← Book details Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 61

Sashe 49

Feeryal Part 3 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Duk abun da ake yi d'in nan Mom na sashin ta bata fito ba,
dan tuni Sahla ta kai mata rahoton abun da ke faruwa,
an kama Dad an tafi da shi kan zargin shi yasa 'yan kidnapping su kama Feeryal, kasa fitowa tayi dan kunya,
tana bakin cikin da basuyi nasara ba.

Feeryal ta waigo in da Daddy suke tsaye da Abbie yana binta da murmushi,
wan da cikin zuciyar sa d'acin abun da d'an uwan sa ya masa yake ji.
ta taka a hankali ta nufi in da suke,
Aunty ta bi ta da kallo ganin yadda take tafiya,
har ta isa in da suke cikin girmamawa ta gaishesu kanta a kasa.
suka amsa cikin sakin fuska sunai mata fatan Allah ya tsare na gaba.

Ko da ta dawo in da su Aunty suke Aunty ta ruko hannunta, a hankali take tafiya har suka isa side d'in su.
kai tsaye bedroom d'in Feeryal d'in Aunty ta jata ciki,
ta ce ta zauna bakin gado.
ta wuce bayi ta had'a mata ruwan zafi cikin bathtub ta fito ta dub'e ta ta ce
"Ta so muje."
ta ruko hannunta suka shige bayin, Aunty ta ce
"Tub'e ki shiga ruwan nan Feeryal kina tafi ba dai-dai ba."
Feeryal ta sunkuyar da kanta kunya kamar ta nitse kasa, shikenan Ammie'n ta gane abun da yayi ta mata.
rau-rau tayi da idanunta hawaye suka taru.
Aunty tayi murmushi ta ce
"To meye abun kuka Feeryal idan kika gasa jikin ki ke ma zaki fi jin dad'i."
hawayen da suka taru a idanunta suka zubo cikin rawar murya ta ce
"Na ce ya dawo da ni gida ya ki."
da sauri Aunty ta katse ta
"Balaifi yayi ba ai tun da shi ke da iko da ke, har yanzu shi d'in mijin ki ne yafi mu iko da ke."
Saurin kallon Aunty ta yi, Aunty ta gyad'a kai
"Kwarai kuwa dan bai sake ki ba, takardar da ya baki bata saki ba ce, gama ki fito na nuna miki."
ganin tana ta nonnukewa Aunty ta barta da bra da pant ta shiga ruwan.
tarika kara mata ruwan zafin yana ratsata sosai.

Bayan sun fito Aunty ta d'auko mata takardan tayi mamakin ganin da gaske ba sakin ya rubuta ba.
nan hankalin ta ya d'an kwanta dan gani take fyad'e yayi ta mata,
amma ta tura baki ita bata jin zata iya rayuwa da shi a yadda yake d'in nan zai iya kashe ta a bed.
ranar wuni Aunty tayi tana gasata.
kafin dare tafiyar ta ya yi normal, zafin ma yaragu sosai.
Miemie Ameerah Sumayya Bilkisu Rahma Saddiqa, duk suna tare da daddare har wajen 11 kafin kowa ya koma makwancinsa.

Washegari Aunty na zaune a parlour suna waya video call da babban yayan su Aliyu, wan da shine babban d'a ga Alhajin Abuja wato Alhaji Tahir Abbas, wan da ke da zama a kasar Lebanon.
yana yi mata jajen abun da yafaru da 'yar da take ruko.
Feeryal ce ta fito daga d'aki tana fad'in
"Ammie bani wayar nayi game."
Aunty ta ce
"Yauwa Feeryal zo ku gaisa da Uncle Aliyu, Yaya Aliyu gatanan ma ku gaisa, ai Allah ma ya takaita Abdulrahim ya yi kokari sosai wajen karb'o ta a hannunsu."
Feerayal ta zauna gefen Aunty tana kallon mutumin cikin wayar da bata tab'a ganin sa ba sai yau,
tana dai jin suna waya da Aunty lokaci zuwa lokaci.
Feeryal tayi masa murmushi tana fad'in
"Ina yini Uncle."
Uncle Aliyu ya mike zumbur yana kallon Feeryal tare da nuna ta da yatsa, bakin sa na motsi alamun magana yake son yi.
ganin yanayin da ya shiga Aunty tayi saurin cewa
"Yaya Aliyu lafiya me ya faru?."
komawa ya yi ya zauna tare da fad'in
"Am..am..ba... ba komai Fatima, lafiya lau ya abun da ya faru?."
Feeryal ta kuma murmushi idanunta akan mutumin.
Uncle Aliyu ya yi musu sallama ya kashe wayar.
yana kashewa Feeryal ta cab'e wayar ta yi d'aki.

Duk da abun da ya faru bai sa Daddy janye, batun auren Zaraddin da Saddiqa ba ya ce a cigaba da shiri aure ba fashi.
Mom kamar zata kashe kanta dan bakinciki, shirin da akayi dan ya wargaza auren duk da ya faru bai sa Daddy janyewa daga batun auren ba,
dan ya ce 'ya'yan Dad bazasu tab'a tashi akan 'ya'yan sa ba.

Ana gobe juma'a wato ranar da zata kasan ce ranar d'aurin auren Zaraddin da Saddiqa.
gidan ya cika makil da 'yan uwa musamman dangin su na Yelwan Shendam maza da mata, duk sun hallara.
da yammacin ranar ana ta shirya babban Hall d'in da ke can gefe karshen cikin gidan, dan biki ne na cikin gida.
Aunty ce ta d'auki nauyin shirya gaggarumin shagalin.

Feeryal na kwance kiran Miemie ya shigo wayan Aunty dake hannun ta.
ta d'aga jin muryar ta yasa Miemie cewa
"Yau wa Feeryal dama ke nake nima,
wai a gidan ma sai kin b'ata lokaci, to ga kayan ki kizo ki karb'a ki shirya ki yi sauri dai dan amaryar ma ta gama shiri, ga me make-up kiyi sauri ki zo."
"Kai Miemie bazaki kawo min ba."
"To bazakiyi kwalliyar ba ke nan ki dai zo ayi miki makeup d'in sai ki saka kayan anan."
"Tom shi ke nan."
ta kashe wayar tana mikewa, ta d'au d'an karamin gyale ta yafa shi a kafad'arta,
riga da sket na atamfa ne a jikin ta, d'inkin ya zauna sosai a jikinta.
ta nufi kofa ta fita.

Ango Zaraddin yana tare da abokasan a kofar side d'in su.
tun daga san da ta fito daga sashin Aunty duk suka juyo gareta.
itako kanta a kasa take takowa.
hon ya danna mata ta d'ago da sauri tana kokarin ketarewa d'aya gefen.
tun da ya dawo da ita yau kwana uku ke nan basu sake had'uwa ba, sai yau da ta gansa cikin mota.
alama yayi mata da hanu ta koma, ta kawar da kanta taci gaba da tafiyarta.
da sauri ya bud'e marfin motar ya fito ya damko hannunta ya yanyo ta ya bud'e motan ya turata ciki,
sannan shima ya zaga ya shiga.
da karfi ya fizgota yana fad'in
"Bakya ji ne nace ki koma! ko bakiga maza bane a gurin."
ya yi maganar cikin tsawa sosai
ido ta rumtse jin tsawan na shirin tarwasa mata kwakwalwa,
ta ce
"Ni ba in da suke zanje ba gurin Miemie zan je."
a fusace ya kuma fad'in
"Bazaki je ba kada na sake ganin kin fito, ko bakiji ba!?."
ya fad'a yana kuma yanyo ta ta had'u da jikin sa.
ya tallafo kanta da sauri ya had'e bakinsu yana tsotsa da zafi-zafi numfashin sa yana fita da sauri-sauri, dan ya fara shiga yana yin b'acin rai.
ya d'au mintuna 10 yana tsotsar bakinta zuwa lokacin yashiga sauke numfashi a hankali.
a sannu ya zare bakin sa yana tallafe da kanta, idanunsa akan fuskarta.
a hankali tayi kasa da idanunta tare da lumshe su,
ta sinkayo muryarsa a hankali can kasa.
"Kar na ganki a waje har a gama bikin nan."
da sauri ta d'ago idanunta ta kalle shi
kai ya gyad'a mata ya ce
"Haka na ce kar ki fito har sai an watse."
baki ta turo tana kwab'e fuska.
ya saki kanta ya bud'e ya fita yazaga d'aya gefen ya bud'e ya ruko hannunta,
har bakin shiga side d'in Aunty ya je rike da hannunta.
in da kallo ya dawo kansu, yana tsaye sai da yaga shi garta ciki kafin ya juya ya shiga motarsa, ya nufi side d'in sa.
ta shigo parlour tana tura baki.
ko da Aunty ta tanbaye ta dalilin fushin nata kamar zatayi kuka ta ce
"Ba Sahab ne ya ce wai na koma ba, kuma kar na fito har a gama bikin."
sai ga hawaye sharr.
Aunty tayi murmushi ta ce
"To meye abun kuka Feeryal tun da ya ce baya so sai ki hakura."

Ai ko haka aka gama bikin nan tass
Feeryal bata fito ba,
dan idan tayi yunkurin fita sai Aunty ta hanata.
amarya Saddiqa da angon ta Zaraddin suka tare a wani sashi na cikin gidan dake can gaba dana Abdulrahim.

bayan biki da kwana biyu,
da yama Aunty tana kitchen tana aiki, Feeryal na d'akin ta ya shigo daidai san da Aunty ta fito daga kitchen d'in.
ya karaso ciki yana gaisheta kan sa a kasa, Aunty ta amsa sannan ta ce masa tana ciki.
ta wuce bedroom d'in ta.
tana shiga yawu ce d'akin.
Feeryal na kwance a kan gado tana game a wayar Aunty dan ita yanzu bata da waya tun da 'yan kidnapping d'in nan suka karb'a,
dama waya bata dame ta ba shiyasa ma bata bi takan ta samu wani ba, dama game ne damuwar ta kuma ga wayar Aunty.
da sauri ta kalli kofa zaton ta Aunty ce, ganin shine ta kwab'e fuska ta turo lips d'in ta.
a hankali ya soma takowa idanunsa a kan ta.
ya na zuwa ya haye gadon ya janyo ta jikin sa.
baki ta kuma turowa tana kokarin zame jikinta.
ya dad'a riketa da kyau yana jefa idanunsa cikin nata,
ya tafi da hannunsa zuwa bayan ta sai ji tayi ya zuge zip d'in rigarta.
da sauri ta manna kirjin ta da nashi tare da kankame bayan rigarsa........!
Chapter 49 · 0% Book details