Sashe 54
Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washegari tana fitowa ta hango shi shi da Uncle Aliyu, ta kauce bata bari sun had'a ido ba.
san da ta shiga gaida sarki Al'Ayzaan, takuma ganin su tare.
mamki take ganin yadda shi ya fita shiga da fita a cikin gidan.
suna gama gaisawa ta koma.
karfe goma da rabi dattijiwa kakarta Ummuh ta shigo ta ruko hannunta kamar kullum tun san da ta zo gidan,
suka fito kan babban dinning mai zagaye da kujeru talatin, an jera abinci kala-kala kan dining d'in,
jikoki da 'ya'ya sune zagaye da gurin,
tun kafin ta karaso ta hangosa zaune shi da wannan d'an uwan nata abokin aikin sa, da wasu mazan suna zagaye da shi suna ta yi masa magana da harshen larabci,
ga takardu a gaban sa da alama dai hannu yake saka musu cikin takardun.
a sannu ta karaso suka rika mikewa suna rumgumar ta, kamar yadda larabawa suka saba wajen gaida d'an uwan su,
har da mazan gurin.
fuska ya d'aure yana aika mata wani kallo.
ta kawar da kanta kusa da Rubah ta zauna aka zubo mata abinci kala-kal,
batawa ni ci abincin kirki ba dan dama ita ba ma'abociyar cin abinci bane, sannan bata saba da cin kalar abincinsu ba,
abun da zata iya ne ta d'an tab'a, ta tsulale ta bar gurin, dan kallon da yake ta jefa mata ya hanata nutsuwa.
Da rana suna zaune da 'yammatan gidan, dattijiwa kakarta Ummuh tazo ta ruko hannunta suka tafi parlour'n Al'Ayzaan.
anan suka tadda mahaifinta zaune.
kakar nata ya dafa kansa yana sanya mata albarka, kana ta nimi guri ta zauna.
ya dube ta da kulawa ya na cewa
"Yake jikata ki shirya gobe zaki koma da mijinki, zai kuma dawo mana da ke bayan wani lokaci."
Feeryal ta d'ago da sauri dan ta ji wani abun da ya fad'a.
Uncle Aliyu ya ce
"Gobe idan Allah ya kaimu zaki koma da mijin ki, idan an kwana biyu zai dawo da ke ki kuma ganin danginki."
Feeryal ta sunkuyar da kai tana tankwashe 'yan yatsun ta, ko ba'a fad'a ba tasan shirin nan na Sahab ne.
Goma na arziki suka had'a mata
in da aka mallaka mata dukiyar mahaifiyarta.
akace idan suka dawo Nigeria za'a transfer dukiyar ta dake aje a banki zuwa bankin Nigeria.
Ummuh ta bata wani sarkar gold ta ce ta kaiwa Ammien ta.
motoci goma na masarauta suka fito rako su airport.
tana rike a hannun dattijuwa kakarta Ummuh ta bud'e motar da yake ciki shi kad'ai ne a baya sai direba ta ce ta shiga, ta shiga ta zauna Ummuh tayi musu fatan isa gida lafiya,
yana amsa mata da larafci.
Ummuh ta share kwalla dan ba shakka bataji dad'in rabuwar su ba.
motocin sukayi layin fita suna haurawa titi ya juyo inda take,
ya janyo ta jikinsa cikin yin kasa da murya ya ce
"Kar na sake ganin kin tsaya wani kato ya rungume ki."
da sauri ta d'ago ta kalle shi ya jinjina mata kai alamun tabbar wa.
kasa tayi da idanunta bata ce ko mai ba, yana rungume da ita har suka isa airport.
ai kuwa da suka sauka ana ta rungumar juna na bankwana duk namijin da zai rungume ta sai ta matsa ta bishi da murmushi,
ji tayi an sakalo ta ta gefe ta juya da sauri shine ya rungume ta ta gefe a haka suka shiga jirgi.
Karfe 6 na yamma suka iso Nigeria.
sai da suka sauka ya kira Ajmaal ya ce ya zo airport da mota.
Ajmaal na kokarin fita da d'aya daga cikin motar Abdulrahim d'in, Daddy ya tsare shi ya ce
"Ina zakaje da motar nashi, wai ina shi Abdulrahim d'in ne, yau kwana biyu ke nan ban sashi a idona ba, ko yana wani aikin ne a asibiti?."
Ajmaal ya ce
"Nima tun shekaran jiya dana ganshi ban kara ganin sa ba, yanzun nan ya kira ni ya ce nazo da mota airport, inaga ya d'anyi tafiya ne."
Daddy ya ce
"Jeka ka d'auko shi."
Ajmaal ya ja motar ya fita.
Ko da ya isa airport d'in yayi mamakim ganin sa da Feeryal,
wan da yaji ance sai tayi wata kafin ta dawo wato shine yaje ya d'auko ta ya dawo da ita.
Ajmaal ya yi murmushi yana girgiza kai.
ya sauka ya bud'e musu motar yana yi musu barka da hanya, kana ya d'auki kayan su ya sa a bayan but.
ya shiga ya jasu suka nufi AA FIYA STREET.
Aunty na zaune sai ganin ta tayi, mamaki ya cika ta tace daga sama ko kasa,
sai kuma ta rungume ta tana yi mata oyoyo.
"Feeryal wani irin dawowa ne wannan babu sanarwa, ya akayi haka, ko Yaya Aliyu fa bai sanar min da dawowar naki ba, ke da zakiyi wata guda sati d'aya kuma sai ki dawo."
"Ammie nima bansan ya akayi ba Uncle da tsohon nan suka ce wai nabi Sahab mu dawo, in an kwana biyu zai kuma mai dani."
Aunty ta rike hab'a da mamaki tana murmushi.
muryar Daddy suka jiyo
"Au shi Abdulrahim d'in dama can Lebanon d'in ya tafi, shi yasa kwana biyu ban ganshi ba ashe yaje d'auko ki ne,
ina ruwan sa ga yadda akayi zakije ki zaga cikin 'yan'uwa shi ne shi zai je ya rushe shirin, zai gamu da ni kuwa."
Feeryal ta zame a jikin Aunty tana gaida Daddy.
Aunty ta ce ta shiga ciki ta wasa ruwa ta rage gajiya.
Feeryal na shiga d'aki, Aunty ta dubi Daddy tana cewa
"Daddy dama fa ba'ayi shawari da shi wajen tafiyar nata ba, yakamata kuma aji ta bakin sa kafin tafiyar nan."
Daddy ya ce
"Dan ba'aji ta bakin sa ba, shi ne zai bita har wani kasa yaje ya d'auko ta, shekara 18 sukayi suna kewar ta da mahaifiyar ta,
shine bazai iya hakuri ya bar musu ita na wata d'aya kacal ba,
sabo da rashin hankali."
Aunty tayi murmushi tana cewa "Uhum Daddy ai gado ya yi, baka tab'a barina nayi sati a gida ba, tun da nazo gidan nan, in na jima nayi kwana uku, duk hidimar da ake kuwa."
Daddy ya yi karamar dariya yana fad'in
"Nashi gajen hakurin ai ya yi yawa, ya kamata ya barta tukun suma suma bukatar ta."
Aunty dai murmushi tayi dan tasan yana bukatar matarsa.
A waje suka had'u da Daddy yana kokarin wucewa side nashi.
Daddy ya dube sa yana cewa
"Ka kyauta da ka je ka dawo da ita."
yad'an sosa bayan keyar sa, yana gaida Daddy.
Daddy ya amsa yana wucewa.
A ranar da suka dawo da daddare karfe 8, Ajmaal ya shigo sashin Aunty suna zaune a parlour da Feeryal.
ya gaida Aunty Feeryal kuma ta gaishe shi, ya amsa yana yi mata murmushi sannan ya ce
"Aunty wai inji Ya Abdulrahim a bashi sudan tea."
Aunty ta ce
"Babu a kasa amma bari a girka."
tana mikewa kira na shigowa wayar Ajmaal ya d'aga ya kai kunnen sa sai yace
"To Daddy."
ya sauke wayar yana cewa
"Daddy na kira na bari na je na dawo kafin an gama."
ya juya da sauri ya fita.
Har Aunty ta gama Ajmaal bai dawo ba, sai can ya kirata a waya ya ce
"Aunty naje wa Daddy aika ne, dan Allah ki bawa wani ya kai masa."
Aunty ta ce "Tom bari a ba wani ya kai masa."
Aunty ta dubi Feeryal da ke zaune tana game a wayarta ta ce
"Feeryal je ki sa mayafin ki ki kaiwa Abdulrahim tea d'in nan."
ido ta waro ta ce
"Ammie akwai mage a hanya."
"Babu mage yana sashin Hajiya, har ki tafi ki dawo bazaki gansa ba."
ta mike ta shiga d'aki ta fito da hijabi a jikinta.
tana kwab'e fuska da tsoro ta ce "Ammie bazanga magen ba ko?."
Aunty ta ce "Bazaki ganshi ba Feeryal, ki sa a ranki bazaki gansa ba."
ta gyad'a kai ta karb'i flas d'in ta fita.
a can farfajiyar gidan ta had'u da Shamsuddin, ganin yadda take ta waige-waige ya ce
"Lafiya Feeryal ina zuwa da daddaren nan?."
ya kalli abun da ke rike a hannunta ya na kuma fad'in
"Ko zaki kaiwa Ya Abdulrahim ne."
da sauri ta gyad'a kai ta ce
"Eh kuma akwai mage a hanya."
ya yi murmushi ganin yadda tsoro ke d'awainiya da ita ya ce
"To kawo na kai masa."
ai ko ta mika masa da sauri ta juya ta koma.
tana shiga Aunty ta ce
"Wai har kin kai masa?."
marairaice fuska ta yi ta ce
"Ai naji kukan mage."
"Au da kikaji kukan mage sai kika aje tea d'in a ina."
"Na bawa Ya Shamsuddin ya kai masa."
tayi maganar tana kwanciya kan kujerar da Aunty ke kai tayi pillow da kafar ta..
Washegari da misalin karfe 7 na safe, Aunty na kitchen tana had'a breakfast.
kiran Abdulrahim ya shigo wayarta.
ta d'aga da sallama ya amsa sallamar tare da gaishe ta ya d'aura da fad'in
"Aunty ko zan sami sudan tea?."
ta ce "Eh bari a kawo maka."
fita tayi ta shiga d'akin Feeryal ta tashe ta a bacci, Feeryal ta tashe tana mussuke ido.
Aunty ta ce "Tashi ki kai masa breakfast zai tafi asibiti, yi sauri ki fito kafin na gama had'a masa."
Aunty ta fita ita kuma ta mike ta shige bathroom.
sai da tayi brush tayi wanka sannan ta fito.
ta zauna gaban mirror ta shafa mai da turare masu sanyin kamshi, sannan taje ta ciro pant da dogon riga normal riga mara nauyi, tasa pant d'in sannan ta zura rigar, batare da ta sa bra ba, ta d'au hijabi har kasa ta zura, ta fito kuwa dai-dai san da Aunty ta fito daga kitchen rike da basket data shirya masa breakfast ciki,
ta mika mata tana cewa
"Yanzu kam dai ba kule a hanya maza ki kai masa."
ta karb'a tayi waje.