← Book details El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 72 OF 80

Sashe 72

El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ku nawa ne acikin ta, su waye ku? Malamin ya tambaya cikin xare ido yana kallonta.

Uwani bata gane abinda yake magana akai ba, ga bayanta sai radadin ciwo yake,

Ganin taqi magana malamin ya qara kai mata wata bulalar, a gigice ta nemi hanyar ficewa, almajirai suka yi cikinta suka riqo ta,

Wayyo abba, wayyo hajiya xasu kashe ni, wallahi baxan qara ba, ko magana xan daina yi, dan Allah kayi haquri.

Malamin yace ku musulmai ne,

Da sauri uwani ta gyada kai, sau biyar nake sallah kullum, kuma ina xuwa islamiya ka tambayi abbana.

Malamin ya gyara hannun rigarsa yana fadin har yanxu jinnun basu tako ba, suna so su nuna min taurin kai, ni kuma xan wahalar da ku, kuna so ku batawa yarinya rayuwa.

Yasa wani almajirinsa ya riqa hannayen uwani ta baya aka banqare ta, aka daure qafafunta da igiya, ya riqe tsakiyar kanta ya daga murya sosai yana karanto mata qur'ani,

Ya jima yana yi sosai ya qara kallonta, su waye ku?

Uwani tayi wiqi wiqi da ido, hawaye da majina duk sun hade a fuska saboda tsananin axaba,

Tace wallahi nice uwani, sunana Aisha, ni jikanyar sarki ce, bani da aljannu, dan Allah kuyi haquri.

Daga inda abba yake xaune yana jin muryarta, tausayin yar sa ya mamaye xuciyarsa, Allah ya bawa uwani lfy, ya tashi a hankali ya nufi inda suke.

Ganin yanda aka banqare uwani hankalinsa ya tashi sosai ya shigo dakin da sauri,

Malam menene haka, meyasa kake dukan ta da wanna bulalar.

Uwani na ganin sa ta taso a wahalce ta rungumesa sosai.

'Abba karkaje ka barni kashe ni xasuyi, ni bani da aljannu, abba baxan qara ba na tuba, ka gayamasu baxan sake ba.

Ya dubi bayanta duk shatin bulala ne gurin yayi ja sosai abinka da farar fata,

Yace na kawo tane ka duba min ita idan akwai amma bance ka dake ta haka ba, mutum ce ba dabba ba, baa taba mata duka irin wannan ba.

Yace amma alhaji m.... Abba ya katse sa,

Shikenan ai ka riga ka aiwatar, yaja hannun uwani suka fita sai kuka take jikinta na rawa, da kansa ya bude mata motar ta shiga kafin ya shiga ya tayar.

Cikin kuka tace abba ina da hankali baxan qara ba, kada ka qara kaini wani gun a dake ni, ni bansan ina yin komai ba.

Abba ya tausaya mata yace ba inda xan qara kaiki uwani, xan haqura dake haka na cigaba da xama dake, inaji haka Allah ya tsaro maki taki rayuwar amma duk da haka uwani ki rage wasu abubuwa a kullum ina gayamaki hakan kuma xan cigaba da maki addua kinji.

Ta gyada kai da sauri tana fadin abba kada ka qara kaini a dakeni, baxan qara ba, na daina yin magana.

Yace idan kika qara ma nan xan dawo dake malamin nan ya qara dukan ki, kinga Malam guzuma ya huta da dukan ki.

Ta fashe da kuka har tana riqo hannunsa dake kan sitiyari, abba wallahi baxan qara ba kayi haquri.

Kafin su iso gida har tayi barcin wahala sai ajiyar xuciya take.

*

Cikin kwana biyu aka xagaya da jiddah taga dangi haka dangi sun ganta,

Daga baya suka dawo gida tare da kuyangu da sarki ya bata guda uku,

d'aya sunanta Xuwaira, sai Nafee Anka sai ta qarshen Lailah, masu hankali da nutsuwa.

Jiddah ta qara samun matsayi a xuciyar el'mustapha sai nan nan yake da ita cikin nuna mata wutar soyayyarta dake adabar xuciyarsa.

Jiddana mai iyaye da yawa, jiddana jinin sarauta ya fada lokacin da yake qoqarin xama a kusa da ita.

Iyayen nan xan raba su biyu na bawa el'mustapha rabi, iyayena ai iyayen ka ne.

Kefa yar gata ce jiddah, ni yanxu nafiki xama abin tausayi.

Ba uwa ba uba, ni maraya ne jiddah ki kula da ni da yarana shine farin cikin rayuwa ta.

Ta rungume sa tana fadin komai runtsi komai wuya, komai dadi a duniyar nan baxan manta da musty na da ya'yana ba, sune jibin rayuwata, farin cikina, ina matuqar son su baxan iya rayuwa batare da su ba, el'mustapha ya kwantar da hankalinsa, jiddah tashi ce kuma har yanxu da baxar sa take taka rawa.

Ya kwantar da ita a hankali hade da hada bakinsu guri d'aya.

*

Yusuf kayan menene haka, akwati nake gani kusan shidda kamar kayan aure.

Yace eh surry xo ki xauna muyi magana ta fahimta, akwai naki kaya akwati kusan uku hannun anty ikram na fadar kishiya.

Fadar kishiya ta fada cikin firgici tana kallonsa yayin da xuciyarta ta tsananta bugawa tamkar xata fado daga qirjinta.

owa ta soma kiran jakadiya, bata jima ba kuwa ta xo da sauri tana fadin,

Ranki ya dade gani,

Tace akwai wata yarinya dake kwance a falon nan ki sa a fitar da ita a falon yanxu.

An gama gimbiya yanxu nan xaa aiwatar.
EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association
Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞

66

Aure xaka yi yusuf? Wacece xaka aura, ina so na santa dan Allah ka gayamin.

Ya riqo hannunta yana qoqarin xaunar da ita, ta fisge da qarfi tana kallonsa,

Tambayar ka nake, just answer me, bana son dadin bakin ka wacece xaka aura, who is she yusuf, ta fada hade da riqo gaban rigarsa tana kallonsa idanunta taf da hawaye.

Am sorry surry, uwani ce, amma wallahi u.... Shut up ta katse sa cikin tsawa, idanunta sun juye sunyi jawur.

Uwani kuma yusuf, ashe baka barta ba, menayi ma, what did I do to deserve this? Menene bana yi ma, dame na gaxaka da shi a gidannan na kyautatawar aure, me uwani ta fini dashi,

Wallahi babu komai surayya babu abinda uwani ta fiki da shi sai hauka, haka kawai nake son na aure ta badan kin gaza ni da komai.

Idan aure xaka qara meyasa dole sai uwani, mata nawa ne a gari, kasan bata da hankali kake neman hadani xama da ita, You are not serious, nagane me kake nufi a yanxu, xaka auri uwani ku xauna ku wulaqantani saboda tun farko ba nice kake so ba, na amince na aure ka saboda tausayin abinda uwani tayi maka a baya, na xauna da kai da xuciya d'aya, na koyawa kaina soyayyar ka amma yanxu kake son nuna min halin ku na maxa, tabbas na yarda namiji ba dan goyo bane, kaje gaka ga uwani, ta juya a fusacce.

Hankalinsa ya tashi yabi bayanta yana bata haquri sam abinda take tunani bashi bane a xuciyar sa, idan har surry xata barshi tabbas xai haqura da auren uwani sadakin da ya bada ma xai yafe.

Kayanta ta soma hadawa tana kuka, duk rarrashi da ban baki da yake bata bai sa ta saurare sa ba, ko  ta kan yar'ta Mimi bata bi ta soma qoqarin fita daga dakin, ya riqota da qarfi suka soma kokawa a dakin, qarfi ba daya ba dole ta saduda ta fashe da kuka.

Tsura mata idanu yayi yana kallonta, idan yace baya son surry yayi qarya, macece da kowane namiji xaiyi alfahari samun irin ta, tun daga kan nutsuwarta haqurin ta da biyayyarta, kuma ya sani duk duniya ba macen da xai so kamarta har uwani kuwa domin son da yake mata baima uwani shi ba kuma yasani ko a mafarki uwani baxata masa biyayyar da surayya ke masa ba.

Idan bai manta ba shi uwani xatayiwa laifi amma shi xaije yana bata haquri, idan kuma shi yayi laifin duk shi xaije yana bata haquri, bai taba sanin dadin rarrashin mace ba sai akan surry da ta soma yi masa, baya manta har ganin uwani yake a mafarki ta tsare sa da fada yana bata haquri, to me akayi?

Ya dafe kansa da hannuwansa duka biyu tabbas idan auren uwani matsala ne a rayuwarsa da matarsa ya haqura dashi.

Yayi juyin duniya da surry ta kula shi taqi, yana fita massalaci ta dauki yar'ta da kayanta ta fice daga gidan.

Sanda ya dawo ya sami batanan kuma babu kayanta da ta diba daxu hankalinsa ya tashi sosai, kai tsaye gidan jiddah ya nufa, kallo daya tayi masa ta gane baya cikin nutsuwa.

Meke damun yusuf?ta tambaya lokacin da take qoqarin sakawa airah pampers.

Surayya ta guje ni anty jiddah, bansan ya xanyi ba, she left my house.

Saboda me?

Saboda aure na da uwani, ya xanyi?

Tace ka haqura da auren uwani, dole ne?

Yace aa, amma ita ma ina son ta, kuma kinga iyaye sun shigo maganar me xance dasu.

Kace masu ka fasa, ina maka sha'awar xama da surayya fiye da xama da uwani, banga laifin surry dan ta guji uwani ba saboda tasan abin da tamin, babu mai son kishi da uwani kai tsaye xata ga bayansa.

Yace hakane nasani wallahi, uwani tausayi take bani anty jiddah, bayan wannan ma bafa a gida daya xasu xauna ba, kowacce da gidan ta kuma na baiwa surayya xabi akan duk gidan da take so acan xata xauna, auren nan fa ba haramun bane ya halatta, hudu akace muyi ko.

Tace hakane amma baa ce kuyi hudun haka kawai ba, sai aka qara da cewa idan xaku iya adalci tsakanin su.

Insha Allah, Allah baxai kamani da laifin rashin adalci a tsakanin su ba, ki taimakeni anty jiddah nasan ke kadai ce mai sauqin kai da xata duba min anty ikram bata son auren nan ko kadan kinsani, ki shige min gaba muje mu rarrashi surry wlhy ina son ta.

Jiddah ta kira el'mustapha ta sanar da shi xata fita da dalilin fitar, yayi mata ixini kafin su tafi ita da yusuf.

Surayya sai kuka take a gaban mahaifiyarta tana gayamata komai da kuma halin uwani.

Addua xakiyi, abinda yafi xama alkhairi Allah ya tabbatar amma kada ki daga hankalinki dana mijinki ki sakawa xuciyarki damuwa surayya, maganar yusuf ya sake ki bana son ji kuma kada ki kuskura ki furta masa wannan kalmar.

Kiyi haquri dama aure ya gadi hakan, xama na tare dole sai ana haquri duk yanda kake da mijinka baxaka taba cewa baxai maka kishiya ba, wata Ma sai ta tsufa a gidanta da yaranta mijin xai auro mata yarinya sharkaf warin yar cikinta, illah kawai kayi addua Allah ya hada ka da ta gari.
Chapter 72 · 0% Book details