayi waje...

Lagos...
Chapter 31 · 0% Book details