← Book details Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 61

Sashe 61

Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel · about 5 min read

Da sauri ya sauka a mota yana waige gami da kwad'a mata kira
"Beauty Beauty Beauty!! ki na ina!!!."
yayi maganar cikin karaji sosai.
da sauri ta zabura daga in da take zaune a keb'abb'en guri, ita da su Chuchu da Chulu,
wanda a gurin aka ajiyeta duk abun da ake sunata janta da hira bata san duk abun da ya faru ba.
da sauri ta nufi in da take juyo sautin muryarsa,
da karfi ta amma kiran nasa
"Sahaaab kana ina."
Chuchu ta ce
"Dakata Feeryal bari mu kai ki in da yake."
suka ruko hannunta kamar kiftawar ido ta ganta a bayan sa.
"Sahab!."
ta fad'a da karfi tana nufowa in da yake da gudu.
shima da gudu ya nufo ta ya rungume ta yana huci.
cikin kakkausar murya mai cike da karaji sosai yake fad'in
"Na rantse idan kuka cutar min da mata da 'yata dake cikin ta,
duk bazan kyale ku ba,
me yasa zaku d'auke ta kuyi gaggawar cireta cikin lamarin ku,
kada ku sake sakota cikin lamarin ku idan kuma ba haka ba, wlh duk bazan kyaleku ba,
d'aya bayan d'aya sai na kashe ku."
daga saman su sukajiyo magana
"Garkuwa a gafarce mu, ka d'auki matar ka kuje, daga yau babu mai kuma shiga lamuran ta."
a fusace ya ce
"Kunyi wa kanku."
ya kama hannunta suka nufi gurin mota ya bud'e mota ya sakata shima ya shiga.
ya ja motar a fusace.

Tun a hanya nakuda ya kamata, sabo da firgicin data shiga, dan haka direct asibiti ya shige da ita.
suna isa bada b'ata lokaci ba ta suntulo 'yarta mace.

Bayan wani lokaci...

Motar Abdulrahim ne ya shigo gidan in da suka kawo wa su Aunty ziyara.
suka fito a motar da ka gansu kasan nutsuwa da kwanciyar hankali yasami masauki a tare da su.
Feeryal takara kyau da girma,
shi kansa gogon ya kara murjewa.
Sheerah na rike a hannun Abdulrahim suka shiga sashin Aunty.
Zahra Saddeeq Haydar suna ganin su suka taho da gudu suka rungume su, suna musu oyoyo.
Zahra da ke da shekaru biyar ta karb'i
Sheerah dake hannunsa tana mata oyoyo.
Aunty na zaune tana ta binsu da murmushi.
suka karaso ta karb'i Sheehra tana mata tsalle tana kyakyatawa.
Daddy ya shigo duk yaran suka mike suka tafi da gudu suka rungume shi.
shima ya rungume su da farinciki, yana d'aga su yana cillasu sama.
yaruko hannayen su ya karaso yana amsa gaisuwar da su Feeryal suke masa.
ya dube su cikin kula da ganin yadda rayuwar su yake tafiya cikin saiti ya ce
"Allah ya muku albarka da ku da 'ya'yan ku baki d'aya."
Aunty ta amsa da amin amin.
bayan sun gaisa, suka d'unguma da yaran sukayi sashin Mommy.
suna shiga yaran suka rungume ta suna yi mata oyoyo.
Zahra ta mika mata chocolate d'aya dake hannunta tana ciki ta ce
"Mommy ga tsaraba."
Mommy ta girgiza kai tana fad'in
"Aa na gode kici ni ina azumi."
Zahra ta rike hab'a tana cewa
"Watan azumi ya kama ne?, yau fa Saturday ne kuma Ammie ta ce ba'a azumi sai ranar litinin da alamis, to ke azumin ranar Saturday kike?."
ta karasa maganar tana dafe kumatu, irin abu ya baka mamakin nan.
murmushi Mommy tayi ta janyo su dukansu jikinta Zahra Saddeeq Haydar Sheehra.
sannan ta ce
"Ina azumi Zahra azumi sittin zanyi, na kashe muku 'yan'uwan ku da nayi."
da sauri Feeryal ta ce
"Mommy ki dai na fad'a musu dan Allah."
Abdulrahim daya karaso ya zauna ya ce
"Mommy babu amfanin fad'an kada ki saka musu hakan a ransu."
Mommy ta girgiza kai tana share kwalla ta ce
"Ku yafe min Feeryal Abdulrahim, bazan dai na rokon yafiyar ku ba,
yaushe nima zaka bani 'ya'yan ka na rike, kana gudun kada na kuma kashe maka 'ya'ya ko,
wlh nayi nadama ina bakinciki da abunda na aikata a baya."
ya ce
"Mommy bai kamata ki rika dawo da abin da ya wuce ba, mu tuntuni muka mance,
idan ta haifi wannan cikin za'a baki, dan Sheehra Aunty nayi alkawarin bawa itama,
dan 'ya'ya biyar nayi niyyar bata."
Mommy ta jinjina kai tana cewa
"Hajiya Fatima ta cancanci fiye da haka."

Suna fita daga parlour'n Mommy ta matse shi a jikin bango.
ta ce
"Me kace idan na haifi wannan cikin wani cikin so kake kace akwai wani ciki a jikina?."
gira ya d'aga mata yana kashe mata ido d'aya.
da sauri ta shiga bugun kirjin shi tana fad'in
"Ni dai Allah na gaji ka tsai da min haihuwar nan haka."
da sauri ya rungumo ta yana cewa
"Kina haifo wannan zaki huta,
kafin ki haifo mana namu,
wan da zamu rika ganin sa a kusa da mu,
yanzu zamu barwa Aunty wannan, taji a ranta itama batayi rashen 'ya'ya ba."
baki ta turo tana lafewa a jikin sa.
bakinsa ya kawo saitin kunnen ta ya ce
"Fad'a min abin da ke cikin zuciyar nan naki."
kwayar idanunta ta d'ago ta kalle shi, sannan cikin siririyar muryarta mai sanyi ta ce
"Meye a cikin?."
hancinta ya ja ya ce
"So na mana amma baki tab'a ce min kina so na ba."
ido ta lumshe tana manna kanta a kirjin sa.
ya kawo bakinsa dai-dai santin kunnen ta ya furta mata
"I love you so much in my life, ke rayuwa ta ce Beauty."
ido ta kuma lumshewa tana shigewa jikinsa.
tana jin wani irin sanyi mai sa nutsuwa yana ratsa jini da jijiya gami da kwakwalwa da rai da zuciyarta......

Ai kuwa kamar yadda ya fad'a. wa Aunty suka barwa Sheehra, suka koma gida suka soma rainon cikin da za'a baiwa Mommy idan an haifi abin da ke cikin.....!

*Tammat bi hamdullah*

Anan na kawo karsher wannan littafi mai suna FEERYAL.
ina fata za'a amfana da dasusan da ke cikin sa.
ya rabbi kasa mufi karfin zuciyar mu ka iya mana da iyawar ka kar ka barmu da dabaran mu.
mu had'u a littafi na na gaba.

Kai ga yadda suka kure ido dan son jin sunan littafin😂
bafa zan fad'i yanzu ba dan zan iya samin masu tashi na a bacci🤗
ka-ki tuntub'eni ta wannan number 👉🏻 08034690723 daga zaran na fara sakin sabon book zaka-kiji.

Masu niman HAMDAH da KARSASHI da sauran book's d'ina kuma ku neme ni ta nan don samin litattafai na 08034690723
Ina maraba da ku masoya na🤗
Chapter 61 · 0% Book details