← Book details El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 80

Sashe 62

El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har goma na dare bata dawo ba tana xaman jiran likita, dai dai wannan lokacin uwani taxo gidan, tana shiga falon idanunta na sauka akan dining, ta jefar da jakarta da gudu ta nufi dining da alama yunwa take ji sosai.

Shiru shiru el'mustapha baiji motsin jiddah ba tun yana wasa da airah da ta tashi tun daxu har ya soma gajiya da alama yarinyar kuka take son farawa yanda yaga tana mutsuniya.

Ya dauko ta ya fito da ita anan yaci karo da uwani xaune sai loda abinci take a cikinta,

Ita wannan yaushe taxo gidan? Xaiyi amfani da son da take masa da kuma tsoron anti ikram da take wajen ganin ya gyara rayuwarta.

Yaushe kika xo gidan waye ya baki ixinin ki xauna kici wannan abincin?

Ta xuba masa idanu bayan ta dago tana kallonsa, nan take taji gabanta ya fadi wani tsoron sa ya risketa lokaci daya,

Tace kayi haquri,

Ya tako a hankali har xuwa inda take, ya xauna yana fuskantarta cikin jijjiga airah,

Ke da nace sai gobe ya akayi kika dawo cikin wannan daren,

'Na kasa haquri ne nasan xaka maidani dakina kada kamin baqin ciki kasan ina son ka.

Yace kinyi sallah kuwa?

Tayi caraf tace ai banayi tun jiya bana yi, kwana hudu nake yi na ga.... yayi saurin katse ta,

Kin san meyasa nace kixo?

Ta girgixa kanta da sauri tana sud'e yatsun hannun ta,

Ai nasan kina sona ko uwani,

Sosai ma wlhy har mafarkin ka nake yi, kullum ina tunanin ka, ina son ka sosai dan Allah kayi haquri ka taimaka ka maidani dakina kada kamin baqin ciki, ko barci nake kai nake gani, idan naji muryar wani namiji kai nake tunawa, ko dan sanda nagani birgeni yake yi saboda kai.

Tau shikenan naji uwani idan kina so na yarda kina sona kuma kina so na maidaki dakin ki sai kin nutsu, duk wannan shashancin ki daina, girmama iyayen ki da duk wanda ya girmeki, banda maidawa mutum magana idan ana maki fada, banda tsokanar mutane  musamman maxa, ki riqa girmama duk wanda ya girmeki, wawancin da kike da rashin ji duk ki daina, ina ga kin xama mutum irin jiddah nan da wata biyu kacal na miki alqawari xan maidaki dakin ki.

Ta langabar da kanta, ai kasan ina son ka kome kake so xanyi, ni yanxu ba ruwana ma da kowa baxan qara kula kowa ba koda xagina aka yi, idan na nutsu xaka aure ni ko,

Ya gyada kansa yana kallonta,

Tace kuma xaka riqa kirana Uwanitilmusty ko?

Nan ma ya gyada kansa, tayi murmushi tana kallonsa,

Yace yanxu xamuje dake driver ya kaimu inda anty ikram dan baxan iya driving ba,

Xumbur ta miqe tana fiddo idanuwa,

'Wannan matar ai wallahi baxan je ba, ai itace ma ta koreni a gidannan saboda tana min baqin ciki da xamana a gidan mijina.

Yace ashe baki sona uwani tunda har bakyason abinda nake so, idan nace ina son abu baxaki iya yi min ba kenan, banda wannan ma yanxu na gama yi maki mgnr girmama wanda ya girmeki amma yaya ta kike cewa tana maki baqin ciki.

Kayi haquri sweet baxan qara ba, ai xanje wasa nake ma, kuma nasan dama bata min baqin ciki tana sona.

'Yauwa gurin ta xaki xauna duk yanda tayi dake haka xaki bi, idan kika nutsu kika gyaru ita ce ma xata maidaki dakin ki.

Allah ko?ta xauna cike da farin ciki dai dai lokacin jiddah ta shigo dauke da arham a kafadarta, duk suka juya suna kallonta, cak ta tsaya qofar falon tana kallonsu cikin faduwar gaba, haka taji kamar falon yana juyawa da ita, da kyar ta iya daga qafafunta ta qarasa cikin falon.

'Anty jiddah kin dawo, kinga nima na dawo ai yaya ne yace na dawo xai maidani dakina.

'Ko kallonta jiddah batayi ba ballantana tasa ran xata amsa ta,

Uwani xata yi magana el'mustapha yasa qafa ya bigi qafarta, ta juyo da sauri tana kallonsa, harararta yayi yana fadin tashi marar sirri.

Ta tashi da sauri, shima ya taso da airah, ya shimfide ta akan sofa kana ya nufi arham yana taba jikinsa, har lokacin akwai xafi.

Arham ya dube sa yana fadin, mummy ta kaini anyi min allura asibiti,

Ya shafa kansa yana fadin sorry, kaci abinci kasha magani yanxu xanxo maka da ice cream ka ji.

Arham ya gyada kai yana fadin harda Pringles daddy,

Yace to shikenan, ya dubi jiddah a hankali yace xamu fita da uwani.

Komai bata ce ba amma gabanta na tsananta bugawa, ya juya ya fita uwani tabi bayansa da jakarta tana waiwayen jiddah.

Wa nake gani kamar uwani cewar anty ikram tana kallonsa da mamaki a fuskarta,

Uwani ta qara matse jakarta tana boyewa bayan el'mustapha,

Ikram tace kada dai uwani bakije gida ba kika dawo?

El'mustapha yace ni na dawo da ita sister?

Meyasa ta tambaya tana kallonsa da tsananin mamaki,

Ya riqa hannun uwani ya xaunar da ita kana ya dubi ikram yana fadin, xo muyi magana sister.

Ikram tabi bayansa, suka fita ya koro mata bayanin komai da dalilinsa na son uwani ta xauna a gidan.

'Naji banqi maganar ka ba, duk wanda ya gyara d'an wani tamkar ya gyara nashi ne, kuma ga lada amma kasani el'mustapha ko ta nutsu ta shiryu baxaka taba auren uwani ba.

Ya sauke numfashi yana fadin na sani sister, kina son jiddah ta barni kenan yanxu haka ma fushi take tun da na kira nace uwani taxo, ko abinci bata ci ba, arham ma bashi da lfy da kanta ta kaishi asibiti duk saboda tana fushi uwani xata dawo.

Banga laifinta ba saboda abinda aka mata da farko bata ji dadi ba kuma baxata qara yarda da uwani ba ballantana ta dawo gidanta.

Nifa ba wai ina son maida uwani bane, kawai ina so nayi amfani da son da take min naga na shiryata da taimakon ke da take tsoro, amma idan nace na barta gida tare da jiddah kishi baxai saka jiddah taya ni gyaran uwani ba.

Uwani tayi mamakin ganin anty ikram ta dawo har tana murmushi, ta kira mai aikinta cewa ta shigar da uwani dakin su amira.

Uwani taji dadi anty ikram ta daina mata baqin ciki.

El'mustapha yayi masu sallama ya tafi, bai manta da saqon arham ba sai da ya saka driver ya biya dashi ya siya masa kafin su dawo gida.

A wannan lokacin tasha kuka sosai kamar ranta, idanunta sunyi jawur tana tuna wahala da tasha a baya saboda uwani amma el'mustapha keson maidata, wannan ke qara tada hankalin jiddah dan batasan plan din uwani na biyu akanta ba duk ranar da ta qara auren el'mustapha, ba wai son xamane bata yi da uwanin ba illah tsoron rashin imanin ta da take.

Kallonta el'mustapha yayi sai da gabansa na fadi saboda ganin yanda idanunta suka yi jawur,

Kuka kika yi jiddah, kukan me?

Tayi masa banxa, ya matso yana tambayar kinci abinci kuwa, nan ma shiru tayi masa,

Yana qoqarin xama kusa da ita, ta tashi xumbur ta dauki airah ta nufi dakin ta, ya bita da kallo har ta shige kafin ya maida kallonsa ga arham dake kwance yana lumshe idanunsa yana bude wa.

Mummy taci abinci kuwa?

No, tun daxu take kuka.

Xo ga ice cream din kasha sai muje mu kwanta dare yayi,

Daddy ni bana jin barci yanxu.

Yace aa, sha ice cream din tukunna kafin naxo, ya tashi ya nufi dakin jiddah, ga mamakinsa jiddah ta rufe qofar da key, hankalinsa ya qara tashi, jiddah bata taba rufe masa qofa ba, meyasa take tsiro da abubuwan da bata saba yi masa ba a xamantakewar auren su?

Saboda tana xargin ka da son abinda take gudu take ganin kamar cutar wane yanxu a gare ta, yaji xuciyar sa ta bashi amsa.

Ya soma buga qofar a hankali yana kiran sunan ta amma tayi masa biris.

Daddy ni baxan sha ice cream din ba sai gobe, idan nasha amai xanyi.

El'mustapha ya juya yana kallon yaron a sanyaye.

On your birthday, I wish you a year with loads of fun, excitement and beautiful memories. Happy birthday Girlfriend Baby Bello🎂🎂🎂🎂🎂🎂🎂

60

Pringles din fa?

El'mustapha ya tambaya yana kallonsa,

Baxan ci ba sai gobe,

Yace tor shikenan, ya riqa hannunsa suka nufi dakin sa,

Daddy yau tare xamu kwanta ne?

Ya gyada kai yana kallon yaron,

Ya xauna yana dialing number jiddah, tana fara ringing yaji an kashe gabaki daya, ya dafe kansa, arham ya kwanta jikinsa yana fadin,

Daddy baka sakamin kayan barci ba, kullum momy sai ta sakamin kafin na kwanta.

El'mustapha ya tashi cike da damuwa yace cire kayan kafin na dauko ma kayan barcin naka,

Bai jima da fita ba ya dawo yana fadin,

Meyasa baka cire kayan ba arham,

Daddy ni bana iya cirewa,  el'mustapha ya xauna yana cire masa kayan, ya saka masa na barci ya dubesa har yanxu jikinsa akwai xafi, suka kwanta.

*

'Washe garin ranar koda suka tashi jiddah ta gama komai na breakfast ta ajiye masu, ta shigewar ta dakin ta rufe., koda suka yi wanka suka fito ta gama komai amma bata falon.

Arham ya sami lfy amma ba qarfin jiki, ga maganin sa a falo amma bai san kansu ba, ya dauke sa suka yi breakfast, ya dawo yana buga qofar jiddah taqi budewa.

Yayi juyin duniya yana rarrashinta amma tayi masa banxa, tunanin sa jiddah bata ci abinci ba tun jiya kada wani abin yaxo ya same ta.

Ya kira anty ikram ya gayamata itama tayi kiran jiddah taqi dauka kuma taqi ta kashe wayar,

Cikin damuwa ya qara xuwa bakin qofar, kome kike ji jiddah ki fito kici abinci ba danni ba please,

'Ko alamar motsinta bai ji ba, yaji kamar ya bige qofar dakin.

Kusan goma na safe anty ikram taxo gidan, tayi magana tayi rarrashi ta dawo fada duk jiddah bata bude qofar ba, idan har suna son ta sun damu da rayuwarta saboda me xasu dawo da uwani.

Anya yarinyar nan tana da rai kuwa ko motsin ta bana ji cewar anti ikram tana kallon el'mustapha.
Chapter 62 · 0% Book details