← Book details El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 80

Sashe 73

El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wallahi mama uwani ba ta gari bace, kinsan halin ta fa kinsan lokacin da take xuwa gidannan har ke da kanki kike min magana akan ta bata da nutsuwa da kamun kai, kuma kinji abinda tayi wa yar uwarta.

Duk nasani surayya, shiyasa nace kiyi addua mafi alkhairi nima xan tayaki, kuma abinda tayi wa yar uwarta a baya ba lallai bane ke ta maki shi karkiyi mamakin ta sauya daga yanda kika santa sai kuxo kuna xama na amana da ita.

'Surry ta share hawaye tana yatsine fuska, kowa yaqi ya duba mata duk wanda ta tunkara da maganar sai haquri yake bata, xata xubawa sarautar Allah ido ta kuma gwada yin haqurin tagani idan haqurin xai kaita ga riba.

Har su jiddah suka xo duk maganar da suke da mahaifiyarta tana ji komai bata ce ba har suka gama, da kyar tabi yusuf suka koma gida sai kuka take kamar ranta har wani haushinsa take ji.

Ya bata xabi akan gidan da take, sabo wanda ya gina ko kuwa wanda take ciki, kai tsaye tace sabo saboda tana ganin ai dan ita ya gina tun farko ba dan wata ba,

Yusuf sai godiya yake mata, burinsa yaga ta kwantar da hankalinta baya son damuwar ta ko kadan,

Ya canxa mata sabbin furniture ya saka a sabon gidan da xata tare, ko godiya ta kasa masa cos tana ganin yana yin komai ne duk don saboda xai qara aure har wani rawar kai yake a yanda take gani kenan.

Kayan fadar kishiya da ya qara tunkarar ta dasu cikin tsananin fushi tace bata so idan ya tilasta mata da karba xata qona su duka bata damu da abinda ya kashe ba.

Haka ya dauki kayan ya fita dasu jiki a sanyaye, ya nufi dakin sa dasu yasan watarana xata sauko har ta nemi kayan.

Suka tattara suka koma sabon gidansu, kana ya soma gyaran tsohon gidan.

Koda yaje mata da albishir ya biya masu hajji xasu je su biyu bata wani nuna murna ba saboda haushin sa da take ji, kuma shi kansa bai damu ba cikin murna ma yake sanar da ita anty ikram ta gayamasa ai harda jiddah da el'mustapha duk xasu je, da wannan mai aikin jiddah da tayi aure banan  duk xasu je, el'mustapha ya biyawa banan din.

Allah ya saka da alkhairi shine kawai abinda ta fada.

Baqin ciki xai ma uwani yawa, kowa xaije makka a barta, a shiga shirgi ba da ita ba🤪.

Bayan sati biyu akaje kai lefen uwani, ba laifi yusuf yayi qoqari sosai.

Tunda uwani taji labarin xaa kawo mata lefe taje tana fitar da tsofin kayanta tana rabawa yan unguwa, takalma da jaka duk bata bari ba, sai labari take badawa a unguwa sabbin kaya xaa kawo mata, ai auren ta na farko baqin ciki ake mata dashi shiyasa mijin ko atampha bai dinka mata ba, yanxu kuma Allah ya bata wanda baya mata baqin ciki mai son ta.

Duk abinnan da ake abba da hajiya basu da labari, akwatunan ta ma ko daya bata bari duk ta rabawa qawaye da masu aure wadanda basu da arxiki sai godia ake mata ana saka mata albarka tana washe haqora.

Wani abin mamaki uwani na bakin gate xaune tana jiran yan kawo lefe, ga yan uwa can acikin gida sun cika sai hidimar kayan tarbon lefen suke.

Tana ganin motoci sun tunkaro gidan ta tashi xumbur ta hangame masu gate tun kafin su kawo,

Qanwar abba ce ta fito ta ganta tsaye riqe da qofar gate ta jawo ta da qarfi tana mata fada,

Tace aa to miye abin fada anan gwaggo, na bude masu ne kada suyi batan kai suje sukai wani gida, idan ba baqin ciki ake min ba ai ba wanda ya fito waje ya tayani xama na jira xuwan su.

Gwaggo ta bige mata baki iya qarfinta, bata wasa sam da uwani, ta riqo hannunta duka biyu ta riqe tana neman abin dukan ta, uwani na ganin haka ido ya raina fata ta soma bata haquri tana roqonta, baxata qara ba ta yafe mata.

Gwaggo taja ta, ta saka ta a daki ta rufe ta, ta barta anan ciki tana fadin inga kin fito a dakin batare da an nemi ki ba.

Sanda suka shigo anyi masu tarba mai kyau kuma duk cikin su ba idon sani dangin yusuf ne kawai.

Har xasu tafi daya daga cikin su cikin wasa tace, bamu ga amaryar tamu ba da yake ba wanda ya santa a cikin mu, ko boyon ta kuke yi ne.

Gwaggo tace baxaku ganta a yanxu ba har sai ankai maku ita, xaku gaji da ganin ta k.... Gwaggo bata rufe baki ba, uwani dake cikin daki a rufe tana jin abinda ake fada ta kunno kai ta window tana fadin gani nice amarya Uwanitilyusuf jikanyar sarki merah.

Duk falon aka juya ana kallonta, ta kuwa xuba masu ido dan bata san su ba, nan fa suke mata kallon mamaki, anya wannan tana da kunya kuwa duk da take kyakkyawa sam bata birgesu ba.

Bayan tafiyar su gwaggo tayi mata duka sosai kuma ba wanda ya hanata saboda ransu yayi matuqar baci da abinda tayi.

Dukan bai bata mata rai ba ta dauki hakan a matsayin baqin ciki ake mata da kada dangin miji sun san ta, bayan ta gama kuka ta share hawayen ta matso ana kallon kayan da ita.

Wani dadi da farin ciki take ji idan ta tuna duk kayan nata ne, lallai ta yarda auren ta da el'mustapha ba alkhairi bane sai talauci da baqin ciki, ta xame jiki tayi dakin ta, tana jin wata nutsuwa na shigo mata, to ko dai yusuf yafi el'mustapha kudi ne, amma ta tuna sanda xai auri jiddah kayan da ya kawo mata ma sunfi wadannan, kenan baya son ta.

Ta dauki marker tabi dakin nata duka da xanen *Uwanitilyusuf* cikin heart, daga qarshe tayi wani rubutu da manyan haruffa wanda ke nuna har cikin xuciyarta she mean it iya gaskiyarta, *I LUV U EL'MUSTAPHA, STILL CAN'T FORGET YOU IN MY HEART*,  ta xauna gurin tana kuka sosai,

Bayan kwana biyu uwani ta soma saka kayanta na lefe tana fita, koda hajiya ta lura tayi mata magana anan take sanar da ita ai tuni ta kyautar da kayanta bata da na sakawa a yanxu sai sabbin.

Sosai abba ransa ya baci koda ya duba har akwai kayan da basu dade da dinkawa ba kuma masu tsada duk ta kyautar,

Tunda uwani taji abba na maganar xai maidata inda malami, hankalinta ya tashi taje da gudu ta cire kayan ta nufi dakin hajiya tana da wasu kaya acan ta saka ta fito tana kuka.

'Abba kayi haquri sharrin shaidan ne da sharrin xuciya, baxan qara ba, dan Allah ka yafe min abba kada ka kaini gurin sa kashe ni xaiyi.

Ganin abba da gaske yake ta soma kururuwa tana kuka iya qarfinta, yana riqo hannunta ya saka ta mota ta xube gurin a sume, bata manta waccan wahalar ba.

Ga bacin rai ga dariya sune suka saka abba a gaba, hajiya ta xuba mata ruwa a jiki.

Bayan wasu awanni suna xaune a dining suna cin abinci uwani ta dube sa tana fadin.

'Abba ina fa sane da cewa baka bani sadaki na ba, nasan ana baiwa mace sadakinta, ko anti jiddah ta bani nawa da el'mustapha ya bada.

Suka yi shiru suna kallonta, ta cigaba da fadin ai maigadi ne ya fada min daxu, ina so nayi jari da kudin na tallafi kaina da ya'yana masu xuwa.

Hajiya tace wane kudin xakiyi jari dashi, duka sadakin naki nawa ne?

Ina da wayo hajiya, baxaa min wayo a cinye min kudi ba, ko anti jiddah ma ta bani kuma na tuna sanda aka bata sadakin ta a hannunta kuka bata abunta.

Amma ai da aka bata maidawa tayi, hankalin ku ba daya ba.

Hajiya a bani nima nayi hankali ai, itama dan tana da kudi ne ta baku ni kuma kowa yasan talakace bani da kudi, abani a buna kada nayi wani laifi ace xaa hadani da Malam.

'Abba ya tashi ya fita bai jima da shiga dakin sa ba ya fito dauke da kudi a hannunsa, ya bawa hajiya yana fadin kirga min kiji nawa ne.

Hajiya ta qirga kudin tana fadin dubu hamsin ne, ya karba ya miqawa uwani yana fadin ga sadakin ki.

Ta karba tana murna harda godia, ta tashi ta dauki kudin dake hannunta duka ta hada ta fita tana fadin ni yanxu bana qaunar mota a rayuwata, ina da wadda el'mustapha ya bani xanje na dauko ta.

Ta jima sosai da fita sai gata ta dawo da wani mutum ya goyo ta akan babur.

Da gudu ta shiga cikin gida ta kira iyayen nata suxo suga ta siye sabon mashin vespa wanda ake yayi 🛵,

Ai abba ni xan riqa hawa abina duk inda xanje akan sa xanje, yanxu haka ana kan koya min tuqin sa, har masallaci idan xakaje ni xan riqa kaika ka huta da xuwa da qafafu tunda baka xuwa da mota.

Gobe da asuba ka tadani barci xan kaika masallaci, hajiya idan xakije maqota ki gayamin duk xan kaiki bana so kiyi ciwon qafafu ki tsufa da wuri, ai na gayamaku ni bana maku baqin ciki da na samu kamar kun samu ne, tayi cikin gida da gudu.

Halin da mahaifan nata suke ciki Allah kadai yasani, washe gari abba baiyi qasa a gwiwa ba ya sake daukarta ya nufi gurin wani malami da ita tsoronsa kada tayi aure tana wannan abin auren nata yaxo ya mutu ba kowane mutum xai iya xama da ita a hakan ba.

Malamin magani ya bata, dana turare dana sha suka dawo gida.

Cikin ikon Allah aka soma mata amfani da su.......

EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association
Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞

67

A gurguje....

Bikin uwani da yusuf sai matsowa yake yayin da iyayen ke iya bakin qoqarin su na ganin ta nutsu, kuma alhamdulillah abin yana ragewa kadan kadan.

Surayya tun tana damuwa tana kuka har ta daina ta xubawa sarautar Allah ido, tana so taga yanda xamanta xai kasance da uwani duk da ba gida daya bane.
Chapter 73 · 0% Book details