← Book details El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 80

Sashe 45

El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Nima dai ban sani ba, abu ne acikin Leda, ya dan dube ta anty yusrah ta aiko kayan nata kuwa.

Tun daxu, suna falon ka,

Ya xauna daf da ita yana fadin, na kusa angwancewa jiddah, ki haihu na huta haka, nayi ta haquri, ko babu lafiyar qafafun I can manage amma Allah yasan abinda ke xuciya ta I need you.

Taja kunnensa tana murmushi, ban san yaushe el'mustapha ya dawo haka ba, idan munje sati nawa xamuyi ne?

Ana maganar watanni kina maganar sati, Allah ya bamu nasara a wannan aikin naki jiddah.

Amin ta bashi amsa, tace ka dauke ni pic da wayarka el'mustapha, xan riqa tuna wannan wheel chair din a duk lokacin dana kalla, baxan taba mantawa da ita ba.

Ya dauki wayar yana ta daukar ta, wani suyi tare wani tayi ita kadai.



*

'Washe gari jirginsu ya daga xuwa Germany,

Satin su biyu acan, an dora ta akan drugs kafin a tashi mata tiyata, sosai dr merah ke kula da ita, tun kallon farko da yayi wa qafar ya gano matsalarta.

Amma bai masu bayanin komai ba kuma ko el'mustapha ya tambayesa akwai wata matsala sai dai ya daga masa hannu, abinda ke damun el'mustapha kenan da dr merah shi kam ya rasa gane qarfin mulkin wannan mutumin ya fiye ji da sarauta kamar a gidansu aka farata.

An saka date din da xaa Ma jiddah aiki, tun da el'mustapha ya kira Nigeria ya sanar da yan uwa banda addua ba abinda suke.

Wani abin mamaki, haihuwar taxo dai dai da ranar da xaa yi mata aikin, tun wayewar garin ta tashi da naquda gadan gadan.

Tun tana cijewa kada el'mustapha ya gano sai da ya gane,

Da kansa yaje ya kira dr merah, halin da suka same ta kuwa gwani ban tausayi.

Batayi wata doguwar naquda ba ta haifo santaleliyar d'iyar ta, jawur da ita kamar jiddah, sai dai gabaki daya yarinyar kamannin twins ta dauko illah dai tafisu hasken fata ne.

Suna tsaye tare da jaririyar suna kallo aka fito da jiddah xaa shiga aikin da ita,

El'mustapha ya miqawa banan jaririyar da sauri ya nufi jiddah, haka Ma banan tabi bayansu da sauri tare da hajiya,

Me na haifa el'mustapha?

Mace ce jiddah kyakkyawa kamar twins, ya fada yana murmushin qarfin hali yana shafa kanta.

Ta juya tana kallon hajiya da kyar ta iya cewa nagode hajiya...

Sai kuma ta dubi banan dake dauke da jaririyar.

Nasan xan fito lafiya insha Allah na same ku, amma duk da haka ki kulamin da ita banan, ki kula da su twins ciki kuwa harda *EL'MUSTAPHA*, cikin kuka banan tace,

Anti jiddah El'mustapha yayi babba da na kula dashi, ke kadai xaki iya kula da shi, ke kadai xaki iya bashi farin ciki irin wanda kike so ya dauwama aciki, dan Allah kidaina wannan maganar xaki tashi lfy.

El'mustapha ya sunkuwa ya sumbace ta jikinsa na rawa, yasa hannu yana share mata hawaye,

Xafin ciwo ba mutuwa bane jiddah, jikina har ynxu bai bani xakije ki barni ba xamu rayu tare har abada mu kula da ya'yan mu, you will get well soon Jiddatulmusty and El'mustapha is for only you jiddana, bana buqatar kulawar kowa sai naki, ya janyo hannunta ya hada qaramin yatsansa da nata,

Yace mun qulla, idan har akayi nasara akan aikin aka fito dake lfy I promise you kome kike so a duniyar nan xan maki shi indai baifi qarfina ba,

Tayi murmushi tana qara riqe mararta dake ciwo,

Idan kuma na mutu fa,

Baxama ki mutu ba jiddah stop saying dat rubbish ya bata ransa sosai, ta shafi fuskarsa tana murmushi,

Sorry Musty na, pray the best for me, xan dawo na cigaba da rayuwa da kai ina matuqar son ka.

Yace yauwa jiddatulmusty, ya sunkuyawa dai dai kunnenta yana rada mata addu'o'i da xatayi,

Tayi murmushi tana nanata addu'ar da ya gayamata a xuciya cikin hope din xata rayu tare dasu.

Haka aka jata aka shiga da ita, banda addua babu abinda suke.

GET WELL SOON JIDDATULMUSTY ❤

'Hajiya dan Allah kiyi haquri ki maidani titin da kika dauko ni ko ki bude min wannan gate naki na fita da qafafuna,

Hajiya Mariya ta tsaida cin Apple da take tana kallon uwani a wulaqance,

Tace kin gama gyara kitchen dinne,

Uwani tace da ban gama ba xaki ganni nan ne, har toilet din da kika ce na wanke, duk dakunan gidannan na gyara, ni nagaji dake nagaji da ganinki ki barni nayi tafiyata.

Kallonta take batare da mamaki ba xaman da sukayi da uwani ta fahimci yarinyar bata da tsoro gurin maida magana sai kaje dukanta ta soma baka haquri amma bakin baxai yi shiru ba ta rasa wace irin yarinyace wannan,

Tace kije tsakar gidannan shima duk sai kin share sa'anan ki dawo.

Uwani ta gyara tsayuwarta, hannayenta akan qugunta kerere take kallonta,

Nifa bamai aikin ki bace, ban taba yiwa kowa bauta ba sai ke, kibarni nayi tafiyata, na rasa me kike nufi dani, baki gaji da ganina bane.

Tana ganin Mariya ta tashi ta fita da gudu da tsintsiya a hannunta, ta daga murya tana fadin,

Kin sato nine kiyi kudi dani, nafi qarfin ki ko wanda xai yankani kisha jinina na kalleshi sai ya girgixa, tun da naxo gidannan ban taba ganin kowa yaxo ba sai kace mayya, ku.... Tayi shiru sakamakon ganin hajiyar ta fito da wata xungureriyar bulala, ba shiri uwani ta sunkuya tana shara,

Tace me kike cewa uwani, maimaitamin banji da kyau ba,

A sanyaye uwani ke kallonta,

Hajiya tunda baki ji mgnr ba abarta kawai ta wuce ta sunkuya da sauri tana sharar.

Dogon tsaki hajiya taja ta juya,

'Na daukowa kaina jaraba wannan shegiya ni ta isheni a gidannan, sai na gama axabtar dake xan fiddaki.

Uwani ta nufi gate din bayan ta ajiye tsintsiya, ta soma kiciniyar bude gate din amma ta kasa kusan kullum sai ta gwada yin hakan, ta leqa ta gate din tana fadin,

Wayyo a taimakeni, akwai wani a kusa ne, wata mata ce ta sato ni, a taimakeni.

Shiru bataji alamar motsin kowa ba,

Ta tsugunna tana leqe ta qasan gate yanda xata ga mai wucewa da kyau,

Kicibis idanunta na sauka akan wani qatoton kare baqi wulik sai fiddo harshe yake, taja da baya da sauri hade da dafe qirjinta saboda yanda yake bugawa, yanda taga Karen yana huci kamar xai cinyeta, aikuwa da ya tona mata asiri idan ya rabata da duniyar saboda baqin ciki ne xai mata.

Ta tashi ta cigaba da shara, tana gamawa ta shiga gidan,

Mariya.... Mariya take kiran hajiya🤔

'Na gama kixo ki sallameni idan ba haka ba wlhy sai in qona gidannan, nifa banda mutunci baki sanni bane sai na nuna maki, tun muna mu biyu kixo ki fiddani cikin wannan gidan naki mai wari da qaxanta, ashema dadin komai baa ci, ya'yan ki ma cikin wahala suke, tuni na gano kina daya daga cikin mutanen dake min baqin ciki da jin dadin duniya shiyasa kika kawo ni gidannan, to baxan xauna ba, hajiyata nake so ehe, itace ke sona bata min baqin ciki tana tausayina.

Tayi shiru tana saurare, bata ji an amsa ba kuma babu alamar motsi a gidan, ta lallaba a hankali ta isa dakin hajiya Mariya.

Ta xare idanu lokacin da ta tsinkayota kwance ta ware qafafunta tana tura wannan abun tsakanin cinyoyinta.

Jikin uwani ya dauki rawa ta juya da sauri tana maida numfashi.

Ita kam nata taba ganin musiba irin wannan ba, kaico da wannan rayuwa ta matar nan, ta xauna ta buga tagumi tana hawaye.

Wai ni meke faruwa dani ne, me nakeyi xaune a cikin wannan gidan da wannan matar, yaushe xan barshi naje ga iyayena, ina so na roqesu gafara, nayi aure na da el'mustapha na xauna gidan mijina cikin jin dadi, tasan yanda jiddah take da haquri xata barta ta auri mijinta tunda tana sonta kuma jiddah bata mata baqin ciki da jin dadi.

Allah na tuba kuskuren da nayi a baya, inda ban tada hankalina ba da yanxu ina can ina cin samosa, ina cin kayan dadi, ina sa masu aiki sumin aiki, amma yanxu nice ma mai aikin, kai jamcy ta cuce ni, surry tana sona, dama hajiya da abba sunce duk na cutar da jiddah Allah baxai barni ba, gashi kuwa, na shiga uku ni uwani Allah ka yafe min, ta soma kuka.

Bayan minti ashirin ta qara tashi suduf suduf taje qofar dakin tana leqen hajiya Mariya.

Tana gani tana kallon wani abu a waya tana shafa jikinta,

Uwani ta rumtse idonta, ta qara budewa dai dai lokacin matar ta sauko daga saman gado, tana kallo ta fito da wasu kaya da alama su xata saka kafin ta nufi toilet tana waqa da wani yare da ta kasa fahimtar ko wane iri ne.

Kayan da ta ajiye akan gado tabi da ido tana kallo, sadaf sadaf ta shiga dakin ta daga rigar tana kallo doguwar rigace mai kyau.

Wani tunani uwani tayi ta ajiye ta fita da sauri tana fadin,

Matar nan idan ban nuna mata koni wacece ba baxata barni na fita ba,

Bata jima ba ta dawo dauke da scissor a hannunta, daga rigar tayi ta soma yankata a tsaye tana mata tsaga ta ko ina yanda rigar baxata moru ba,

Tana gamawa ta ninke yanda ta ganta ta ajiye ta fita da sauri tana numfashi.

Binni binni take dubawa tagani ko ta fito, tana tsaye gurin taga fitowar ta xindir kuwa, ta bude bakinta bayan ta dora hannunta akan bakinta,

Shegiya yar iska, tambadadiya, tana gani ta bude wani qoqo ta laqato wani abu a dan yatsanta ta ware cinyoyinta tana shafawa.

Uwani ta saka a xuciyarta sai taga ko menene, ta koma ta xauna bayan minti talatin ta qara dawowa har lokacin bata shirya ba amma ta saka pant da bra, tana kallon sanda ta janyo rigar xata saka sai da gaban uwani ya fadi.

Cike da mamaki take kallon rigar, ta soma tunani,

Uwani.... Uwani ta soma kiranta da qarfi,

Saboda tsananin tsoro da firgici Sam uwani ta manta Ma a bakin qofar take tsaye, sai ta soma amsawa da qarfi,

Hajiya Mariya ta juyo cikin mamaki tana kallon qofar,
Chapter 45 · 0% Book details