← Book details El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 80

Sashe 49

El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kowa ma baya sona duk inda naje sai an cutar dani, yaran unguwa sai kallona suke, duk kyawuna da gayuna sun tafi a iska, na dawo kamar wata shegia a gari, wani maraya ma yafini gata a yanxu saboda kawai na cutar da jiddah, Allah ya ga xuciyata yanxu bani da wani mugun nufi a tare dani na shiryu baxan qara cutar da kowa ba ko daukar xugar qawa ama meyasa kowa baya yarda dani ne, ya suke so nayi da rayuwata duk gata na amma dubi yanda na koma a yau kuma anqi a tausayamin, ina suke son naje, ba inda xanje na sake fadawa halaka anan xan cigaba da xama har su yafe min, ta kwanta gurin tana kuka.

Barci mai nauyi ya dauke ta a gurin,

Duk wanda yabi gurin sai ya kalle ta babu mai tunani cewa uwani ce wannan sai dai kallon mahaukaciya ce, yadda aka san uwani da tsabta, ga gayu ko banxa tana da kyankyami akan mutane amma ita ce yau a hakan.

Kiran sallar magrib ya fito da abba da saurin sa xaije masallaci, kicibis yayi karo da ita kwance a gurin, girgixa kansa kawai yayi ya tafi abinsa.

Iskan hadari ya tada ta daga barcin da take, ta qara takurewa guri daya,

'Wannan rayuwar bata min adalci ba idan gaskiya ake bi ai wahalar da nayi jiddah batayi irin sa ba kawai dai dan ta rasa qafafun ne amma ni dube ni kamar yar tasha har wadanda suka haifeni basa sona.

Ba inda xanje anan xan xauna saboda duk duniyar nan ba inda yafi min gidan ubana, koda ruwan nan da xai sauko xai kasheni baxan bar qofar gidannan ba.

'Abba bai dawo gidan ba sai bayan isha, tana ganinsa ta tashi da sauri tana kallonsa.

'Abba dan Allah kayi haquri na tuba na bi Allah, ka yafe min kabarni na shigo naji dadin da kowace d'iya keji a gidan ubanta dan Allah abba kayi haquri.

Bai saurare ta ba ya shige hade da rufe gate din,

Tayi shiru tana kallon sama yanda ake ta xuba walqiya, ta xauna tana dafe cikinta, yunwa take ji amma ya ake so tayi tunda ba sata xata je tayi ba ko bata.

Tana xaune a gurin ruwa masu qarfi na fara saukowa, ta rakube guri daya da alama harda sanyi tana ji sai sharar kwallah take, wata wahalar ni najawa kaina ko yanxu na gane kuskure na, da ynxu ina can tare da anti jiddah ina cin dadi na kwanta cikin AC Allah sai ya sakamin baxan taba yafewa jamcy ba.

Ance d'a da mahaifi sai Allah, ya kasa samun nutsuwa sai tunanin uwani yake da halin da take ciki,

Abinda tayi kuskure ne ta riga ta aikata idan yayi laakari da shekarun ta kuma qaddara tana kan kowa, musamman idan yayi dubi da kowacece uwani kamar hankali bai ishe ta ba.

Tana aikata komai nata batare da tunani ko neman shawara ba kawai abinda yaxo ranta shi xatayi ba ruwanta ko xai baci ko xai gyaru burinta kawai ta biya buqatar ta.

Idan ya Kora ta tabi duniyar alhakinta na kansa kuma yana da kamashon lalacewar ta saboda macece kuma qarama mai rauni, ba abinda uwani ta cancanta kamar addua shiriya kuma yana qara roqon Allah ya shiryeta ya gyara ta yasa tuban da tayi har acikin xuciyar tane.

Umbrella ya dauko ya fito sosai ake ruwa, yana bude gate din ya ganta tsugunne a gurin ta rakube sai makyarkyata sanyi take,

Jin alamar bude gate din ya saka ta dagowa tunanin ta mai gadin ne ke leqenta tayi masa rashin mutunci, suna hada ido ta tashi da sauri,

Tausayin ta yaji, yar'su kwaya dal a duniya haka Allah ya rubuto da tata rayuwar, Sam uwani bata da nutsuwa, baiyi magana ba ya juya tana ganin haka ta shiga gidan harda rufe gate din,

Bayansa tabi tana fadin,
'Ashe dai abba kana sona, ai nayi tunanin xaka barni acan ne ruwan ya kashe ni, irin kune ake gani a aljanna ayi mamaki baa san tausayi ne da ku ba.

Kyaleta yayi baiyi magana ba, yana ganin sai an kai uwani asibiti an duba masa kwakwalwar ta.

Ta tsaya tana matsar kayanta har lokacin jikinta bai daina rawar sanyi ba,

Ta shiga falon tana kallonsa,

'Abba yanxu dai ka yafe min saura hajiya da anti jiddah, shi el'mustapha baxan roqe sa ba saboda yaci amanata ya kulleni a prison kuma ya harbeni a qafa banda ibrahim da yanxu ta fara wari ancire.

Shiru baice komai ba, sai kallonta yake cikin jimami,

Wayarsa ta dauka tana fadin abba bari nayi selfie da wannan kayan da datti saboda daga yau baxan qara xama acikin su ba, hassalima kayan meenah parrot xan baiwa su ko khadija candy.

Yana kallo ta fara daukar pic harda bashi wai ya dauke ta....

Tana gamawa dakinta ta nufa, ta jima sosai a ciki ta fito sanye da kayan barci bayan tayi wanka,

Yana xaune yana kallon news,

'Abba ni inajin yunwa kamar xan mutu, hanjina sai xafi suke suna bugun juna tun daxu.

Yace ai kinsan hanyar kitchen bana tunanin kin manta,

Har xata je sai kuma ta dawo tana kallonsa,

Wai ina hajiya ne abba hala dai bata ji dadin dawowa ta ba shiyasa Ma ta kasa fitowa?

Hajiya taje Germany,

Uwani ta xube qasa cikin firgici,

Germany abba, waye ya kaita?

El'mustapha ya bata amsa yana kallonta, sun je ayiwa jiddah aiki a qafar da kika nakasa.

Ta hadiye wasu yawu, wannan ba shine damuwar taba,

Tace yanxu abba kana nufin hajiya ta shiga jirgi kenan, innalillahi amma meyasa xaa min haka, ni nafi cancanta aje dani meyasa ake min baqin ciki ne, ta soma kuka kamar ranta ana mata baqin ciki da shiga jirgi banda haka meyasa baa jira ta ba ko anje an nemo ta.

Shiru yayi yana kallonta, shi dai yasan ba wannan ne karon farko da hajiya ta shiga jirgi ba ballantana uwani ta tada hankali, sunje Makkah sunje umrah to kwadayin me hajiya xatayi wa jirgi banda fitina ta uwani da rashin kunya har tana cewa aje da ita jinyar jiddah.

Shikenan abba babu komai tunda na gyaru, ina so a maidani makaranta, Cairo ko London ko sudan.

Yace ke me xakiyi da karatu keda babu abincinki aciki kuma kwakwalwarki baxata dauki karatu ba.

'Abba ka daina tuna baya wannan duk baqin cikin shaidan ne da sharrin xuciya, tuni na hango akwai abincina a karatu, akwai arxikina a ciki, nifa abba ina ji a jikina nan gaba first lady xan xama shiyasa har islamiya nake so ka sakani ko a aji daya ne xan xauna, ina so nayi ilimi saboda ya'yana kuma xa kuyi alfahari duk inda kuka shiga ana nuna ku ana ga iyayen uwani first lady 😊.... Bai bari ta qarasa ba ya tashi ya bar falon cike da haushi.

Ta bisa da kallo kafin ta tabe baki, wato har yanxu baa daina mata baqin ciki ba, ina laifin ta xama first lady ai abin alfaharin su ne.

Ta tashi ta nufi kitchen tana yan surutai, cornflakes ta gani babu batun cin abinci an dade baa hadu ba,

Qaton Cup ta dauko da spoon ta shiga neman inda aka ajiye madara.

*

Kallonsa dr merah keyi yana observing din sa, halayen el'mustapha suna burgesa sosai, akwai soyayya mai tsanani tsakanin sa da jiddah ba sai an baka labari ba kaida kanka xaka gano hakan.

Ya dafe kansa da duk hannayensa biyu cikin damuwa, meya hanata farfadowa, why ya fada a hankali yana Jan numfashi.

El'mustapha ya dago yana kallonsa daga cika wata takarda da yake, ya ajiye biron yana fadin.

Thanks once again Dr Aiman Merah,

Dr merah yayi murmushi yana miqa masa hannu,

Can we be friends?
El'mustapha bai bashi hannu ba kallonsa yayi yana fadin,

Xaka iya abota da d'an sanda ba jinin Mulki ko Sarauta ba?

Of course ya fada yana kallonsa, I have alot of friends like you,

Murmushi el'mustapha yayi kafin ya bashi hannu,

El'mustapha ya juya ya fita yana fadin ina jiran ka insha Allah yau xamu koma qasar mu da gawar jiddah.

Jiddah na kwance har lokacin idanunta a lumshe, jin alamar bude qofar ya sakata bude idanuwanta a hankali carab suka hada ido,

Kusan rudewa ko ince gigicewa yayi, ya rasa ina xai nufa ciki ko waje, jiddah ce ko dai fatalwarta ke mata gizo, shi ko fatalwarta jiddah ce yana so xai iya xama da ita, koda babu jiddah ya xamto ruhinta yana tare dashi,

Da sassarfa ya isa ciki har lokacin bai dauke idanunsa akan taba, sai kallo jiddah ke binsa da shi na mamaki.

Hannu yasa ya taba ta baiyi magana ba, ya qara riqo hannunta ya kai bakinsa ya ciza don son gasgasta jiddah din ce ko fatalwa.

'Wash Allah ta fada a hankali tana qoqarin xame hannun ta,

Ya rasa me xaiyi saboda tsananin farin ciki, sai kawai ya sami kansa da yin sujjada a gurin yana qara godewa Allah kafin ya taso ya rungumeta tsam a jikinsa yana sauke numfashi da sauri da sauri,

Jiddah is back, jiddana bata mutu ba I know, ya fara sumbatarta ta ko ina cikin rudewa kamar wanda xai maida ta ciki.

Shiru tayi tana sauraren wannan sabon al'amari daga el'mustapha, tasa hannu da kyar ta riqo fuskarsa tana kallonsa dai dai lokacin dr merah ya shigo tare da su yusrah da hajiya da nurses a bayansa.

Cak suka tsaya suna kallon ikon Allah cikin tsananin mamaki, jiddah ta janye jikinta tana qoqarin kwanciya el'mustapha sai qara rungumarta yake,

Dr merah da mutanen sa suka koma baya, anty yusrah sai washe baki take cikin tsananin farin ciki ita da su hajiya.

Qafata ciwo take el'mustapha ka barni haka,

Ya bude idanunsa a hankali yana kallon qafar, kafin ya dubeta,

Ina son ki jiddah cikin kowane hali, ko da qafar ko babu, ki rayu tare dani jiddana.

Murmushi tayi tana fadin, nima ina son el'mustapha cikin ko wane hali, son da ban taba yiwa kowa ne mutum a duniya ba bayan ummata.

Ya gyara xamansa, hannunsa na cikin nata  sai murmushi yake kamar wanda akayi wa albishir da gidan aljanna,

'Me na haifa el'mustapha?
Chapter 49 · 0% Book details