← Book details El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 80

Sashe 23

El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Oh no wonder ashe kece kika nuna masa kada ya soni ya kulani saboda naqi naje na nemi gafarar iyayena, ki gayamin xagin su nayi, dukan su nayi kome, saboda me xasuyi fushi dani?

Allah ya baki haquri uwani ni ban isa na aibataki a gurin mijinki ba sai ma qoqarin na gyaraki naga kun dai dai ta.

Ki gyarani yanda kike nufi yanxu a lalace nake, ok kece xaki gayamasa ya soni, gaskiya ni wannan rayuwar ta isheni anci amanata ashe da gangan aka amince na aure shi a cutar dani ba dan tausayi na ba, nikuma yau Aisha sai na fada auren mijin hajiya mijin tace, da anyi magana yace wani jiddah wai jiddansa bako kunya harda wani jiddatulmusty, to wlhy nima na xama Uwanitilmusty a gidan nan ai nima matar shi.

Murmushi kawai jiddah tayi, ita kam yanxu uwani tsoro take bata ta daina bata mamaki, sai kace ba tare suka taso ba amma yanxu uwani rashin mutunci ba wanda batayi mata.

Yanxu dai baxa kixo muje ba,

Eh baxan je ba, inkinje ina gaidasu idan kuma baa so a maidamin gaisuwata ba dole, ina tashi xanje da kaina, idan na biki ko anyi niyar yafemin aka ganki sai a fasa gwanda naje ni kadai kuma kada a qullamin wani munafurci kuma.

Jiddah ta fice tana dariya, kallon mahaukaciya take Ma uwani a ynxu Sam bata mata kallon masu hankali.

A gurguje😏

5 Months....

Lokacin cikin jiddah yana cikin wata bakwai, sai yanxu yake fitowa, haka halittar ta take jikinta baya nuna girman ciki.

Duk abin nan da ake a gidan uwani bata taba sanin jiddah nada ciki ba, tuntuni el'mustapha ya bata jari ta fara business irin wanda jiddah keyi before, duk inda tasan jiddah na kai kaya can take kaiwa ana siye jiddah bata taba kula taba,

Ynxu bata el'mustapha take ba, ba ruwanta dashi ta kudin ta take, sai sufi kwana biyar Ma bata saka jiddah a idanuwanta, tun da safe xata bar gidan tunda an bata mota itama xataje gidan qawayenta baxata dawo gidan ba sai lokacin dawowar el'mustapha kada yaxo gidan batanan ne dalilin daya sa take dawowa.

Babu ruwanta da kowa a gidan, ta xama hajiya ita kadai ke rayuwarta el'mustapha ne kawai tun da safe aje a gaidashi idan ya dawo aiki aje a gaidashi shima dan ana son sane wai da ko ganinta baxai yi ba.

A lokacin saura wata uku auren su ya qare dashi kuma tana sane ita kadai tasan abinda take saqawa a xuciyarta tare da jamcy.

Ranar da taga cikin jiddah sosai hankalinta ya tashi ta kasa boye mamakinta.

Anti jiddah cikine dake, yaushe ma kikayi cikin?

Jiddah ma kallonta take da mamaki?

Inayi ciki sai na gayamaki nayi ciki ne, ko xan fito in fadawa duniya mijina ya kwanta dani yayi min ciki.

Oh oh ai ba abin fada bane Allah ya baki haquri, dama masu ciki sun fiye xafin rai, tasa kai ta fice.

Hankalinta yayi matuqar tashi ta kira jamcy ta gayamata harda kukanta tana sharce majina.

Ya akayi ke bakiyi cikin ba, kinsa wasa ba kince bakida lokacinsa ba ai kuwa xaki gani tana haifa masa yara yana mutuwa ta tashi da dukiya ke kuma zero.

Ki gayamin ya xanyi,

Ke nifa nabi saurayina xamuje America ko mahaifiyata bata sani ba kinsan xatamin baqin ciki ta hanani xuwa ni kuma ban taba xuwa can ba baxan haqura  ba, kibari idan na dawo xaa san yanda xaa yi.

'Ashe bani kadai iyaye kema baqin ciki ba harda ke,

Kedai bari kawai sai na dawo ta tsinke wayar.

Uwani ta kasa haqura ranar da kyar taga tayi barci tunda sassafe ta nufi a asibiti a gwada ta idan bata da ciki.

Anyi test ba komai, negative, banda abin uwani inma akwai shi wata biyar ai xaa sani.

Da kukanta take kallon likitan,

Wlhy sau biyu yayi min kace bani da ciki, amma ita gashi nata cikin ya fito, so kake na xama bora a cikin gida, dan Allah laifin me nayima kaima kake baqin ciki dani.

Abin ya daure masa kai, mamaki bayyane a fuskarsa,

Yace abinda babu xan maki qaryar akwai ne, ko sau dubu kikayi ba biyu ba kuwa, ina ruwana da ko sau nawa aka maki ne.

To yanxu likita ba yanda xaayi kasamin cikin ne ya fito, ance komai likitoci sunayi, dan Allah ka taimakeni ko nawa ne xan biya nidai kasamin cikin yanxu in ganshi da girma ya fito, ka taimakeni likita kada kamin baqin ciki.

Pherty......... ✍🏻

EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association
Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞

32

Sororo yayi yana kallonta,

In sama ki ciki ni Allah ne?

Ba haka nake nufi ba Doctor, meyasa kuke sanin mutum yana da ciki, meyasa kuke duba idan mace ne ko namiji a cikin mace, meyasa kuke sanin idan yana motsi ko bayayi, meyasa kuke fitar da yaro daga ciki matacce ko raye, indai xaku san wannan ai xaku san yanda xaku sawa mutum ciki, ni ko nawa ne xan biya naxo da kudina a jaka.

Ke tashi ki barmin office, ina tunanin baki da hankali, something is wrong with your brain.

Allah yasa ba kai kadai bane likita a garin, kuma kaine baka da hankali,

Ya tashi a fusacce yayo kanta tana ganin haka ta fice da gudu tana xaginsa.

Tana fitowa harabar asibitin ta hadu da yusuf da surry, har surry xata mata magana yusuf ya hana yaja hannunta suka bar gurin.

Ita ba wannan ne gabanta ba, cikin da tagani jikin surry ya kara tada hankalinta, jiddah da surry duk ciki ne dasu xasu haihu su barta, yusuf din Ma kamar bai san ta ba shege mayen mata maciyi amana, ka aure min qawata ban yafe ba Allah xai saka min, gashi har tayi ciki.

Cikin motarta ta xauna tana kallon masu shige da fice a asibitin, duk mai ciki ta wurga xata bita da kallo kamar mayya, ita mamaki take yadda akayi su sukayi cikin ita batayi ba tunda har sau biyu yayi mata, to ko sai anyi sau uku ne ta fada tana kallon wata mai ciki da ta fito asibitin, ko xata tambayi matar ne ta gayamata sau nawa aka mata ta sami cikin.

Duk ma laifina ne dana daina kulasa na daina sa masa pills ko ranar girkina, xanyi amfani da wannan dama ta yau in saka masa duk abinda xaa yi ayi nima ya min ciki in huta da gori da yan baqin ciki dan sai na sami dukiyar nima.

Da wannan tunanin uwani ta isa gida.

Tana shiga falon ta taradda jiddah xaune a falon, banan xaune a qasa tana tausa mata qafafu twins suna wasa tsakiyar falon.

Cikin jiddah kawai take kallo har ta shigewarta daki, xama tayi tana neman mafita, jiddah bata isa ta haifi cikin nan a gidannan ba, nasan me xanyi.

Da dare ita da banan sun gama girki saboda ita ke tayata dan bata iya komai ba,

Sun jera komai a dinning, ta duba ba kowa a falon tsit da sauri ta nufi dakinta ta dauko pills tana xuwa ba tunanin komai ta xuba acikin juice din el'mustapha,

Naganki cewar banan tana shigowa falon dauke da kaskon turare a hannunta.

Wata irin faduwar gaba ta same ta lokaci daya, ta juya tana kallon banan.

Me kika gani?

'Na ganki kina sa abu a juice din yaya,

To ba dai magani bane dan ni bana bin bokaye.

Baxan gane haka ba cewar banan, bayan ta ajiye kaskon ta qaraso inda uwani ke tsaye tana kallonta,

Uwani ta dube ta rai a bace, wai ke wane hurumine dake a gidannan bayan xaman ki mai aiki, ki kiyayeni fa ina ruwanki da abinda nakeyi, ah ah kujimin yarinya da rainin wayo.

Tau shikenan naji tunda ni mai aikice xan tsaya matsayina, dama kafin a daukeni aiki a gidannan an min gargadin karna cutar da kowa a gidan kuma kada na bari a cutar, dan haka xan gayawa anti jiddah cewa na ganki kina sa wani abu a juice din yaya.

Uwani ta rude ta soma rawar jiki, ta riqo hannun banan, ke meyasa kike min haka ne, kixo mu hada kai muji dadi a gidannan, ni xan maidaki ma yar riqo na ba yar aiki ba.

Ai kinji matsalar ni xuciyata bata da dogon buri da kwadayi irin naki, uwar dakina uwar rainona bata koyamin haka ba, bata saka min kwadayin duniya da cutar da wani ba, ta koyamin yanda xan xauna da mutane da xuciya daya koda kuwa mutum yana bibiyata da sharri ne, ta koyamin yanda xanyi mu'amala da mutanen kirki, bata gina min xuciya da sharri ko cin amana ba, ta riqeni da xuciya daya baxan bari a cutar da ita ko wani nata ba, xuciyata bata manta alheri komai qanqantarsa, ta sakamin da alheri na saka mata da sharri Sam wannan baxai yiwu ba, mafita daya ce xan rufa maki asiri amma da sharadin sai kin shanye wannan juice din dakike ikirarin ba magani kika xuba akai ba.

Ke wlhy baki isa ba, kinyi kadan, baxan sha ba, ke wacece da har xaki sakani yin abu, who d hell focus are you, stupid kawai😂

Damn you Banan ta fada tana kallonta dai dai lokacin el'mustapha ya shigo, dawowarsa daga masallaci kenan,

Kallon uwani yayi kafin ya maida kallonsa ga banan dai dai lokacin ta juyo tana kallonsa a karo na uku😊

Da kyar ya bude bakinsa yana kiran jiddah a hankali kamar bayason magana.

Jiddah ta fito tana kallon mutanen dake falon.

Yaushe mai aikin naki tayi matsayin da xata tsaya da matar gida suna sa'in sa, am not siding uwani amma ina son sanin dalili ko ba komai uwani ta girmeta kuma gidan auren tane.

Jiddah ta dubi uwani kafin ta maida kallon ta ga banan, jikinta yayi sanyi ita kam bata son tashin hankali a rayuwarta.

Kullum ina gayamiki banan kima uwani biyayya, matar mai gidance a qarqashin ta kike meyasa ba kya jine.

Anti jiddah nagayamaki baxan iyama anti uwani biyayya ba, baxan daina sa'in sa da ita ba,  nafiso akanta na bar aiki a gidannan.

Meyasa banan, kina so kijawo min matsala ne bansan yaushe kika fara taurin kai ba.
Chapter 23 · 0% Book details