← Book details El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 80

Sashe 30

El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'Anty ikram da kanta ta soma share masa hawayen, a yanda el'mustapha yake jin kansa tamkar qaramin yaro, yau ya rasa maman sa, yayi kukan mutuwa a karo na biyu bayan na baban sa, bai san wanene na uku a rayuwar sa ba.

'Anty ikram, mama has gone, shikenan babu uwa babu uba, shikenan baxan qara kwanciya a jikin mama ba, baxata qara min fada ko rarrashi na ba, mama baxata qara bani  abinci a baki ba, mama baxata qara saka ni dariya ko share min hawaye ba,mama baxata qara shafa kaina ta samini albarka ba,  tell me meyasa baxan yi kuka ba, meyasa baxan xubar da hawayen rashin uwa ba?

Daga anty ikram har anty yusrah kuka suke,

Inna lillahi wa Inna ilaihir raji'un, shine abin da mutane ke Nana tawa a xuciyar su a duk lokacin da suka ji mutuwar mahaifiyar AIG, Mace mai fara'a da karamci, kowa nata ne babu kyama ga talakawa haka kuma bata koyawa ya'yanta su kyamaci wani mutum a duniya ba duk yanda yake.

Bayan sadakar bakwai, abubuwa suka soma yiwa el'mustapha yawa, ya saka mama a xuciyarsa sosai yake mafarkinta, bashi da nutsuwa a koda yaushe sai nema mata gafarar ubangiji.

Anyi saa uwani tayi masa gaisuwar mutuwar cikin nadama da qasqantar da kai kamar mai roqon el'mustapha xai maidata.

*

Inna ige yau kam ina jin motsin abinda ke cikina, ina roqon Allah ha rayamin shi har xuwa lokacin da xan haifesa, cewar jiddah tana kallon tsohuwar da aka dauko domin kula da ita cikin murmushi tana shafar cikin.

Ai na gayamaki ina karban haihuwa a karkarar mu, kowa yasan ni ungoxuma ce, tun da nace kisha wannan gayen komai xai warware ai kinga kin sami sauqi.

Jiddah tayi murmushi tana kallonta, nagode Inna ige, kin taimakeni da yawa, kin nuna min so da kulawa babu kyama, ina Ma ina da abinda xan saka maki dashi a yanxu da na baki domin nuna godiyata akan ki.

Karki damu jiddah, da na kowa ne, amma xan tambaye ki, me kikayi aka kawo ki nan?

Hawaye suka taru idanun jiddah,

Banyi komai ba Inna, kishiyata yar uwata ta jefani a wannan halin saboda mijina, ba wannan ne damuwata ba kamar ciwon qafata, dubi yanda ta kumbura, ina tsoron wani abu ya same ni na kasa tafiya a rayuwata.

Inna lillahi, kishiya jiddah?

Jiddah ta maida kallonta ga cikinta tana murmushi, ta daga rigarta tana kallon yanda yake motsi, farin ciki fal a xuciyarta ta san komenene yana cikin qoshin lfy.

Hala shine cikin farko jiddah?

Jiddah ta dube ta tana girgixa kanta bayan ta rufe jikinta,

Ina da yara biyu maza tagwaye, na jima ban sami haihuwa ba kafin wannan, duk abinda ke ciki ina son sa ne saboda ya wahala, jiddah ta bata labarin komai, Inna tayi matuqar tausayawa jiddah harda kwallah tayi.

A yanda na tsani uwani bana son ko sunan ta naji an ambata a tare dani, ta cutar da rayuwata baxan taba yafe mata ba, ta soma kuka.

Inna ige tace ni Allah xai saka maki jiddah tabbas wannan matar baxata gama duniya lafiya ba.

Ina so na taimakeki jiddah amma ina jin tsoro,

Jiddah ta dube ta, kada kiji tsoron komai na gayamaki mijina dan sanda ne, idan suka maidaki gida yau ki qoqarta kije ki sanardashi, xan baki lambar wayar da xaki kirasa ko kuma na baki address din office din sa.

Inna ta ciro wayar ta cikin xaninta jikinta na rawa ta miqawa jiddah tana fadin,

Ko ki gwada kiransa yanxu kiji, jiddah na qoqarin amsar wayar taji wani sauti daya hargitsa tunanin ta sai ga Inna xube a qasa cikin jini,

Jiddah ta rude taja baya tana kallon qofar, kurma ne tsaye fuskarsa tamau ba alamar imani a tare dashi, ba tare da tunanin komai ba ya dauke fuskar jiddah Mari, tayi dif saboda Marin ya shige ta sosai, ta dauki lokaci kafin jinta ya dawo gare ta sai ga jini na fita ta hanci da bakinta.

Goga.. Goga.. Kurma ke kiransa cikin kakkausar murya kamar wani basaraken xaki, goga na shigowa ya nuna masa Inna ige,

Dauke min wannan shegiyar ka fice min da ita a gidannan, ajiye ta a qofar gidan idan mun tashi shiga gari muje da ita mu yar da.

Goga ya juya ya kira yan uwansa dan baxai iya ba shi kadai, yana mamakin me tayi aka harbeta.

Ke dan ubanki ni xaki ci amana, kinma samu ina tausayamiki bana baki wahala har kike son tona min asiri, to daga ba wannan xan nuna maki ko waye kurma, babu sauran tausayi tsakanina dake, kuma kome kike so ke xakiyi da kanki ba wanda xan koma daukowa.

Rarrafo ki fito nan, tun bansa kan bindigar nan na fashe maki tsakiyar kai ba,

Da sauri jiddah ta soma rarrafowa tana kuka, a falon ya nuna mata inda xata xauna tana kallo aka fita da gawar Inna, a wane qauye Inna take su waye yan uwanta duk bata sani ba, ashe haka suke da yawa bata taba sani ba harda mata a cikinsu kowace tana xuqar sigari,  maxan kuwa sai giya suke sha, ta juya tana kallon inda kurma yake xaune suna hada ido sai da cikinta ya hautsina, mararta ta qule saboda wani fitsari da yaxo mata.

Ina jin fitsari, shine abinda ta fada tana kallonsa cikin rawar jiki,

Ya xuqi sigari ya furxar da iskan yana kallonta,
Kiyi sa a nan ki xauna a cikinsa, xan axabtar dake ne na daina tausayinki,

Tayi tunanin idan tayi fitsarin Dame xatayi sallah, dama a xaune take yin abinta, yanda take ji baxata iya riqe fitsarin ba, ta riqe cikin tana sharar kwallah, sai ga fitsari na fitowa qasanta ya soma gangarawa,

Kurma ya bita da kallo bayan ya ajiye sigarin, ta tsorata a tunaninta ko wani abin xai mata ne,

Tace kashi nake ji...
Shima kiyi sa anan dan ubanki, kurma ya fada bayan ya tashi yana gyara bindigarsa,

Goga... Goga...
Kawo min ruwa da tsumma ta gyara gurinnan da ta bata kafin na hasala na dauke dayan qafar da bullet.

*

Kwana biyu uwani ba kudi kuma tana so ta fita ko mai babu a motar ta, duk ta kode ta dawo wata iri, ko gayun yanxu an daina, ba ruwanta da kowa a gidan.

Tana xaune taji dawowar su aryan daga skul, ta fita daga dakin sukayi karo da aryan a falo,

Sai da ya tsorata da ganin ta, ya juya da gudu ya bar falon tsoronta suke sosai, tan fitowa taga driver yan so fito da arham motar yaqi sai kuka yake,

Rufe motar ka kyaleshi kada ya fito ina ruwan wani, uwani ta fada bayan ga rufe arham a motar, ta karbi key din motar ta juya cikin gida ta shirya ta fita kafin el'mustapha ya dawo, dama tun bayin mutuwar mamansa take samu tana fita.

Arham yayi kuka sosai har barci ya dauke sa a motar, ya kwanta yana maida numfashi, uwani na fitowa Sam ta manta da wani arham a motar ta shiga ta ja abinta ta fice daga gidan, ta jima da fita sai ga el'mustapha ya dawo, bashi da wani buri a yau kamar ya gansa a gaban uwani, sun riga sunyi tracing layin har record na yanda tayi da jiddah ta fito gidan duk yana da.

Yana fitowa sai ga banan dauke da aryan sai dube dube take alamar tana neman inda arham ya shiga.

Sun dawo skul amma banga arham ba cewar banan tana kallon el'mustapha,

El'mustapha yace arham ai baxai bata a gidannan ba indai driver ya dawo dashi, where did you left him aryan.

In the car... ya fada yana kallon el'mustapha,

Suka juya suna kallon motocin gida,

Yace sauke shi banan xo ka nuna min wace mota ce,

Ya qanqame banan alamar baxai sauka ba, ya dube sa yana fadin daddy our school car, ai anty uwani ce tace a barshi a ciki tunda baxai fito ba shine taje ta rufe shi acikin motar.

El'mustapha ya duba ba motar, hankalinsa ya tashi yana tambayar driver dake kai su skul, yayi masa bayanin komai, ya dawo yana kallon banan koma ciki da aryan cool your mind komai yaxo qarshe.

Wayar sa ya ciro, office din su ya kira yana buqatar yan sanda nan da minti goma, ya dubi DSP Bello Marona😜,

Kiramin ibrahim na kasa samun sa, ya laluba aljihunsa yaji bindigar sa na nan, ya juya da sauri ya shiga cikin gida, bai jima ba ya fito cikin uniform din sa, fuskar nan tasa ba walwala ko kadan.

Amma ta ina xasu soma neman uwani, ina ta nufa duk basu sani ba sai sun jira dawowar ta.

Jiddah kuwa da kyar ta gyara gurin, sai taji cikin ya koma mata gefe daya, tayi amfani da ruwan da aka kawo ta xuba a jikinta tunda ba wani xane da xata sauya, duk abinda take idanun kurma na kanta har lokacin da uwani ta shigo gidan.

Tana yin parking arham na tashi daga barci, ta fita daga motar cikin sauri ko rufewa bata yi ba, ya tashi yana kalle kallen sabon gurin da ya gani a yau, yana ganin inda uwani ta shiga ya fito yabi bayanta batare da tsoro ko fargaba a tare da shi ba.

Uwani na shigowa suka ci karo da kurma,

A kashe min jiddah ka gayamin ko nawa ne xan biya daga yau xuwa gobe,

Jiddah ta dago tana kallonta cikin tsananin tsoro da mamaki,

Kurma ya xuqi sigari yana murmushi da alama xancen ya masa dadi tunda xai yi kissa,

Mummy........ Shine sautin da suka ji ya fito dai dai qofar shigowa falon, gabaki dayan su suka juya suna kallonsa,

Bugun xuciyar jiddah ya tsananta da ganin arham, tsoro ya bayyana a fuskarta lokacin da taji uwani na fadin,

'Na manta yaro nan yana cikin mota naxo dashi, tabbas idan na koma dashi asirina xai Toni xai iya gayawa el'mustapha, shima ka kashe shi....

Jiddah ta xaro idanu tana kallon lokacin da arham ya nufo ta da gudu yana kiran,

I miss you mummy...... Jiddah ta daqa hannu tana tsaidashi cikin daga murya ganin kurma ya saita shi da bindiga,
Chapter 30 · 0% Book details