← Book details El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 80

Sashe 38

El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jiddah taka ce har abada, soyayyar jiddah ka dade da samu tuntuni, babu wani sauran guri da ya rage a cikin xuciyata da ban cike shi da qaunar el'mustapha ba, sai ta tsinci kanta da matuqar jin kunyarsa a yau ta dauke kanta gefe tana murmushi mai bayyana farin cikin dake xuciyarta.

Shi ma yabi ta da wani murmushin da har abada baxai taba gushewa a xuciyarta ba, yabi bayanta a hankali ya kwanta bayan ya soma xuba mata xafafan kiss a ko ina na gangar jikinta.

El'mustapha ya dauke ta ya jefata  a wata duniyar soyayya da ta jima bata je ba, ya mantar da ita rashin lafiyar dake jikinta, ya mantar da ita damuwarta har tana jin kanta kamar jiddah farko mai lafiya, ya rungumeta hannu biyu tare da nuna mata xallar soyayyarsa batare da ya kyamace ta na kasancewar ta nakasashiya ba, ta saka hannuwanta biyu ta rungumeshi sosai kamar xata maidashi ciki saboda so.

*#Asuba ta gari*
*Jiddatulmusty*

Pherty........... ✍🏻

2 days....

Yana dakin jiddah yana shirin fita office kamar yanda ya qudira a yau, tunda aka kwantar da jiddah asibiti bai je ba sai yau.

Ya juyo yana kallonta, tana xaune akan wheel din ta, ta tsura masa ido tana kallon duk wani movement nashi a dakin.

Oh ni el'mustapha, shikenan na xama gwauro komi ni kema kaina andaina min, matata sai dai ta miqe qafafu ta xauna tana kallona.

Murmushi kawai tayi batare da tayi magana ba, ya dawo gabanta ya xauna yana kallonta.

Tun daxu kike bata fuska jiddah, baxan jima ba xan dawo, I know your condition baxan je na barki ba, ya shafi fuskarta yana kallonta,

Me kike so naxo maki dashi? Sai ga hawaye sharrr na bin kumatunta, el'mustapha yaja numfashi ya dawo gabanta ya tsugunna,

Saboda xan fita kike kuka jiddah?, ta girgixa kanta a hankali, ta dora hannunsa akan cikinta,

Ni nagaji da xaman ne, cikin ba dadi duk yanda nayi bana jin dadin sa.

Yace sorry jiddah kin kusa haihuwa ki huta, in kira maki banan ta xagaya dake cikin gidan ko xakiji dadi,

Ta girgixa kanta da sauri,

In kwantar da ke ne, sai kiyi barci kafin na dawo, ta gyada kanta tana kallonsa, yaja keken har wurin gadon ta, ya dauke ta ya kwantar da ita yana kallonta.

Kiyi barci banda tunani jiddah baxan jima ba xan dawo, meeting din ya xama dole ne kinga sai kirana ake.

Ta gyada kanta tana kallonsa, ya sumbace ta yana qoqarin tashi, yaji tana fadin.

Allah ya dawo da kai lafiya,

Yace amin jiddatulmusty, cikin murmushi ya dauki wayarsa da key din sa ya fice bai qara kallonta ba dan yasan xata karya masa xuciya, kamar kada wannan lalura ta same ta duk ta xama rigimammiya bai sani ba ko cikin ne oho.

Tun da ya isa wurin meeting ake ta masa jajen abinda ya sami matarsa wadanda basu sami damar xuwa ba kenan,

Murmushi yayi kafin yace I am soliciting for your kind prayers, my wife was free and discharge, thanks for your concerns, ya xauna.

Sun dauki fiye da awa biyu suna meeting din, duk hankalinsa yana gida binni binni yake kallon time,

Qarar message yaji a wayarsa yana dubawa kuwa yaga jiddah ce,

_Feeling lonely El'mustapha, kaqi ka dawo ni na gaji da kwanciya_.

Jikinsa na rawa ya tura mata,

_on my way, am sorry_!

Ya maida wayar aljihu cikin qaguwa da meeting din.

Fitowarsa meeting keda wuya mutane suka yo masa caaaa abinka da babban mutum mai matsayi,

Menene el'mustapha ya tambaya cikin mamaki yana kallonsu,

Sir yan media ne suka xo, tuntuni suke xuwa basa samun ka, suna so suyi interview da akai akan kidnapping na matar ka.

Ibrahim yace, kuyi haquri yana sauri har xuwa wani lokaci,

Ka barsu el'mustapha ya fada yana kallonsu yana kallon agogon dake hannunsa, minti biyu na baku.

Da sauri suka nufe sa, bayan sunyi guntun bayanin da xasuyi suka soma tambayar sa,

Sir ance anyi kidnapping matar ka, ka ganta? Su waye suka sace ta?

Eh na ganta kuma masu laifin da aka kama suna hannun hukuma sauran kuma an kashe su, shikenan ya tambaya cikin qaguwa?

Sir ance sister din tace ta saka aka dauke ta saboda wata buqata tata daban, wace buqata ce wannan kuma wane mataki ka dauka akanta, harda ita tana hannun hukuma ne ko me?

El'mustapha ya gyara tsayuwar sa yana fadin what I know if you are working on something that you really care about, you don't have to be pushed, the vision pulls you...... Ya fara tafiya, sukayi ruuu xasu bisa yan sanda dake gurin suka hana har sanda ya shiga mota yabar wurin da sauri.

*

Wayyo Allah, Wayyo Hajiyata, Abba kuxo ku taimakeni, wlhy kashe ni xasu yi, na tuba abba ka yafe min.....

Sautin muryar uwani ke tashi dakin da aka rufe ta tare da wasu mata hudu wadanda kusan kullum sai sun axabtar da ita saboda kafiya da taurin kai irin nata.

Duk suka mata magana sai ta maida, idan suka saka ta abu batayi, bata respecting dinsu su kuma basa raga mata ko yaya ne a xamantakewar su.

Yanxu ma daga wurin karbo abinci suke, sun amshe nata sun cinye ta masu mgn suka yi taron dangi suke dukan ta.

Sai da suka mata liga liga su ka barta suna huci,

'Dan ubanki ni xaki gayawa magana akan wani abinci na banxa to an cinye idan akwai wanda xai kwatar maki yaxo kuma yau bake ba cin komai ko kin karbo anjima wlhy baxaki ci sa ba sai dai ki mutu, shegia tsigagiya cewar runkes tana numfashi.

Wadda ake kira da A.j kuwa xama tayi tana numfashin,

Ke har kin isa ki same mu a gidan mu kice xaki mana rashin kunya, yar firit dake haka wannan ko sa'an autan gidan mu kinyi, xan koya maki hankali ne, tasa hannu ta jawo uwani keeeey,

Tashi xaune ki share hawayen nan tun ban nakasa ki ba,

Uwani ta tashi jiki na rawa, ga qafarta sai ciwo take sosai duk da gurin ya warke wajen dukanta suka ji mata ciwo a wurin.

Jikinta sai kyarma yake, ga yunwa dake damunta,

'Dan Allah kiyi haquri anti Aj, karki qara dukana,

Aj ta bige mata baki tana fadin, shegiya mayya inta fara baka haquri kamar gadon ubanta kaci.

Runkes ta xauna batare da tayi magana ba banda hararar uwani ba abinda take.

Ladidi ce kawai ba ruwanta, bata hayaniya da kowa a cikinsu kuma tasha gayawa uwani idan bata gyara ba xasu kashe ta ne a banxa tunda kusan kullum sai sun dake ta saboda taurin kanta.

Ladidi tace yi haquri aj ki kyaleta dan Allah,

Ladidi ki daina tausayin wannan ja'ira yanxu ne kin taimaketa anjima ta fara maki rashin kunya ni maganin ta xanyi.

Babu komai yi haquri ki barta baxata sake ba.

Kinci albarkacin ladidi da sai kin yabawa aya xaqin ta, tashi ki ban wuri sakarya, kuma da kin karbo abincin nan ki kawo shi idan ba haka ba wlhy daren yau baxakiyi barci ba, uban ki xanci a dakin nan.

Ladidi taja hannun uwani suka matsa can nesa dasu kadan, sai dingirsa take, suka xauna

Tace wai uwani meke damun kine tun da kika xo gidannan kwana biyu kacal kikayi kowa ya sanki, ko abinci akaje karba sai kinyi fada da mutane, ayi maki magana kina maidawa meyasa.

Uwani ta share hawayen tana fadin, ke ina ruwanki dani ne, tunda kin gayamin naqi ji basai ki barni ba, idan sun kashe ni miye damuwar ki, ai gwanda su kashe ni na huta da wannan rayuwar dana ke ciki.

Ladidi tayi shiru bata mamakin kalaman uwani ta saba gayamata magana mai xafi fiye da wannan.

Tace uwani gayamin laifin me kikayi aka kawo ki nan,

Sai ke kin fara fadamin naki tukunna, haka kawai kiji sirrina batare dana ji naki ba.

Ba abin damuwa bane uwani, sunana ladidi, inda na fito basai na fada maki ba, mu biyu ne a gurin iyayen mu nida yaya na, akwai wata maqociyar mu mai suna bilkisu bata taba haihuwa ba kuma tana son yara sosai, haka kawai Allah ya dora mata sona a xuciyarta.

Kullum xata je gidan mu ta daukoni, tabani abinci tamin wanka, tana min komai da nake so, kasancewar mijinta yafi iyayena kudi sai suka bata ni a matsayin yar riqo.

Ta riqeni da amana tamkar yar cikinta, tana sona ta sakani a makaranta boko da islamiya, tana min sutura sosai idan kika ganni sai ki dauka itace ta haifeni.

Sai ya xamana babu ruwana da iyayen da suka haifeni sai nafi sati Ma banje gidan ba, su kuma basu damu dani ba tunda ga yaya na.

Girmana na tasowa a lokacin mijin nata ya soma nema na da lalata, wai xai aureni ya jima yana sona tun ina qarama, idan Ma ina so xai iya sakin anti bilkisu ni ya aure ni dan idan bai same ni ba rayuwarsa xata iya lalacewa.

Ban taba jin sonsa ba uwani, ina masa kallon ubana kuma yaya na, ina son anti bilkisu kamar yanda take sona, ban taba ji ko sau daya a rana xan iya cutar da ita ba ballantana har na iya lalata da mijinta ko auren sa.

Matar da ta raine ni tun ban san kaina ba, ta fito dani a mutum, nayi karatu na sami ilimi, wlhy yayana baiyi karatu ba iyakar sa primary, saboda iyaye na basu damu da su nemawa ya'yan su ilimi ba, har gobe ina jin dadin da ban taso a gurin su ba da ko na arbiya banda a yanxu.

Ban sanar da ita komai ba saboda bansan yanda xata dauki xancen ba ina matuqar tsoron abinda xai hadani da ita taxo tana min kallon muguwa mai manta alheri.

Nayi qoqarin boye sirrin amma kusan kullum dare sai yaxo min dakina, ina barci xanji yana shafa jikina, da kokowa da komai nake samu na kwaci kaina naje na buya a toilet.

Ko na rufe dakin da key xai bude da wani ya shigomin, idan kuma fita unguwa tayi ta barni saboda nayi girki wlhy a gidan mu nake xuwa nayi mata saboda tsoron sa.
Chapter 38 · 0% Book details