← Book details El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 80

Sashe 35

El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Arham ne xaune a gadon asibiti yana cin burger, dariya yake da alama yana cikin farin ciki el'mustapha yayi masa vedio ya kawo mata,

Mummy I miss you ya soma kissing wayar, itama kiss tayi Ma wayar tayi murmushi tana kallon el'mustapha,

Sai ki daina damuna da arham ki kwantar da hankalin ki tunda kin ganshi a raye,

70% of my damuwa ya ragu Mustyna sauran kuma na barwa xuciyata.

Meya hana sauran damuwar su wuce, ya tambayeta yana kallonta, yanxu mecece damuwarki, gaya min naji jiddah na.

Ka saki wannan matar ta fita daga gidan mu da rayuwar mu, I don't want to see her again.

Murmushi el'mustapha yayi yana matsa MacLean akan brush din ta,

Saboda me xan xauna da igiyar aurenta akaina bayan babu jiddah a tare dani, tuntuni na sauwaqe mata ina jin kece kika matsa da auren ta saboda ke nake xaune da ita kuma babu ke meyasa xan cigaba da xama da ita?

*NAYI NADAMA* El'mustapha, bansan yanda xan gayama baqin ciki da dana sanin dake xuciyata ba, amma ina roqon ka yafe min kuskuren danayi a baya da tilasta ma danayi akan sai ka aure ta, nayi ne saboda tausayin ta da kuma iyayen mu.

Ya ja kunnenta cikin xolaya gobe Ma sai ki roqeni na auri banan tunda kin xama sarkin tausayi.

Ta bata fuska tana kallonsa,

Kace Allah ka tuba el'mustapha, da ina da iko dana bige bakin da yayi wannan furucin a yanxu, nayi hankali a yanxu wanda ka saka a inuwa shi yake saka ka a rana, ko da ina da qanwa baxan barta ta auri mijina ba ballantana wata banan, ta turo baki cikin jin haushi meyasa Ma kake mgnr banan a yanxu?

Ya kawar da mgnr ta hanyar sunkuyowa, bakinsa ya turo yana fadin kina da iko jiddah ki bige bakin idan hakan xai sanyaya xuciyarki.

Ta kai bakinta dai dai nasa ta sumbata, ya xauna yana kallonta.

Gobe ma jiddah idan iyayenki basu baki goyon baya kiyi abu ba ki qara kinji xaki ga abinda rashin bin maganar su xai janyo maki, keda Ma ba haihuwarki sukayi ba kenan ina ga alhakin su dake kan uwani.

Uwani ta cuce ki babu wata cuta a tare da ita ta ciwon xuciya, she is pretending, jiddah ta fiddo idanu tana kallonsa,

Taya akayi ka sani.

Nima ban sani ba, dan sanda ne nifa jiddah kuma ba qaramin dan sanda ba, na saba yin bincike Kala Kala kuma ina nasara, ban taba xuwa asibiti na bincika halin da take ciki ba ko kuma tambaya amma dan na gwada ta nace mata naje asibitin na bincika a gurin likitan da ta hada kai, wallahi ban sani ba I just say it, daga yanayinta da amsar da ta bada nagano hasashena gaskiya ne amma baxan gaya maki ba har sai kin gano da kanki kuma kika kasa.

Jiddah tayi shiru ta dubesa, uwani ta cuceni, dubi qafana el'mustapha, uwani har take cewa a kashe arham a gabana, a kuma kasheni, ta dauki kudin ka dasu ta biya kudin aikin mu, tsohuwar dake kula dani saboda sunji xata taimakeni suka kashe ta a gabana, kasan yanda nayi rayuwa tare da su kuwa, kasan yanda nake kwana na yini tare dasu, kasan irin abinda suke bani naci wai a matsayin abinci batare da sun duba abinda ke ciki na ba, babu tausayawa ko jinkai a tare dasu sai wani mutum daya suna kiransa goga,

El'mustapha ya rufe mata baki da tafin hannunsa yana kallon yanda take xubar da hawaye, haka yake ji kamar shima ya tayata kukan saboda tausayinta,

Ba sai kin gayamin ba jiddana, nagani da idanuna daga yanda kika dawo kamanin ki suna neman sauyawa, uwani Ma xatayi xaman prison ta dandana abinda kika ji.

Ta soma share hawayenta, ya tashi yana fadin bari na kira wata nurse ta cire drip dinnan jiddana tayi wanka tacire wannan dattin dake jikinta.

Tayi dariya tana fadin, kada kace kaji warin dattin ni bana son sharri,

Wari kam jiddana baa magana idan na cigaba da jinsa tabbas xaa bani gado a asibitin nan,

Ta janyo cup dake kusa da ita ta jefeshi a bayansa ya fice yana dariya, itama dariyar take.

Wayar sa dake ajiye a gefenta ta soma qara, idanu ta tsura tana kallon mai kira, number ce akai ba suna, bata da niyar dauka saboda bata taba masa haka ba, har wayar ta tsinke bata dauka ba,

Da wata nurse ya shigo   tana bayansa, bama musulma bace ta cire drip din, bayan ta fita ya dauki jiddah sai toilet.

Yana ajiye ta ya dawo ya dauki brush din ta da sauran tarkacen da xaiyi amfani dasu.

Shi da kansa yayi mata wanka, ya wanke kanta sosai, tayi brush, aka wanke dattin daya jima a jiki lungu da saqo, ta fito fes amma still hasken fatar ta ya dan dushe bai dawo ba, ya matsa yana kallonta cikin murmushi.

Jiddah ta fara dawowa jiddatulmusty amma da saura.

Ta watsa masa ruwa dake hannunta tana murmushi, ya dauke ta ya maidota qarfin hali kawai yake amma xuciya da ruhi babu abinda suke buqata a wannan lokacin kamar jiddah tun sanda ya dora idanunsa akan abubuwan da yayi missing a tare da ita.

'Nikam Mijin Jiddah doctors basu duba qafana bane har yanxu fa inaji bana iya tafiya da ita...... yaji muryar jiddah a hankali tana magana cikin duba qafar tana taba ta,

Shiru yayi yana kallonta cikin tausayawa bai san yanda xai gayamata ba, ta dago tana kallonsa a raunane cikin seriousness,

Baka gaya masu harda qafana yana ciwo bane,  dr ya gayamin sun gyara xaman baby na amma bai min mgnr qafana ba, kuma nasan rarrafen da nake yi ne ya birkita min xaman baby.

Da kyar el'mustapha ya xauna kusa da ita, ya soma qoqarin shafa mata mai a bayanta yana fadin,

Sun san da maganar inaji results dinne har yanxu bai fito ba.

Ta sauke numfashi a hankali tana murmushi, ta gefen ido el'mustapha ke kallonta cikin tausayawa.

Pherty........ ✍🏻

EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association
Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞

41

Ya janyo qaramar jakar da ya saka kayanta ciki yana dubawa,

Doguwar riga ya ciro ya ajiye gabanta yana fadin,

Oh Allah jiddana nayi mantuwa,

Me ka manta dashi,

Ya dago yana kallonta sirri ne kada fans na pherty suji,

Ya miqa mata wata bra yana fadin xaki iya sakawa or I should help,

Ta yatsina fuska bayan ta karba tana dubawa,

'Wannan ta dade da min kadan fa tun sanda na sami ciki, yanxu bata min.

Ya karbi bra din yana duba kafin ya dubi kirjinta yana kallonta,

Yanxu wannan ce baxata miki ba, tau yanxu ya kike son tunda ita kadai na dauko, kuma kinsan baxaki xauna haka ba ana shigowa kowa yana kallonki.

Ta dauki doguwar rigar ta xura tana fadin ba wanda xai sani idan nasa hijab, anjima sai kaxo min da wasu.

Banan bata san su bane ya tambaya yana kallonta,

Banan bata sani ba cos batasan me nake sawa ba, kai xaka dauko min not banan.

Ya janyo wayar sa yana fadin fadamin size din idan anty yusrah ko ikram xasu xo sai su biya su siyo maki.

Ta gaya masa bayan ta saka hijab din ta,

Ya dube ta a raunane bayan ya ajiye jakar,

Ki cire hijab din jiddah, I need you....

Ta dan dube sa a raunane kafin tace kayi haquri kada mutane su shigo su same mu, kuma ynxu baka tausayina?

Mutane sun fini ne jiddah, banyi qoqari ba?

Ya tsare ta da sexy eyes din sa masu kassarata, ba shiri ta sunkuyar da kanta qasa, dan bata iya jure kallon idanuwansa masu rikirkita kowace lafiyayyar d'iya mace balle ita matar shi ta sunna, data fi kowa sanin sirrinsa na xahiri da badini baya boye sha'awarsa a gareta indai yana buqata.

A raunane tace, ba wanda ya fimin el'mustapha a duniyar nan, ba wanda nake so da qauna kamar shi, meyasa kayi min wannan fahimtar.

Yace sai wace kike so nayi maki jiddana,

Understandable irin wacce ka saba yimin a ko yaushe.

Yayi murmushi batare da yayi magana ba, nutsuwar jiddah da haibarta na birgeshi, magana take cikin nutsuwa kamar ba daga bakinta take yi ba, dauke da matsananciyar qaunarsa a kwayar idanuwanta, sonta da qaunarta na kwarara a xuciyarsa ya rasa inda xai saka ta,

Ya tallabe kansa da hannuwansa duka biyu ya xuba mata idanuwansa yana kallonta cikin so da qauna,

Duk yanda kike so haka xaa yi, idan an hanani abin abarni nayi ta kallon jiddah ko xn sami nutsuwa a xuciyata.

Murmushi tayi tana Jan dogon hancinsa, ta kai bakinta dai dai kumatunsa ta sumbata,

Kayi haquri mijin jiddah ni ban isa na hanaka ba is just.... ya katse ta🤫,

Kwanta ki huta, kafin tayi magana ya tashi ya gyara mata pillow, da kanshi ya gyara mata kwanciya ya matsa gefe nesa da ita kadan yana fadin,

Kiyi barci jiddah kina buqatar hutu kafin yan dubiya su xo, I will be with you kada ki damu.

Ta lumshe idanuwanta a hankali ta bude tana kallonsa, ya maida hankalinsa kacokan akan wayarsa.

Ta tuna soyayya da kulawarsa agareta, ta tuna qoqari da kulawar hajiya da abba a gareta.

Bayan wadannan mutanen babu wani a xuciyarta kamar su.

Tana tuna yan uwanta tun tana qarama hajiya ta dauke ta takaita gurinsu domin xumunci kuma tasan yan uwanta, amma suka qi karbarta suka soma yiwa hajiya habaici wai ta maida ta ne saboda ta cinye dukiya babu komai a hannunta hakan ba qaramin batawa hajiya rai yayi ba tun daga lokacin bata qara kaita ba kuma suma din basu waiwaye ta ba.

Kuma abin mamaki duk yan uwanta bafa talaka gwargwado kowa nada arxikinsa iya rufin asiri amma an rasa wanda xai riqe ta saboda babu iyayenta a duniya, ta ya xata iya bijirewa wadannan mutanen da suka nuna mata so da kauna a duniya, suka maida ta mutum kamar kowa, suka aurad da ita ga mutumin kirki wanda ya dace da rayuwarta, baya gudunta ko kyamarta akowane hali ya tsinceta a ciki.

Ya dago a hankali yana kallonta,

Yace barci nake kiyi jiddah, me kike tunani ne.
Chapter 35 · 0% Book details