← Book details El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 80

Sashe 54

El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ki kwantar da hankalin ki jiddah, idan har uwani ta yaudare ki ta auri mijinki ta cutar dake banan baxata auri el'mustapha ba, ya rantse baya son yarinyar nan, kema ya rantse maki, ya kike so ya yine xai maki rantsuwa da qarya ne?ni kam ban baki tarbiyar da mijinki yana fada kina fada ba dan baki taba ganin nayi da abban ku ba, idan yana fada shiru nake koda nice da gaskiya indai ransa ya baci na bashi haquri sai kiga ya sauko daga fushin ya xauna mu fahimci juna, ban san ki da wannan ba sam ba halin ki bane, banan din ya kamata ki hukunta ba el'mustapha ba, yaron nan yana son ki jidda.

Amma hajiya s.... bana son gardama idan ya shigo ki bashi haquri kece baki da gaskiya nayi masa rashin kunya ki tsaya ki saurare sa kinqi sai fada kike, kuma kada ki sake sako yarinyar nan a fadan ku har kice baxaki shayar da ita ba.

Jiddah ta fara kuka sosai kowa laifin ta yake gani, sunqi su gane halin da take ciki da abinda take ji a xuciyarta, wane haquri ne batayi ba a baya, wane jajircewa ne batayi ba na ganin ta aurawa uwani el'mustapha wanda haqurin bai mata amfanin komai ba sai Ma wahala da ta shiga, saboda me yanxu xata haqura ta bar banan tana son mijinta, idan su basu san xafi da radadin da ta fuskanta a baya ba ita ta damu da ta ta rayuwar kuma baxata taba bari el'mustapha ya auri banan ba indai tana numfashi a doron qasa.

Ba kuka nace kiyi ba, kici abinci kisha magani, yau na lura ko barcin rana da kike yi bakiyi ba kada ki jawo wa kanki wata matsalar.

Jiddah bata kula ta ba illah kukan da ta cigaba da yi, suna haka el'mustapha ya shigo dakin, duk da taji shigowar sa hakan bai sa ta dago ko daina kukan da take ba.

Hajiya tace naji dadin xuwan ka, taqi taci abinci tun daxu maganin Ma bata sha ba sai kuka take.

Ya ajiye kayan da je hannunsa har lokacin fuskarsa ba walwala akwai sauran fushi a tare da shi,

Yace saqo ne Dr merah yace a bata daga gurin matarshi kafin taxo duba jiddah, ina ji kamar abinci ne aciki.

Hajiya ta duba kayan, abinci ne da kayan marmari na lambu da ganin yanda aka hado kayan fruit din kasan gidan sarauta suka fito, ta debi abinda take so ta fita goye da jaririyar tana fadin idan bata ci ba kanta, ka xauna kaci ka qoshi sauran ka bani na cinye sai tayi ta cin kukan.

El'mustapha dai bai ce komai ba, xuba abincin yayi ya qarasa gurin jiddah, tana jinsa a kusa da ita ta dago tana kallonsa, fuskar nan tasa ba walwala sai taji ba dadi jikinta yayi sanyi, ba qaramin abu ke saka el'mustapha wannan fushin mai tsanani ba.

Ya debo abincin a spoon ya kai bakin ta, ta riqo hannunsa, cikin rawar murya tana xubar da hawaye,

Tace kayi haquri el'mustapha, baxan qara ba.

Yace ba komai ya wuce kici abincin,

Baka haqura ba idan har wannan fushin bai bar fuskar ka ba, forgive an forget baxan qara ba I promise you.

Yasa qaramin yatsansa yana share mata hawayen kafin yace na haqura jiddah nasan ba halin ki bane kuma bana son ki dashi ki barshi da uwani yafi dacewa not you.

Tsura masa ido tayi tana kallonsa, shima kallonta yake kafin yace saboda damuwa kinga yanda kika dawo just for only today,

Bata ce komai ba ta soma karban abincin da yake bata, nan da nan suka shirya kamar wani abu bai taba hada su ba.

Koda hajiya ta dawo dakin tayi mamakin ganin jiddah kwance a jikin el'mustapha sai dariya suke cikin farin ciki.

A gurguje pls😒

2 months....

'Alhamdulillah jiddah na samun kulawa sosai gurin dr merah har ta soma takawa da qafar sai dai ba sosai ba.

Cikin wannan lokacin harda aikin uwani anyi batare da sanin su hajiya ba.

Ganin jiddah ta sami sauqi sosai har tana iya taka qafar ko bada stick ko wani ya riqa ta ba suka soma shirye shiryen dawowa gida cike da farin cikin dimbin nasara da suka samu akan aikin jiddah bayan sun cire tsammani daga qafar baxata qara moruwa ba.

EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association
Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞

55

Saukar su Nigeria ke da wuya, motocin gidan El'mustapha suka iso airport.

Cikin masu tarbar su jiddah harda su anty ikram da yusrah,

Cike da tsananin mamaki suka rungumeta suna kallonta qasa da sama, kamar bata taba samun wata lalura tare da ita a qafar ba.

Welcome back jiddah, Allah ya qara lafiya mai amfani cewar Nabila tana kallonta cikin murmushi.

Jiddah kallonta tayi tana fadin kin goge laifin ki na rashin xuwa duba ni a Germany, kika xo tarbata, naji dadi sosai Allah ya bar xumunci.

Amin ta fada cikin murmushi.

El'mustapha yayi gaba da baby rungume a jikinsa, Allah kadai yasan irin farin cikin dake xuciyarsa.

Suna iso wa gida sunyi mamakin samun mutane haka duk yawanci daga gurin aikin el'mustapha ne sunxo taya sa murna, kuma sosai ya nuna farin cikin sa,

Shiru jiddah tayi tana kallon gidan bayan ta fito, ba abinda ya canxa daga gidan yana nan yanda ta barshi, Alhamdulillah take nanatawa a xuciyarta yafi a qirga na murnar dawowar ta gida cikin qoshin lafiya tare da dimbin nasarori da ta samu.

Ji tayi an rungumeta, ko baa fada ba tasan twins din tane,

Welcome back mummy, we miss you,

Ta sunkuya tana kallonsa cikin tsananin tausayinsu yanda suka rungumeta sosai a jikinsu,

Mummy baxaki qara xuwa ki barmu ba ko? ta gyada kanta tana murmushi.

Da kyar suka barta suka nufi inda el'mustapha, sai tambayar sa suke baby waye, ya kyale su.

A falo suka yada zango, hajiya kam a gajiye ta nufi dakin baqi, duk falon ya cika da yan uwa cikin farin ciki.

Mummy baby waye a hannun daddy cewar aryan,

Arham yace mummy kice daddy ya ajiye ta ya dauke ni, tun daxu bai cirani sama ba nayi masa oyoyo.

Aryan yace mummy  wheel chair dinki yana dakin daddy, kixo ki xauna ni xan riqa tura ki.

Banda murmushi ba abinda jiddah keyi, falon kuwa sai dariyar yaran ake yi.

Banan tayi sallama ta shigo, da murna ta isa inda jiddah ta rungumeta tana mata sannu da xuwa,

Jiddah ta amsa sama sama,

Tace anty jiddah me kike so na kawo maki, nayi maki girki Kala Kala irin wadanda kike so.

'ki barshi anjima xanci.

Batare da tunanin komai ba banan ta juya tana kallon el'mustapha dake ta surutu da twins, ta saki ajiyar xuciya kamar wacce ta dade tana neman abu bata samu ba sai yau,

Tace yaya me xan kawo maka ka ci, kafin yayi magana jiddah tayi caraf tace ya qoshi ki tashi ki tafi idan yana buqata xan neme ki.

Banan ta tashi jiki a sanyaye ta nufi kitchen kamar xata dauki wani abin, leqen sa ta soma yi, Allah ya jarabceta da son el'mustapha ta kai har bata iya boye feelings dinta akansa, ina ma jiddah xata fahimce ta, ina Ma jiddah xata bata dama kamar yanda ta baiwa uwani saboda baxata taba nadamar aura mata el'mustapha ba, bata da niyar cutar da jiddah ko wani abu nata xama take so suyi na amana, amma jiddah taqi ta saurara mata kamar Ma ta tsaneta a yanxu.

Allah ka cire min son wannan bawan Allah idan ba alkhairi bane.

Yusrah ta tashi tana fadin, anty ikram xan tafi ina so na dauko su amira skul,

Tau shikenan nima xuwa anjima kadan xan tafi.

Jiddah Allah ya huce gajiya ya qara lafiyar jiki, kuma a kula da qanina yanda ya dace saboda yayi haquri cewar yusrah.

Murmushi kawai jiddah tayi suna wasa sosai tsakanin su,

Yusrah ta dubi el'mustapha tana fadin, xo muje ka taka min akwai maganar da xamuyi,

Yace ok sister, ya tashi yana ajiye baby akan sofa, twins suka mata caa suna kallonta sai yanxu suke ganin fuskarta da kyau.

She is beautiful daddy, who gv you?

Yace Allah, babyn mummy ne idan kuka taba ta tashi barci ba ruwana, mummy xata dake ku.

Suka juya suna kallon jiddah cikin mamaki, el'mustapha ya fita tare da yusrah.

Wai haka ne mummy? Ta gyada kai tana kallonsu,

Jiddah ta juya tana kallon kitchen tana lura kamar banan din bata fita ba,

'me kike yi a kitchen dinne banan?

'Anty jiddah ina hada abincin ne ta fada cikin rawar jiki, ta fito da sauri da warmers a hannunta ta nufi dinning tana shiryawa duk abinda take idanun jiddah akan ta, tana gamawa kuwa tace ta fita...

Wai me banan tayi maki ne jiddah, na lura tun a Germany kika takura mata cewar ikram.

Jiddah ta tunxuro baki, batayi magana ba,

Baki ji bane? Ta qara tambayarta fuskarta ba walwala, sosai jiddah tasan anty ikram bata wasa ko akan el'mustapha ne kuwa shi kansa yana tsoronta itace babba a gurin su duk yanda tace haka xaa yi musamman yanxu da take kamar uwa a gurin su.

Tace El'mustapha  take so...

'Anty ikram ta kalle ta da mamaki,

Tace ba dan na san ki nasan halin ki ba jiddah dana qaryataki, saboda banan xata so el'mustapha, ba ajin ta bane she knows, dan haka baxatayi wannan tunanin ba.

Idan har uwani xata iya son el'mustapha ta aure sa saboda me banan baxa ta so sa ba? Ita da take ganin xama kawai tayi a gidan bata da alaqa damu ba kamar uwani da muka taso tare ba.

Amma dai banan ta bani mamaki jiddah, sosai kuwa wannan simi simi nata ashe dai munafuka ce tunanin ta el'mustapha xai aure tane, mtsewwwww aikin banxa kada Ma ki wahalar da kanki wajen dorawa kanki damuwa dan el'mustapha baxai aure ta ba, ba abin da xaiyi da banan.
Chapter 54 · 0% Book details