← Book details El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 80

Sashe 1

El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*EL-MUSTAPHA*

HASKE WRITERS ASSOCIATION
(Home of Experts and Perfect Writers)

Fertymerh Xarah💞

sɪsᴛᴇʀ ʙʏ ʜᴇᴀʀᴛ ʜᴀᴜᴡᴀᴜ ᴀʜᴍᴇᴅ ʀᴜғᴀ'ɪ, ʏᴏᴜ ᴀʀᴇ ᴛʜᴇ ʙᴇsᴛ❤

1_5

Motoci ne keta sharara gudu tsakanin titin kaduna xuwa Abuja,
A qalla motocin xasu kai shidda koma fiye da hakan,

Dare ne mai tsananin sanyi, cikin watan nuwamba, haxo ya lullube duhun daren ta yadda ya fidda launi mai haske kamar hadadden hadari, wanda ya takura da yawan al'ummar birnin tarayya.

Daya daga cikin motocin A.I.G (Assistant inspector General of police) El_mustapha Maneer ne tare da Matar sa.

Kallon ta yake cikin alhini da son sanin asalin damuwar ta, ta yanda har ta takure kanta nesa dashi tana kallon hanya ta glass batare da ta damu da ta kwanta a jikinsa ba kamar ko yaushe idan suna cikin mota xasuyi tafiya.

Yayi tunani ya kasa gano laifinsa gurin uwargidan sa tun bayan barowar su kaduna bikin wani taro da akayi.

Tana sanye da suwaita ta rungume hannayenta duka biyu a qirjinta, alamar tana jin sanyi sosai amma hakan bai hanata takurewa guri daya ba saboda tana fushi dashi.

Murmushi yayi marar fitar da sauti bayan ya dauke dubansa daga gareta, Jiddah rigima, kome xatayi a rayuwa tana burgeshi, yana sonta sosai, so bana wasa ba, komai nashi xai iya salwantar wa saboda ita, yana yi mata son da alqalamin Pherty baxai iya rubutawa a takarda ba, saboda yaransa dake cikin motar suna tsaron lafiyar sa ya hana yaje gareta ya rarrashe ta tare dajin laifinsa har ake wannan fushin dashi.

Jiddah kuwa qara takure jikinta tayi, xuciyarta nayi mata wani xafi ganin halin ko in kula da mijin ta yayi da ita a yau, tasa yatsun ta biyu batare da tabari ya gani ba ta dauke wasu siraran hawaye da suka xubo a idanuwanta tana cigaba da kallon titi xuciyarta a daqushe tare da tunani iri iri duk a kansa.

Wata sassanyar ajiyar xuciya ta saki lokacin da taji saukar hannunsa cikin tafin hannunta, ta juya tana kallonsa ta cikin hasken farin wata da ya haske motar, bata ganinsa sosai ta dai san ba ita yake kallo ba hakan yabata damar janye hannunta a hankali hade da qara matsawa nesa da shi cikin tunxuro baki idanunta taf da hawaye.

Jikinsa ya qara sanyi, meke damun Jiddah, meyasa ta canxa masa haka lokaci daya?

11:30pm

Suka shigo garin abuja, dirar motocin su ya sanya Uwani miqewa da sauri ta gyara powder fuskarta hade da qara feshe jikinta da turare mai sanyin qamshi.

Ta mirror take kallon kanta tana qara jujjuya jikinta, ita kanta tasani ta ko ina tayi bata da makusa har take ji Ma tafi matar gidan komai amma meyasa El mustapha ke ganin Jiddah tafi mata dubu a duniya, meyasa yake ganin Jiddah ce tauraruwa acikin mata, meyasa ya kasa gane yanda xuciyarta ta mutu da qaunarsa, har take kishin yar'uwar ta duk saboda shi.

Ina son elmustapha da izinin Allah sai na aure shi, sai na sami matsayi a xuciyarsa fiye dana Jiddah.

Jiddah tana fitowa motar bata tsaya wata wata ba tayi shigewarta kai tsaye, a falo taci karo da uwani tana fitowa kallon mamaki ta bita dashi wanda ya sanya uwani daburcewa...

'Uwani duk wannan kwalliyar ta mecece, ina xakije da wannan daren haka?

'Anty Jiddah.. Uhm.. dama Yusuf ne yaxo to bai jima da tafiya ba, yanxu dama nake so na cire kayan na kwanta sai naji dawowar ku shiyasa Ma na fito.... ta fada cikin murmushi

Jiddah bata bi ta kan xancen ba ta soma tafiya tana fadin,
'Naji gidan shiru, ina Arham da Aryan ne.

'Sun jima da yin barci bayan sun gama rigimar nemanki,

Jiddah ta juya tana fadin
'Alhamdulillah, domin a yanzu ba abinda taxi muradi,irin taga yaranta cikin koshin lafiya,ta haura steps, Uwani kallo ta bita dashi tana sauke numfashi a hankali ganin asirinta bai tonu ba, juyawa tayi ta fita harabar gidan inda ta tsinkayosa tsaye duk police sun xageya sa, da alama magana yake dasu yanda taga duk sun tattara hankalinsu da nastuwarsu ta reda sunkuyar da kansu suna saurarensa.

Wannan dalilin ya sanyata dawowa Falon xaman jiransa.

Kai tsaye ya shigo falon idanunsa na kan wayar sa da alama akwai abin da yake nema kamar mai son yin waya, ko wanda ze tura saqo,

Qamshin turarensa ya soma fisgarta, jikinta ya dauki rawa, nan da nan wata irin kasala ta rufeta, a yanda takeji kamar ko yatsanta ba zata iya motsawa ba,haka zuciyarta ke ingizata tamkar taje ta rungumeshi, bata san wane irin so take masa ba,

'Barka da dawo wa yaya, cikin dauriya tayi maganar,da kashe murya irinta mai jan hankali...

Ya dago rinannun idanunsa yana kallonta wadanda ke qara ruruta wutar qaunarsa a xuciyarta, cikin sakin fuska ya soma yi mata mgn,

'Mun same ku lafia Uwani, ashe bakiyi barci ba,

Murmushinsa kawai tamkar ya barar da Uwani a falon, don haka duk qarfin halinta sai ta kasa tankawa illah girgixa kanta da tayi domin idan ta tilastawa kanta mgn a wannan lokacin tabbas xata iya bayar da mata domin ba abinda xai hana mata fallasa masa sirrin xuciyarta, bugu da qari Ma bata ga fuska a tare dashi ba.

Batare da yabi ta kanta ba, ya nufi sashen sa, kallon sa take harya bacewa ganin ta, ta qara kallon jikinta, sama da qasa,tana girgiza kai tana mai tambayar kanta,

Ko bai lura da kwalliyar da tayi domin sa ba, baiyi mgn ba kamar yanda Jiddah tayi magana, sai ta tuna elmustapha yana da halin ko in kula akan kowa idan ba Jiddah bace, tana gani Jiddah kome xatayi sai ya yaba yayi godiya amma saboda ba itace gabansa ba ya kasa gano abubuwan da takeyi domin sa.

Jiki a sanyaye ta nufi dakin ta, kuka take na zuci har yafito fili,tayi kukan sosai, Wanda tana ganin yin hakan kadai xaisa ta sami sassauci daga xafin da xuciyarta keyi ma ta, kamin ta samu damar cikar burinta.

Jiddah kuwa sai da ta duba yaranta biyu, twins maxa masu shekaru shidda shidda, tayi masu addua, wadda acikin ranta, tana fatar ta rayu da su har izuwa girmansu,kafin ta numfasa, taja musu kofa, ta nufi sashen ta,

Tana cikin cire kayan jikinta ya shigo dakin,ko baa fada ba tasan waye sai tayi qoqarin shigewa toilet, yayi saurin riqota yana kallonta,

'Haba jiddatulmusty, wannan fushin duk na menene, na kasa gano laifina, ki gayamin.

Ta dauke kanta gefe tana tunxuro baki, bai yi fushi ba saboda kome Jiddah xatayi masa a rayuwa yana birgesa yana sonta da yawa,

'idan kuma baxan sami amsar tambayata bane shikenan, xan barki kiyi ta fushin amma nima xanyi fushi da kowa da komai a gidannan har lokacin da xaki daina fushi dani ciki kuwa har abinci xan daina ci, ya juya kamar da gaske xai bar dakin yasan ba abinda ta tsana kamar xamansa da yunwa, kamar daga sama yaji muryarta,

'to ba kai bane.... sai kuma tayi shiru ya juyo yana kallonta,

'dana yi me?
'Na ganka da wata kuna magana, kuma qasaqasa kukeyi, har kuna dariya, kana so ka batamin rai ne kuma kayi Nasara and what else? Sai ga hawaye sharrr suna bin kuncinta, ba abinda ta tsana a duniya kamar ta bude idanu taga mijinta da wata mace, tana da mugun kishi, kishi mai tsanani kuwa shi kansa ya san da haka.

'ya salam.... Ya furta a hankali bayan ya dafe goshinsa da hannunsa na dama, ya dago yana kallonta,

'kin san wacece kuwa? Me xanyi da wannan matar jiddah?

'idan hakane meyasa kaja ta can gefe inda ba kowa kuna magana, kuma naga harda hannunka ta taba baka hana ta ba.

'saboda ke ne Jiddah, nasan kishi irin naki bana son bacin ranki ko kadan ya sanya na jata nesa da mutane muyi mgn amma meyasa idan kishinki ya rufe maki ido kina manta ko waye mijinki?,pls Jidda don't ever doubt ur trust in me, I give you my heart so honestly!,

Tayi shiru bata tanka ba, sai dai ta sami nutsuwa a xuciyarta domin ta yarda da mijinta baxai taba mata qarya ba,

'Wannan matar is a Christian, matar Captain Johnson ce, tana min mgn akan abubuwan da yake mata ne bayan ya rabota da qasarta yaxo da ita inda bata san kowa ba yana cutar da ita, tana ganin ba wanda xai masa mgn yaji kamar ni wannan dalilin ne yasanya har kika ganni da ita, maganar riqe min hannu da tayi kinsan su a gurin su ba wani abu bane halin da take cikine ya sanya na kyaleta.

Ta saki ajiyar xuciyata tareda wani zazzafan iska, wanda batasan tariqe shi ba se fitowarshi ta ji, hade da langabe kanta gefe tana kallonsa, se cemata yayi breath my dear....and don't repeate to act like dat I can take it anymore my dear, I am madly in love wit yhu, habawa da sauri Jidda ta dago kanta suna had'a 2eyes ya ce yes my Jiddah I love u.......pls say something I want to hear ur sweet voice,

'Cikin tsanaki ta bude bakin tace am sorry.... My dear Ka yafe min, yaja dogon hancinta yana murmushi,kurawa juna idanu sukayi 4 sometimes at d end Elmustapha ya janye Na shi tare da bata peck a forehead da kumatunta,

'I love you jiddana... ta fada jikinsa tana dariya, ya dauke ta cak suka nufi toilet.

My Wattpad Phertymerh1
*El_Mustapha*

Haske writers Association

Fertymerh Xarah💞

6_10

'Uwani.... Uwani, take kiranta cikin muryarta mai sanyin gaske,

Shiru Uwani bata amsa ba kuma bataji motsinta ba hakan ya bata damar isa dakin nata tana kiranta,

Babu alamar ta a dakin amma ta jiyo motsinta a toilet, ta fita daga dakin, harabar gidan ta nufa sashen masu aiki,

Bata jima ba ta dawo tare da wata yar budurwa a bayanta,

'kinga yanda su Arham suka bata falonnan, kuna cikin gidan amma ba wanda yayi tunanin gyarawa, idan wani baqo yaxo ya same ni a haka fa, ko shi maigidan?

'Dan Allah kiyi haquri hajiya, ba wanda ya gani acikin mu.... tayi saurin katse ta,
Chapter 1 · 0% Book details