← Book details Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 61

Sashe 44

Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Parking lot ta isa ta shiga d'aya motar data d'auko key'n sa.
ta ja motar mai ganin side d'in ya bud'e ta fita.
tana kokarin juya motar ta saita hanyar nufa babban get,
taji anyi knocking glass d'in motar.
da sauri ta d'ago shi ta gani, tana shirin zuge glass shi ya rigata bud'e murfin.
ido cikin ido suka kalli juna.
"Koma ciki."
ya fad'a idanunsa cikin nata.
saurin janye idanunta tayi, ta cuno lips d'in ta ta ce
"Wannan motar Ammie'na ne."
gira ya d'a alamun ya fahimci in da maganar nata ya dosa, wato tunanin ta wancan motar Mommy'n sa ce.
hannu ya mika ya zare key'n motar ya ce
"Wannan motar Daddy ne ya siya ba ita ta siya ba, dan haka fita, kaf parking lot d'in ta duk motocin ciki Daddy ne ya siya kar kiyi gigin d'auko wata."
da sauri ta talle shi taji haushin maganar nasa, nan da nan idanunta suka ciko da kwalla.
wato gori ya yi mata ita bata da ikon d'aukar wani mota cikin gidan nan, tun da ita ba 'yar gidan bace.
duk yadda taso danne kukan kar tayi a gabansa, ina sai da kukan ya kwace mata, ta fita da gudu tayi ciki tana toshe bakinta.

Ta wuce Aunty a parlour da gudu tayi cikin bedroom nata.
ta zube kan gado tare da fashewa da kuka.
karo na farko data ji gorin wani ya mata zafi.
tun tashin ta da ta fahimci wace ce ita, duk gorace-goracen da ake mata kazamin gori mai muni. bata tab'a jin zafin gori irin wanda ya mata yau ba, sai taji nashi ya fi na kowa mata zafi.
ta sha kukan ta tayi shiru dan kanta, tamike tana share hawaye da turo baki, ganin Ammie'n ta bata biyota ba bare ta zo ta rarrashe ta kamar yadda ta saba.
ta fito parlour tana kumbura a dole tayi fushi ba'a zo an rarrasheta ba.
Aunty ta bi da ido har ta karaso ta zauna can gefe tana kuma kumbura baki tana jan hanci.
"Je ki sako abinci ki ci."
cewar Aunty tana duban ta.
"Na koshi."
ta fad'a a shagwab'e.
tana kuma tura baki ganin har ta fito Aunty bata tambaye ta me ya same ta ba.
Aunty ta girgiza kai tana mai da idanunta kan TV.
Feeryal ta cika fam Aunty tana kallon ta da witsiyar ido.
wayan ta ne yayi ring ganin Miemie ce,
kamar bazata d'aga ba har ya kusa yankewa kafin ta d'aga.
Miemie ta ce
"Feeryal bai barki ba ko? gashi TJ ya ce sai kin zo da kanki kafin ya bada d'inkin ki,
kin san halin sa sai yace wai so yake ya ganki bazai bawa kowa ba."
"Zan zo ina ruwan shi da ni da zai hanani zuwa."
ta kashe wayar.
Aunty ta mike tashige kitchen tana girgiza kai da yin murmushin da ita tasan manufarsa.
Aunty na shiga kitchen ta mike ta nufi kofa ta fita.

Tana fita tanufi babban get masu gadi suka bud'e mata karamar kofa ta fita.
a hankali take takawa eriyan shiru babu kowa.
wani ta hango yana tsaye da waya a kunnen sa, yana ganin ta ya soma tako wa in da take.
"Sannu 'yammata."
ya fad'a san da ya iso in da take.
ta kalle shi tana kawar da kanta ita ma tace masa sannu.
"Am na ce ba ko taxi kike nima ne?."
kamar bazata amsashi ba sai kuma ta ce
"Eh."
ya ce "Okay ni ma taxi nake jira amma kinsan unguwa kamar wannan taxi basu fiye shigowa ba, kowa zaki ganshi a motar gida ne ya ke zuwa, ni ma na kawo ziyara ne so motata kuma ta d'an sami matsala, dole a taxi zan koma,
amma yanzu nayi waya da wani direban taxi ya ce min yana kusa da nan zai iso yanzu, mu d'an jira ya karaso, amma ina zaki je ne ke?."
ta ce
"TJ plaza kan titin gaba in zaka shigowa wannan titin."
ya ce
"Okay nan kusa ma zakije, yanzu taxi zai iso,
am na ce amma ke ba 'yar Alhaji Abubakar AA FIYA ba ne."
juyowa tayi ta kalle shi sai kuma ta kuma kawar da kanta."
"Yi hakuri fa na fiya dambaya ko, naga bakiyi kama da 'yan gidan bane, ko ke 'yar matar sa da akace ya auro ta daga wata kasace, dan kin fi kama da 'yan ta can kasashen labarabawan nan."
batayi magana ba tana jinsa.
ya danna waya ya kai kunnen sa yana cewa
"Kayi sauri mana dan Allah muna jiranka, gashi ka sami karin fasinja."
yana sauke wayar taxi tana shigowa titin, koda motar ya karaso mutane biyu ta gani cikin motar,
d'aya a baya sai direba a gaba.
mutumin da suke tare da shi ya zaga ya shiga gaba yana fad'in, "Shiga da sauri muje kinga ya d'auko fasinja."
ta bud'e gidan baya ta shiga a hankali tana rufa kofar yaja motar da gudu.
shiru tayi a hankali zuciyarta yana d'an harbawa.
sosai motan ke sharara gudu, ganin sun kusa da plazan da zata sauka ta ce
"A TJ plaza zan sauka."
suna zuwa dai-dai gurin ganin bai sa alamun tsayuwa ba tayi saurin cewa
"A nan zan sauka."
babu wan da ya kula ta sai kara gudun motar da akayi.
da karfi ta ce
"Direba na ce ma can zan sauka, ka tsaya na sauka ana."
da sauri ta had'e maganar ganin na gefen ta ya ciro bindiga ya nuna mata.
zabura tayi ta matsa gefe tare da fasa kara tana toshe bakin ta.
tsawa ya buga mata ya ce
"Idan kika mana ihu sai na fasa kanki anan rufa baki!."
zabura ta kuma tana dad'a toshe bakinta da tafin hannunta jikin ta na rawa.
"Yi sauri muje kara gudu."
cewar na gaban wanda suka shiga mota tare da ita.
shi kuma d'aya na bayan wanda suke tare da ita ya d'aure mata fuska da bakin kyalle.
sannan ya kwace wayar hannunta ya kashe ya tura a aljuhun sa.
Feeryal jikinta na kakkarwa sosai, sabar yanda ta firgita ruwan hawaye ya d'auke a idanunta.
sosai suka tafi suka fita wajen gari sosai.
kafin taji alamun motar ta tsaya, suka sauko suka fito da ita.
suka jata zuwa bayan wani katon dutse da ciyayi sosai a gurin.
sai da suka shige da ita mab'oyar, kafin suka bud'e mata fuska.
Feeryal ta razana da inda ta ganta, gaban wani katon mutum mai katon tumbi, yana zaune a kasa kafadunsa a mike ya aje katon ciki gaba.
wasu kattin biyu na tsaye a kansa,
dukansu da shi suna hura sigari.
ga kuma mutane ukun da suka taho da ita suma suna tsaye.
ogon nasu dake tule a kasa ya ce
"Kai wannan zazzafar fa ita kuka samo, gaskiya wanan mutumin ya iya haihuwa ga dukiya ga kyakyawan 'ya'ya gaskiya nera tayi,
wannan ba karamin hutawa zakayi da ita ba, matso nan yarinya matso."
ta kuma zabura tayi baya tana girgiza masa kai, cike da mugun tsoro.
"Ke ba ance ki matso nan ba!."
d'aya daga cikin munen ya fad'a yana kokarin cafkota.
"Aa rabu da ita yau ai muna tare."
"Gaskiya oga zazzafa ce idan ka more, ni zan biyo baya kai gaskiya wannan taji kayan had'i."
cewar d'aya daga cikin wanda suke tsaye suna ta bushe bushen hayaki.
suna ta binta da mayataccen kallo.

A b'angaren su Miemie kuwa har suka gama zaman su basuga ta zo ba, TJ ya basu d'inkin su har da nata suka juyo gida.
sashin Aunty suka shige suna kiran Feeryal, Aunty ta fito tana fad'in
."Ku duba ta a d'aki tana ciki."
suka shiga bata nan, har bayi Miemie ta leka bata nan.
suka fito suna gayawa Aunty bata ciki.
Aunty ta ce
"To ina tayi."
kamar da wasa ta gwada number taji shi a kashe......!

Kamar da wasa fa aka nimi Feeryal aka rasa,
hankalin Aunty ya yi masifar ta shi,
Daddy ma haka.
da karfe 5 Abdulrahim ya dawo daga asibiti.
yana shiga yako kowa a tsaye a kan kafarsa, Daddy yanq rike da waya yana ta kai kawo.
ya kashe mota ya fito tun kafin ya karaso in da suke Hajiya take fad'in
"Gara da Allah yasa ka dawo Abokinn turawa, wasu maysiyata sun sace wannan yarin ya Feeryal, tun safe ake niman ta ashe d'auke ta sukayi sai yanzu suka kira Abubakar suke gaya masa, sunyi garkuwa da ita."
wani irin bugawa kirjinsa yayi da karfi,
har sai da yakai hannu ya dafe dai-dai saitin zuciyar sa, a hankali ya furta "Beuaty!."
Hajiya ta ce
"Eh ita bity sun sace ta."
Daddy ya dube sa yana fad'in
"Sun kirani sanar wa kawai sukayi min na san da sun d'auke ta, amma basu fad'i bukatar su ba,
ina shirin tambayar su suka kashe wayar, da sun fad'a ko nawa ne sai a basu yanzu a karb'o ta."
Daddy bai rufa baki ba wayar Abdulrahim yayi ring ya d'ago wayar b'oyayyiyar number ce,
da sauri yayi picking call d'in ya kai kunnen nan sa.
"Dr AA FIYA maraba da dawowa muna shirin sanar maka, sai tsofin ka suka riga mu, kasami labarin yadda ya dace ko mu kara yi ma bayani."
rike wayar yayi da karfi zuciyar sa yana tafarfasa.
cikin fusatacciyar murya ya ce
"Nawa kuke bukata? ku sako ta kada wani abu ya same ta!."
dariya aka kece da shi
"Hahaha tun da wuri haka yau dai da ita zamu kwana, wannan laushin jikin da kyan sura ai dole mu d'ana,
to meye na fusatar kai da ba matar ka bace yanzu,
amma fa kayi asarar had'ad'd'iyar mace, tun da bakayi mu bari mu d'an more,
ka saurare mu gobe zamu sanar maka."
da karfi cikin hargagi ya ce
"Wallahi! idan kuka tab'a ta sai na kashe ku zan yi muku kisan wulakanci!."
kashe wayar akayi muryoyi da yawa suna dariya.
Chapter 44 · 0% Book details