← Book details El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 80

Sashe 33

El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna gurin ibrahim yaxo ya sanardasu halin da uwani take ciki duk cikin su ba wanda ya kula har ibrahim ya gama magiyar sa ya fice.

El'mustapha kuwa drugs din daya sha harda na barci a ciki, yana xuwa gida wanka kawai yayi ya soma barci,

Banan kuwa tana son jin yanda jikin jiddah yake amma bata sami fuskar tambaya ba.

El'mustapha bai je asibitin ba sai bayan isha'i yana fitowa masallaci can ya nufa direct.

Ya gaida su hajiya yana fadin ya jiddah?

Sai ga hawaye na bin kuncin hajiya,

Tace har yanxu bamu san halin da take ciki ba, likitoci kawai ke shiga suna fitowa tun daxu.

Jikinsa yayi sanyi, hankalinsa ya qara tashi ya dubi anti ikram da kyar yayi magana.

Sister kixo kije gida,

Itama jikinta a sanyaye yake ta tashi tayiwa su hajiya sallama ta fice, el'mustapha na bayanta har gurin motarta, ta riqo hannunsa tana kallonsa.

Insha Allah jiddah xata sami sauqi, she will be on her legs, bana so ka saka damuwa a xuciyarka.

Ya bude mata motar batare da yayi magana ba, ta shiga tana fadin ihsan ta kira daxu baka nan, gobe xata shigo taje kaduna daxu ne, idan jiddah ta farfado let me know please.

Ya rufe motar yana fadin insha Allah, ki shafa min kan affan,

Ta tada motar tana murmushi kawai, yana tsaye gurin har ta fice kafin ya juya cikin asibitin,

Driver yana jiran ku hajiya, kuje gida dare yana yi.

Baxaa yi haka ba cewar abba, idan muka je gida sai a barka kai kadai a asibiti da majinyata har biyu.

Ba komai bane abba, nurses Ma suna kula da patient da kyau anan, damuwar yanxu jiddah bata farfado ba amma ba wani abu bane.

Kai da baka da lfy kaine xaka koma gida el'mustapha, mu kuma xamu tsaya mu kula dasu,

El'mustapha yace aa, idan haka ne abba kai xaka koma gida sai mu tsaya tare da hajiya amma ni baxan iya barin asibitin nan naje na kwanta batare da nasan halin da jiddah take ciki ba, ko naje banda nutsuwa ba barcin xanyi ba.

Da kansa ya raka abba har mota, ya dawo yana amsa call, mutane sai kiran sa ake ana masa barka da ganin matarsa.

Likitoci biyar ne kan jiddah, tunda aka kawo ta suka duba yaron cikin ta baya xaune dai dai wannan dalilin ne ya saka tuntuni suke aikin ganin sun maida yaron dai dai shiyasa basu sanar da yan uwanta ba kada hankalinsu ya tashi.

Cikin nasara kuwa suka yi aikin, sai dai rashin farfadowar jiddah ne abin tambaya?

Suna kan duba qafar jiddah sun kasa gano matsalar illah kumburin da kawai suke gani, duk da ba sun gama binciken ba suna cikin yin sane, Dr. Bakori shine babba a cikinsu, yayi matuqar tausayawa halin da jiddah da abinda ke cikin ta, duk kansu suna buqatar kulawa.

El'mustapha haka ya dawo kamar wanda bashi da lafiya a jiki, ya jingina da bango wanda ya taimaka masa wajen daukar nauyin gangar jikinsa,  rungume da hannayensa a qirji.

Likitoci kam sun tsananta bincike akan qafar jiddah da dalilin rashin farfadowar ta har xuwa wannan lokacin.

Ya koma bakin barandar asibitin cikin tsananin sanyi ya xauna, jikinsa sai rawar d'ari yake amma bai damu ba, babu abinda yake sai addua,

Ya ciro wayarsa daga aljihunsa yayi switching dinta saboda mutanen dake damunsa da kira, baya son damuwa.

El'mustapha wata likita tana neman ka, yaji muryar hajiya a bayansa.

Xumbur ya tashi yana maida glass din sa a aljihunsa, bai saurari hajiyar ba yayi cikin asibiti da sauri tana bayansa.

Itace ta nuna masa likitar Dr Fulani Gafai,

Tace kaine Mahaifin Arham El'mustapha, ya gyada kansa da sauri xuciyarsa na bugawa.

Tace tun daxu yaron ya farfado yana neman maman sa, kaje ka duba sa.

El'mustapha yaja wani numfashi yana jin wani sanyi a xuciyarsa ya juya xuwa dakin da aka kwantar dashi, tare da hajiya suka shiga dakin.

Arham ya juyo yana kallonsa,

Daddy anty uwani tace driver ya rufe ni a mota, taje dani inda mummy shine naji wani abu a hannu so painful,

El'mustapha ya xauna a gadon, ya dora hannunsa a goshin arham kafin ya sumbace sa a goshi,

Kada ka sake maganar uwani, try to forget her..... Arham ya katse sa,

I saw mummy, tears rolling from her eyes, daddy take me to her.

Hannun ka baya ciwo ne el'mustapha ya tambayesa yana kallon hannun.

Akwai ciwo aryan ne yaji min ciwo,

Aa kada kayiwa aryan sharri, yana can yana neman ka a gida.

Daddy yayi kuka?

Yayi kuka sosai yana neman arham, anti banan ta Goya shi.

Daddy nima xata goyani? El'mustapha ya gyada kansa ya juya yana kallon hajiya.

Kayan da anty ikram ta kawo daxu naga harda kayan tea aciki, ko xaa hada masa ne.

Hajiya taje tana duba kayan, el'mustapha ya dora kansa jikin arham, kansa ke masa ciwo sosai.

Daddy kana da nauyi.... Yaji muryar arham, ya dube sa yana murmushi,

Kai kuma gaka raggo, ya tashi daga jikinsa, hajiya da kanta ta bashi tea din, ta juya tana kallon el'mustapha,

Ko a xuba maka abinci ne kaima baka ci komai ba fa,

Aa hajiya bani tea din nasha saboda maganina da nake so nasha yanxu bana iya cin wani abu mai nauyi.

Ta hada masa ta bashi,

Yana gamawa ya tashi xai fice, arham ya kirasa,

Daddy ka kaini inda mummy, I know where she is, inda wasu masu bindiga irin naka.

Kayi barci mummy tana gida, very soon xata xo ta ganka, make sure you takes your drugs from hajiya idan ta baka kuma banda rigima, xata kula da kai kafin nadawo.

Arham yayi shiru yana kallonsa, shikam jiddah yake son gani.

El'mustapha ya dawo yana kallonsa, me kake so na kawo ma yanxu,

Daddy bring Aryan,

Tau shikenan xan kawo maka aryan gobe in kayi alqawari  baxakayi wa hajiya fitina ba irin na anti banan.

I promise daddy, kaxo dashi da mummy.

'Yauwa good boy xan xo maka dasu, apart from them me kake so na siyo ma.

Bana son komai hannuna yana ciwo ne,

Xai daina ciwo ne, bari na kira likita ta qara duba ka, ya dubi hajiya.

Kema kina buqatar kici abinci hajiya, arham ne sai kinyi haquri da rigimarsa as usual.

Murmushi kawai tayi, el'mustapha ya juya ya fice.

Ya isa dai dai lokacin da aa fito da jiddah har lokacin bata farfado ba, ICU aka nufa da ita yana daga bayansu.

Yayi shiru yana kallon agogon hannunsa, sha biyu ta gota na dare.

Allah ka farfado da jiddah lafia cewar el'mustapha bayan yaja numfashi yana furxar da iska a bakinsa.

Pherty.... ✍🏻

EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association
Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞

_dis page 4 u bestyna Ummi Aysher_❤

40

'Washe garin ranar da sassafe ibrahim ya shiga asibitin,

Yana xuwa kai tsaye dakin da aka kwantar da uwani ya nufa, ta farfado tana xaune tana shan tea abinta hankalinta a kwance ba wata damuwa a tare da ita.

Shine ya taimaketa amma bata jin xata iya gaidashi illa idanu da ta xuba mashi,

An tashi lafia, ya jikin uwani.

Ta tabe baki tana yatsina fuska,

Ina so na tambayeka jiddah tana da rai kuwa?

Baiyi mamakin tambayar ba idan da sabo ya saba da wannan tambayar a duk lokacin da ya xiyarci uwani, yana tuna shine ya dauki nauyin kula da ita maganin ta da komai na asibitin duk cikin aljihunsa ne amma yarinyar ko godiya baxata iya masa ba hassalima kallon kirki baya samu daga gareta ballantana yayi darajar da xaa gaidashi, ita bata da damuwa sai ta jiddah.

Bata san cewa albarkacin jiddah da iyayenta ya saka ya taimaketa ba da kasancewar ta musulma.

Dama hausawa na fadin duk inda musulmi yake dan uwan musulmi ne kuma xuciyarshi tasha banbam da ta Arne ko ya take, dama Allah ya halicci musulmi dan xumunci da qauna ga dan uwansa musulmi,

Koda basu hada jini ko yan uwanta ka ba, ko da kuwa haduwar hanyace, amma uwani ta kasa gane darajan mutanen da taci.

Ya dubeta fuskarsa a daure, naxo na duba jikin kine xuwa gobe xaa wuce dake a rufe ki kamar yanda el'mustapha ya bada umarni.

Ta fiddo idanuwanta tana kallonsa cikin tsoro,

Ni xaa rufe? Me nayi, jiddah ce kuma ya ganta saboda me xaa rufe ni, laifin me nayi, saboda mugunta da cin amana ana baqin cikin ganina a raye ake son kulle ni a hana min walwala da jin dadin rayuwata.

Ke har kina da bakin da xaki kira wani mugu ne, akwai wanda ya kaiki mugunta a duniya ne, ki shiga taitayinki uwani kisan me kike, wlhy idan baki roqi gafarar jiddah da iyayenki ba alhakin su baxai bar ki ba.

To naji ban warware ba, kuma baxan warware ba dan har yanxu ina jin xaxxabi.

Ya fiddo mata ankwa ya nuna mata kin ganta anan tuntuni ya bada ita kuma ya rantse sai ya rufe ki gobe ko dani ko ba dani ba, naso na taimakeki amma nagane ke wawiya ce bakida hankali gwanda ya rufe ki din ya axabtar dake kamar yanda kika sa aka axabtar da jiddah, wannan qafar taki Ma naso ta lalace ta rube acire a yarda kowa Ma ya huta da baqin halinki.

Uwani ta fusata tace idan remote din duniya a hannunka yake ka maidoshi baya ka barni inda ka ganni ba sai ka taimakeni ba, waya sani Ma ko sona kake shiyasa ka nace min kai baxaka yi xuciya ka barni ba, baka ganin kowa ya gujeni ba mai xuwa inda nake harda wadanda suka kawoni duniyar saboda suna min baqin cikin rayuwa ta, nidai baxan soka ba mata biyu ne dakai baxan je a ta uku ba, el'mustapha nake so kuma sai na mallakesa.

Murmushi yayi mai cike da takaici,
Chapter 33 · 0% Book details