← Book details El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 80

Sashe 29

El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Banan dauke da arham a jikinta, bai da lafiya sosai xaxxabi ke damunsa, dawowar su daga asibiti kenan tare da el'mustapha.

Kallonta yayi cikin tausayawa yanda take bata lokacinta gurin kula da yaran ta xama kamar jiddah a gurin su abinda uwani ce ya kamata tayi, kuma iyayensu ba yanda basu so karban yaran ba el'mustapha ya hana yafi so yaransa suna hannun sa.

Allah xai saka maki banan, bani da bakin da xan gode maki amma Allah kadai yasan abinda ke xuciyata game da kulawarki ga yarana, sai kuma yayi shiru yana sharar kwallah.

Ki gayamin abinda kike so daga gare ni insha Allah xan maki shi ko menene.

Banan ta dago tana kallonsa, tausayinsa ya qara mamaye xuciyarta, yanda el'mustapha ya dawo abin tausayi ne ga duk wanda ya sanshi a baya,

Taji ina ma xata kasance dashi da ta dawo masa farin cikin da ya rasa a baya, da ta maye masa gurbin jiddah, amma Sam baxata iya hakan ba ta riga ta sanarwa jiddah ta amince da Islam kuma koda ace jiddah bata raye tabbas sai ta cika mata burinta na auren Islam domin yanxu sun soma dai dai tuwa.

Ba komai ina yine saboda Allah da qaunar mahaifiyarsu, dawainiyar da kukayi dani tun ina yarinya ya isa nima na dauki dawaniyar yaran ku.

Allah ya saka maki da alheri, ki qara kulamin dasu ki masu duk abinda suke so kuma ki kare min su kada ki bari suma a cutar min da su.

Ya tashi ya fice daga gidan, arham ya soma amai sosai ta ajiye shi ta fice da sauri da xumar ta dauko abinda xata gyara wurin.

Sai ga uwani ta shigo gidan tana huci, ba xato ta taka amai ta dubi arham din batare da tunanin komai ba ta dauke fuskarsa da Mari dai dai lokacin banan ta shigo dauke da tsumma da Cup na ruwa a hannunta.

Banan ta saki Cup din da tsumma ta sha gaban uwani dake qoqarin shigewa dakin ta, arham sai kuka yake yana kiran mummy.

Me yayi maki kika dake sa Uwani?

Kallon ta take da mamaki,

Yau kuma Uwani xaki kirani babu anti lallai yarinyar nan saboda na daki yarana kike tambayata ko wadda ta haifesu bata isa tamin wannan isar akan su ba.

Uwani me arham yayi maki kika mare sa, shi nake tambayar ki,

Uwani taja da baya ganin ganin banan din na shigowa cikin ta kamar xata dake ta,

Saboda xai yi amai anan tsakiyar falo naxo na taka, kuma ke me ya hana tuntuni kixo ki kwashe.

Oh saboda kin taka aman sa kika mare sa, yaron da ko lfy baida, to idan aman ya taba jikin ki kuma ya xakiyi.

Uwani tace kamar ya tana kallonta, banan ta riqo hannunta uwani ta soma kiciniyar kwacewa sai suka soma dambe a falon, arham ya rude musamman da yaga ankai uwani qasa, ta soma kururuwa tana kiran mutanen gidan taimako.

Banan ta cusa kallabinta a bakin uwani ta rufe yanda kowa baxai ji ba,

Yau duk uban da xaki kira yaxo ai na dake ki dama ina ciki dake, ina ganin take taken ki akan yarannan ba kya tausayin su, kinsha duka na ina kyaleki yau duk xan fashe, ki kira qaumi ko hajja duk basu isa su hana na dake ki ba,

Batare da tunanin komai ba ta goga fuskar uwani a cikin amai, yanxu sai ki mutu ko kuma idan kin tashi kada kibarshi da rayuwarsa....

Kai kai kai me nake gani haka cewar el'mustapha bayan ya nufi inda suke da sauri, ya dauke banan daga jikin uwani sai huci take kamar Serdia  a filin dambe.

Uwani ta tashi tana cire kallabin bakin ta ta nufi banan da niyar kai mata duka el'mustapha ya hana,

Me ya faru ne,

Saboda arham yayi amai ta taka shine ta mare sa bayan ta san kuma bai da lafiya, yanxu da na sa mata aman a fuska nake son ganin matakin da xata dauka akaina ko akansa.

El'mustapha ya dauki arham dake kuka yana kallon fuskarsa, ya kalli uwani yanda tayi wani xuru alamar ta daku a gurin banan, ga aman duk ya bata jikinta.

Murmushi yayi har a ransa yaji dadi, Sam ya lura banan bata da haquri kamar jiddah,

Xo ki gyara falon banan, kije kiyi wanka ki huta ni xan kula da shi kinji, sannu da qoqari Allah yayi maki albarka.

Ya dubi arham,
Is ok yaro na no need to cry again, baka ga anty banan ta rama maka dukan ba ai ko ba komai mutum yasha aman ka You have to be proud of it, kuma ba wanda ya isa ya taba ka, idan kuma mutum ya qara gigin taba min kai ko aryan xai sha mamaki kuwa, ya fice.

Wanka yayi wa yaron, ya bashi magani bayan ya sha tea, ya kwantar dashi inda aryan ke barci tun daxu bai san wainar da ake toyawa ba.

Dakin uwani ya nufa lokacin ta fito wanka daga toilet kenan tana tunanin qila sai ta hada banan da kurma, itace matsalarta a yanxu.

Kallonta el'mustapha yayi qasa da sama,

Kudin da kika dauka dakina naxo kibani abuna?

Gabanta ya fadi, kamar ta saki kashi a gurin yanda cikinta ya murda,

Tace ni ban dauki kudin ka ba, ni da baa xuwa dakin ka.

Ki gayamin gsky me kika yi da kudin da kika dauka a dakina, just tell me uwani, tun da nake xaune da jiddah bata taba min sata ba, cikin wannan bangare babu mai shigowa acikin maaikatan gidannan sai banan kuma nasan baxata dauki kudi na dan bata taba xuwa ko falona ba ballantana daki na, ina kika kai kudin.

Jikinta ya dauki rawa ta fara rantse rantse tana hawaye ita bata dauka ba an mata sharri ne dan ko aljannunta basu sata.

'Naji shikenan baki dauka ba, kuma duk wanda ya dauka asirin sa na gab da tonuwa har da mai sa hannu a batan jiddah very soon xan gane.

Kije na sake ki saki daya saki biyu, dan babu kyau yin uku ne da nayi maki mai gaba daya, na aure kine saboda jiddah babu jiddah a tare dani babu amfanin xamana tare da ke, ba kyason yara na ban son ki, kuma baxaki bar gidannan ba xaki xauna ne har sai ranar dana ga jiddah, har yanxu ke nake xargi kuma ina bincike akan ki, ya juya ya fice yana so yaje yayi tracing layin jiddah agani waye ya kirata urgent, abinda ya kamata yayi tuntuni amma saboda tashin hankali da damuwa baiyi wannan tunanin ba.

Pherty... ✍🏻

EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association
Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞

37

Ya fito harabar gidan yana kallon securities,

Kada kubari uwani ta fita a gidannan, idan kuka yi wannan saken a yau wlhy ran ku xai yi matuqar baci fiye da kuskuren da kuka yi a farko.

Ya isa ga motar sa dai dai lokacin da wayar sa ta dauki qara, yana dubawa anty ikram ya gani, yayar sa.

Ya dauki wayar bayan ya kara a kunnensa,

'autan mama, kaxo asibiti jikin mama yayi tsanani sai sunan ka take kira.

Ya tsinke wayar batare da yayi magana ba, da sauri ya shiga motar ya bar gidan abinda ya mantar dashi xuwa mtn office kenan🤦🏻‍♀.

Uwani tun daxu tsaye take, ta kasa xama ta kasa gasgasta abinda kunnuwanta suke jiye mata, el'mustapha yayi mata saki biyu, aa bata yarda ba kunnuwanta basu jiye mata da kyau ba.

Jikinta ya dauki rawa, lokaci daya xaxxabi mai xafin gaske ya taso ya rufe ta, jikinta yayi xafi rau, da kyar ta isa bakin gado ta xauna, sai ga hawaye sharrr na bin kumatunta.

Ji take duniyar ta mata xafi, duniyar Ma gabaki daya juya mata take, wani duhu ya mamaye idanunta, duk wani motsi ko sauti bata jinsa a kunnuwanta, sai ta gigice ta fashe da kuka mai tsananin gaske kukan da bata taba irin sa ba,

Ta rasa el'mustapha har abada, ta rasa wannan abin da take matuqar so da qauna, ta rasa wannan abin da take gani tana gab da samuwar sa, ta rasa wannan abin da ta wulaqanta yar uwarta saboda shi, ta rasa wannan mutumin mai matuqar tsada da muhimmanci a rayuwarta, el'mustapha yayi mata nisan da har abada baxata taba samun sa ba, ba ita kadai ba har jiddah ta gama samun sa, idan ta rasa shi shima xai rasa jiddah, jiddah Ma xata rasa shi, kowa ya rasa, indai tana numfashi a doron qasa el'mustapha da jiddah baxasu taba kasancewa tare ba.

Idanunta suka yi jawur saboda kuka,  da kyar ta janyo wayarta ta soma neman layin jamcy, kusan sau biyar tana kiran layin baya shiga, ta tashi da kyar ta xura doguwar riga, qaramin mayafi ta dora akan ta, key din motar ta kawai ta dauka ta fito da kyar tana layi saboda axababben ciwo da kanta keyi.

Horn tayi alamar a bude mata gate din, amma aka qi, tayi magana suka gayamata abinda el'mustapha yace, bata damu ba saboda yanda take jin jikinta, tana komawa dakin ta ta fadi ragwaf, xaxxabi mai xafin gaske ya rufe ta.

El'mustapha kuwa yana isa asibitin kai tsaye ICU ya nufa,

Gaba ki daya mama ta fita hayyacinta ba abinda ke fitowa bakinta sai el'mustapha, hannunta ya hada da nashi bayan ya tsugunna a qasan gadon da take kwance.

Magana take yi a hankali da kyar yake iya jiyo abinda take fada, da alama wasiya take bashi musamman akan yayyunsa da yan uwansa, ya rumtse idanunsa sai ga hawaye na xuba, jikinsa ya dauki rawa lokacin da yaji tana kalmar shahada, kafin wani lokaci numfashin ta ya ajiye.

Ya bude idanunsa sosai yana kallonta, no he can't believe it, mama ta mutu yanxu a hannunsa, ya soma jijjigata a hankali yana kiran sunan ta.

Da kyar nurses suka fitar dashi dakin,

Idan el'mustapha dake namiji yayi kuka akan mutuwar mama, mu da muke mata mu ce me? Cewar anty ikram tana kallonsa bayan ta riqo hannunsa.

'Anty yusrah tace ba kuka xamuyi mata ba addua ce, kukan mu baxai amfanar da ita da komai ba, kuma ta roqa ko bayan ranta kada muyi mata kukan mutuwa.
Chapter 29 · 0% Book details