← Book details El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 80

Sashe 57

El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'Abba ya tambaya dalili, batare da tunanin komai ba tana yarfe hannuwanta tace uwani na fasawa kai an nufi asibiti da ita.

'Abba baice komai ba ya juya cikin gida ko baa fada ba yasan duk akan el'mustapha ne daga yanayin da yaga ya fita.

Yinin ranar sai taji ta damu el'mustapha bai kirata ba kuma ta kira yaqi ya dauka,

Tana ganin sanda aka dawo da uwani asibiti an daure mata kai da bandage 🤕 amma dan qarfin hali irin na uwani sai cewa take sai dai na dawo dakina ko kashe ni xaa yi kuwa.

Jiddah ta kasa sukuni, ga kukan airah ya Dame ta, ta dauke ta, ta nufi sashen su banan da niyar cewa ta goya mata ita tana so ta daura girki.

Sai ta sami banan daki kwance tana waqa da tsananin farin ciki a fuskarta,

Idan ba kunnuwanta ke mata gizo ba kamar waqar da banan keyi harda sunan el'mustapha a ciki,

_farin ciki a yau ya sameni_
_Dadi na rayuwa ya riskeni_
_Majaujawa ta so da ta daukeni_
_Sai ta barni gidan da aka raineni_
_Ta bani wanda nake so a badini_
_Soyayya na xata xata barni_
_Sai akace min naje an kyaleni_
_'Na auri wanda nake so ya soni_
_Kullum da safe in har ya ganni_
_Da murmushi yake qawatani_
_Naxo Musty ka in gantani_
_Eh..... Gani gaka_💃🏻

Jiddah ta shigo dakin hankalin ta a tashe take kallon banan, idanunta a rufe take waqar fuskarta dauke da murmushi cikin farin ciki, jiddah na tsaye ta qara dauko wani baitin,

_Cikin gidan mu akwai wani d'an yaro_
_Dadin muryarsa shi nafi sauraro_
_Farin wata nake shiko tauraro_
_Sonsa a xuciya da shi naci karo_
_Al'bishiri kuce min dan goro_
_Ya dan uwa musty xan yo koyo_
_Nayo Mari akan sa na bijiro_
_Lambar girma musty baya cin xero_
_'Na baka xuciya baniyi kwaro_
_Mai kyau kamar fulani uban toro_👍🏻
_Yau gani gaka bana jin tsoro eh... Gani gaka._

How I wish nima na xama BanantulMusty ka..... tayi shiru sakamakon saukar Mari da taji a kuncinta,

Ta bude idanunta da sauri ganin jiddah a gabanta ta xabura ta tashi cikin matsinanciyar faduwar gaba.

Kafin tayi wani motsi jiddah ta qara dauke ta da wani Marin cikin bacin rai, sai ga jini yana fita ta gefen bakin banan,

Kashe ni kuke son kuyi, me nayi maku, meyasa kuke son mijina, meyasa kuke son ganin bayana, farin cikina ne bakwaso ko me, ku raba ya'yana da farin ciki, baxan taba yafe maku ba, kuma bake ba el'mustapha har abada sai dai ki xamo  Banantulislam, kiji rani kiga hukuncin da xan yanke akan ki.

Ta fita a fusacce tana tafe tana sharar kwallah cikin tashin hankali ga wani xafi da xuciyarta ke mata,

Wayarta ta dauko, nabila ta kira cikin boye damuwarta,

Ki turomin islam gobe Nabila,

Lafiya jiddah naji muryarki wata iri.

Ba komai, ki turo min shi xamuyi magana.

Tace to shikenan jiddah.

Kuka sosai jiddah tayi, babu wata walwala ko sukuni a tare da ita, hajiya tayi juyin duniya tana tambayar ta taqi ta gayamata, haka ma abba, ganin yanda har idanunta suka kumbura.

Cikin qanqanin lokaci xaxxabi mai xafin gaske ya rufe ta, haka el'mustapha ya dawo ya sami airah gefenta tana ta kuka taqi ta kula ta.

Ya dauke ta da sauri yana kallon jiddah, yanayin ta kadai ya gane babu lafiya, ya kai hannunsa a jikinta ya taba xafi rau.

Me ya same ki jiddah, ta bude idanu da kyar tana kallonsa kafin ta maidasu ta rufe rub xuciyarta na cigaba da bugawa saboda tsananin tashin hankali.

Bai qara magana ba ya fita yana tambayar hajiya,

Nima nayi tambaya bata fada ba sai kuka take tun daxu,

Ya bata airah kana ya juya xuwa dakin,

Meke damun ki jiddah ya tambaya yana dago ta,

Batayi magana ba illah qara shigewa da tayi jikinsa, yana jin bugun xuciyarta ga jikinta yayi xafi rau,

Ko muje asibiti ne jiddah,

Ta girgixa kanta.

*

'Washe koda islam ya xo el'mustapha ya fita,

Tace ka gayamin gaskiya islam ka shirya auren banan.

'Na shirya anty jiddah, ki tambayi anty nabila tasan komai.

Tace ka turomin iyayen ka gobe suxo da sadaki, cikin satin nan xaa yi auren ka da banan.

Farin ciki ya mamaye xuciyarsa sai godiya yake mata, ya tashi ya fita,

Ta kira kakar banan ta gayamata tana son ganin ta gobe tare da kawun banan xaa yi auren ta cikin satin.

Duk shirye shiryen da ake ba wanda ya sani har el'mustapha da banan, sai bayan xuwan iyayen islam ne el'mustapha ya sani, shine ya xama kamar waliyin banan ya bada auren ta tare da wani kawunta.

El'mustapha bai san dalilin saka wannan auren da wuri ba kuma bai tambaya ba kada yayi laifi ace kuma son ta yake gashi jiddah cikin kwana biyu bata cikin walwala kamar wacce bata da lfy.

Banan kuwa da ta sami labari hankalin ta ya tashi sosai taga iyayen islam nesa ba kusa ba yafi qarfinta daga babban gida ya fito amma bata san meyasa take jin el'mustapha fiye dashi a xuciyarta ba, tayi kuka har ta gode Allah.

Ga sadakin banan cewar el'mustapha yana kallon jiddah.

Ka riqe hannunka, gobe xanje nayi mata duk abinda yace nayi a matsayina na mahaifiya na gayawa kakarta kada su wahalar da kansu ni xan mata komai.

Ni kuma me xanyi jiddah, abari na sami ladar aurar da marainiya jiddah.

Murmushi kawai tayi batare da tayi magana ba.

Cikin satin akayi komai na biki, kuma alhamdulillah biki yayi jama'a anyi komai lafiya an kai amarya.

Jiddah tayi mata hudu ba sosai, ta qara da cewa,

'Na xauna dake da xuciya daya banan bani da niyar cutar dake, tun kina qarama na dauki amanarki a wurin kakar ki, alhamdulillah na aurar dake ga mijin da nake ganin ya dace da rayuwarki, idan kika ci amanar sa Allah baxai barki ba, idan kika ci gaba da son el'mustapha a xuciyarki keda Allah kuma baxan taba yafe maki ba, ki rungumi mijinki da hannu biyu kuma ki so shi, mata da yawa a waje suna neman irin islam basu samu ba kada kiyi sake da damar ki, ko kashe auren kika yi kika fito baxaki taba auren El'mustapha ba hassalima baxaki xauna gidana ba sai dai kije qauyen ku kiyi zawarci.

Ta tashi ta fice, banan sai kuka take, ta dauki islam a matsayin qaddararta kuma xatayi masa biyayya ta xauna dashi da xuciya daya tasan jiddah baxata taba cutar da ita ba, el'mustapha ya riga yayi mata nisa har abada.

Jiddah na dawowa gida wanka tayi ganin dare yayi sosai, ta nufi dakin el'mustapha suna hada ido ta saki ajiyar xuciya tana kallon sa.

Ta kau da banan yanxu babbar matsalarta *UWANI* ce.........

Kallon ta El'mustapha yayi, kafin

Yace uwar amarya an dawo kenan.

Ta qarasa cikin dakin, shimfidar da airah tayi tana kallonsa,

Me ya hana ka barci tuntuni el'mustapha?

Rashin barci nawa kuma ya xama abin tuhuma yanxu jiddah, lallai

Sai ya gyara kwanciyarsa hade da lumshe idanunsa,

Ta tabe baki ta xauna tana fadi a ranta in ma banan ce ta riga ta xamo matar wani a yanxu.

Pampers ta soma sakawa airah, tayi feeding din ta kafin ta kai ta saman bed din ta, ta kwantar da ita, ta rage hasken fitilar dakin ta dawo bayan el'mustapha ta kwanta.

Haka take ji cikin kashi 70 na damuwar ta 30 ya kau, uwani ce babbar matsalarta a yanxu kuma bata san yanda xata bullowa al'amarin na ta ba.

Ta sauke numfashi a hankali tana kallon el'mustapha tuni ya jima da yin barcinsa, ta lumshe idanuwanta tana karanto addu'ar barci a xuciyarta.

*

Kuka take tana qarawa, lallai sai an maidata dakin ta.

Saboda baa sona ba wanda ke maganar yayi min aure a maidani dakin mijina abin sona, banan ma da take mai aiki anyi mata aure, ta auri miji mai kyau da kudi sai dan ni da ake ma baqin ciki anqi a maidani dakin mijina.

Sam hajiya bata kula ta ba, ta cigaba da hada kayanta saboda gobe xasu bar garin

Uwani ta tashi ta fito daga dakin taci sa'a kuwa el'mustapha ya fito xai je aiki,

Ta sunkuya tana fadin yaya an tashi lfy, yaya kayi haquri ka yafe min kuskuren da nayi a baya dan Allah ba danni ba ka yafe min, ka roqa min anti jiddah ta yafe min mu dawo tamkar da, dan Allah yaya ka taimakeni nima qanwar kace kuskuren da nayi a baya jarabawa ce da qaddara da bata wuce bawa.

Shikenan ki tashi komai ya wuce... yana maganar ne fuskarsa a daure,

Yaya a bani key din daki na xanje na gyara, yaushe xan fara karban girki.

Kafin yayi magana sai ga jiddah ta fito duk da bata ji me uwanin ke fada ba amma tayi mamakin samun uwani da el'mustapha a falon ta, gabanta ya tsananta bugawa.

Idan hauka ke damun ki uwani, na fiki hauka a yanxu indai akan el'mustapha ne, wallahi in baki barshi ba xan iya halaka ki ban damu ba.

Uwani ta tashi tana fadin haquri naxo na baki anty jiddah ki yafemin kuskuren da nayi a baya wallahi sharrin qawa ne, ni yanxu xuciyata a wanke take da alkhairi baxan cutar dake ba, ki qara roqon yaya ya aure ni ko baya da kudin sadaki ni xan iya ara masa, idan key din dakina yana hannunki ki bani naje na gyara.

Jiddah tace tau shikenan bari na baki, ta juya da sauri kamar mai neman wani abu

Ta rasa me xata dauka, kujerar dinning ta dauka tayi kan uwani a fusacce,

Uwani na ganin haka tayi bayan el'mustapha da gudu tana fadin,

Aa yaushe anti jiddah ta fara hauka kuma shine abba bai kaita itama a duba ta ayi mata aiki ba,

El'mustapha ya tare jiddah da sauri,

Me kike yi haka jiddah, kashe ta xakiyi?

Ko sauraren sa batayi ba tayi bayansa suka soma xagayen sa yana tsaye a tsakiyarsu, ya kalli wannan ya kalli waccan,

Lallai basu da hankali, wani abu ya taba kan jiddah indai ba gurin aikin bane aka taba kwakwalwarta,

Ya tsaida uwani cikin bacin rai yana kallon jiddah,
Chapter 57 · 0% Book details