← Book details Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 61

Sashe 25

Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana fita sashin Aunty ta zarce.
Aunty na zaune a parlour tana sauraran karatun alkur'ani dake tashi a tv.
Umma karima ta shigo babu ko sallama ta nimi guri ta hakimce kan kujerar da yake fuskantar ta,
ta d'aga kafa ta d'aura d'aya kan d'aya, tana girgizashi tare da bin Aunty da wani kallon wulakanci.
sannan ta ce
"Hajiya Fatima ya gajiya ya fargaba, tun yanzu naga kinyi kwalas har kin tsare ne haka da wuri, tun bakiga karshen wasan ba,
bakiga ko mai ba muzuba mugani, ki dakance ni ina kan zuwa ta kanki."
tana kaiwa nan ta mike ta nufi kofar fita daga parlour'n.
Aunty tabi bayanta da kallo tana shirin fita daga parlour'n Aunty ta ce
"Shi aure da kike gani iko ne na Allah dan abune mai rai,
da rayuwar sa da mutuwar sa duk daga Allah suke,
Allah ne kad'ai keyin yadda yaso da shi ba d'an mutum ba, ina sauraran ki Hajiya Karima!."
Umma karima tayi wani dariyar rashin mutunci, kana ta kad'a kai tayi waje.

Daddy na Saudi ya sami labarin,
Aunty kam taki gaya masa da ma ta ce sai ya dawo, Ajmaal ne ya sanar masa da abunda ke faruwa,
Daddy yayi masifa fari yayi baki, ya kira Abdulrahim ya yi masa kaca-kaca ya nuna masa b'acin ransa da bai tab'a gani ba.
shi dai bai ce masa kala ba har ya kashe wayar.
ko da Daddy ya kira Mommy kalmar da ya iya fad'a mata ke nan
"Kin kyauta Hajiya Halima."
daga nan bai kara cewa komai ba ya kashe wayarsa.

Kwana uku da faruwar lamarin, kafin 'yan Abuja suka sami labarin.
Abba ransa ya b'aci matuka ya kira Daddy ya ce zai tura a d'auko Feeryal bazataci gaba da zama a gidan ba, tun da suka kasa iya riketa suka maida ta karamar bazawara.
Daddy ya yi ta bashi hakuri,
ya ce idan ya dawo gida ko mai zai dai-dai ta.
Abba ya tire yace sam yau za'a sata a jirgi a kawo ta Abuja shi zai nima mata mijin da zai iya riketa.
Daddy bazai ja da Abba ba a matsayin sa na sirikinsa haka yabar zancen akan sai ya dawo.
a ranar kuwa Abba ya sa aka shirya mata tafiya Abuja.
Feeryal tana ta murna zataje taga Hajja Umma da Maryam da suke ta waya da ita tun da safe,
dan Maryam d'in tana gida, anyi posting d'in inspector Nasir ogun State kuma tana da tsohon ciki, shi ne ta dawo gida sai ta haihu kafin ta koma.

Sai da a kazo d'aukar ta kafin jikin ta yayi sanyi ganin zata rabu da Ammie'n ta, har da kukan ta.
duk da Aunty taji ba dad'i rabuwar su amma tasan zata sami saukin maganganun da ke kai kawo a cikin gidan.

Karfe 12 na rana motan gidan Alhaji Tahir Abbas ya isa airport d'aukar Feeryal.
Hajja Umma da Maryam suna tsaye a farfajiyar gidan suna jiran isowar ta.
suna isowa tun kan motar ta paka suka yiyo gurin motar suna fad'in
"Oyoyo Feeryal."
Feeryal ta fito cikin farinciki suka rungume juna.
ta bud'e baki tana kallon Maryam da katon cikin ta,
"Laa Aunty Maryam dama kin kusa haihuwa ne?."
ta fad'a da mamaki tana rike hab'a da waro ido kan cikin tana dariya.
Maryam tayi dariya taja hannunta, sukayi ciki Hajja Umma tana ta zolayar ta...

Ranar har dare suka kai suna hirar yaushe gamo.
da daddare suna kwance a dakin su na da, Maryam tana manne da waya tana waya da Inspector Nasir.
ta mikawa Feeryal wayar da Nasir ya ce a bata su gaisa, dan tun tasowarta ya sami labari daga matar tasa.
Feeryal takarb'a ta gaishe shi a takaice ta mika wa Maryam wayar.
Inspector Nasir yayi dariya jin tayi saurin mikawa Maryam wayar, ya ce
"Wai har yanzu mutumiyar a haka take dai bata sauya ba, kamar mai jin tsoron magana,
ni dai daga yau kullum zanrika tuni kada wani yazo ya kuma mana shigar sauri, dan har gobe Major Sadam yana son ta,
bazai zo ba har sai tayi idda, in Allah ya yarda bayan idda da sati za'a d'aura auren nan, ke dai kiyi ta mana fadanci."
Maryam ta ce
"Tom Allah ya nuna mana, amma ai za'a barta ta huta tukun, daga yin idda sai aure kuma ai yayi wuri da yawa."
da sauri Nasir ya ce
"Aa wife kar muyi haka dan Allah wannan karon ki mara mana baya kin fi kowa sanin halin da Major Sadam ya shiga a lokacin da ya rasa ta,
dan Allah ki taimaka mana."
numfashi ta sauke ta kalli Feeryal dake kwance tana buga game a wayarta ta ce
"Duk da yarinya ce har yanzu amma addini ya bata dama a wannan karon ta yi zab'i da kanta, sannan iyaye su taimaka mata wajen duba ingancin zab'in nata,
idan har Sadam yana cikin kundin kaddarar ta zai aure ta."
"Wife auren Feeryal fa duka-duka wata biyu da kwanaki ne, har yanzu iyaye suna da damar kuma zab'ar mata miji, na tabbata idan Abba ya kawo mata Sadam a matsayin miji bazata ki ba, dan haka da wuri zamuzo mu sami Abba Major Sadam zai rike Feeryal ruko bana wasa ba dan yana sonta."
"Uhum a dai bari lokacin yayi ni dai nafi son a barta, tazab'i wanda ranta ya kwanta da shi kar a dawo gidan jiya."
ya ce "Hmmm Wife ke dai ki bamu gudumawa wajen fahimtar da ita irin son da Sadam ya ke mata, yanzu ya baby na yake."
shafa cikin tayi ta ce
"Gashinan sai motsi yake."
"Had'a ni da shi naji motsin sa."
ta zaro wayar ta d'aura kan cikinta, kiss yayi wa cikin ta waya yana fad'in
"Muna maraba da zuwan ka abar kauna."
ta zaro wayar ta kai kunnenta tana fad'in
"Ni na matsu ya fito na huta."
"Saura kad'an ai EDD ya cika, insha'allah bazaki wuce EDD ki ba sai kiga ma a daren nan in Allah ya yi ikon sa,
ki haihu, in kin wuce ma bazaki kai kwana goma nan gaba ba, saura 6 days fa."
ta ce
"Ni dai kayi min addu'a Allah ya kawo min da sauki."
sun jima sosai suna waya Feeryal kam tuni tayi bacci.

Washegari Abba Hajja Umma Maryam da Feeryal duk suna kan dinning, suna breakfast.
Hajja Umma ta rike baki ganin abun da Feeryal ta maida hankali kan cinsa, ta ce
"Wato dai har yanzu hali na nan, shi yasa baki karu ba jikinnan nanan kamar tumatur."
murmushi tayi tana kai loman cake bakinta.
Abba ya yi dariya ya ce
"Ta karu mana ke bakiga takara girma ba, ai dole ma na kara sadaki, tun da shi wancan ya kasa iya rikewa."
dariya tayi tana d'agawa Hajja Umma gira.
Hajja Umma ta yamutsa fuska tana fad'in
"Ahaf ni na dad'e ina cin moriyar."
da wasa da dariya suka watse a kan dinning d'in...

Bayan kwana biyar Maryam ta tashi da nakuda,
nan da nan aka garzaya da ita asibiti.
cikin ikon Allah ta suntulo d'anta na miji.
zo kaga murna gurin su Hajja Umma, Feeryal baki yakasa rufuwa, ana fitowa da baby'n ita tariga kowa karb'a.
tana kallon yaron da ya mugun burge ta, sai hotuna take musu.
takira Aunty video call, Aunty tayi murnar ganin sabon baby.
Inspector Nasir da ya kira wayar Maryam video call yana hannunta ta d'aga.
ta nuna masa d'ansa kamar yasa hannu ta cikin wayar ya d'auke shi,
yayi ta murna yana kissing d'in sa ta waya.
da kyar ta baiwa Hajja Umma shi.
ko minti goma bata bari yayi ba ta kuma karb'ar sa.
tuni asibitin ya soma cika da 'yan'uwan Inspection Nasir dana su Abba, da yamma aka sallame su dan lafiya lau ta sauka, ita lafiya jaririn ma lafiya.
sun fito daga cikin asibitin ana kokarin shiga mota Major Sadam ya iso asibitin.
ya paka motarsa ya fito.
cikin girmamawa yake gaida Hajja Umma da sauran mutanen, kana ya juya ga mai jego cike da farin ciki yake fad'in
"Sannu da kokari muna godiya da samar mana baby."
Maryam tayi murmushi.
Hajja Umma ta dunguri Feeryal dake rumgume da yaron ta ce
"Mika masa d'an nasu ya gani."
a hankali ta taka zuwa in da yake ta mika masa yaron, ya mika hannu ya karb'e shi idanunsa a kan ta.
kaucewa tayi gefe ta tsaya dan kallon da yake mata yayi mata yawa.
motoci biyu ne a gurin ga mutane kuma da yawa, ya ce wa Hajja Umma su shigo motarsa ya karasa da su gida.
mejego Maryam da Hajja Umma suka shiga gidan baya,
ya tako gaban Feeryal ya mika mata yaron yana fad'in
"Muje Madam."
tana tsaye har ya shige mator sai da Hajja Umma ta leko ta ce
"Shigo mu tafi mana Feeryal."
ta tako a hankali tana kokarin wucewa in da su Hajja Umma suke ya bud'e mata gefen gaba, ya ce
"Shigo nan."
a sannu taja kafarta ta shige motar ta zauna, tana gyara rukon jaririn.
ya fita daga mazaunin sa ya zaga ya rufe mata kofar, kana ya dawo mazaunin sa ya ja motar suka nufi gida...
suna isa tayi saurin fita ta nufi ciki..

Da Feeryal ake jegon dan kullum tana like da jariri, ana gobe suna Aunty ta zo.
Feeryal tayi ta murna.
ranar suna akayi suna nagani na fad'a, iyayen Inspector Nasir sun nuna bajin ta kwarai da gaske, dan ba karamin kaya sukayiwa mai jego da d'an ta ba.
bayan suna da kwana biyu Aunty ta koma...
haka rayuwa yaci gana da tafi, jego dai da Feeryal akeyi..
Chapter 25 · 0% Book details