← Book details El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 66 OF 80

Sashe 66

El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kai haba, chabdi, wallahi baka isa ba, da kasan kana sonta tun farko meyasa ka aure ni, ka tuna fa kaine na roqeni na aure ka saboda cin amanar da uwani tayi maka, na amince na aure ka saboda kyawawan halin ka da kuma haushin abinda uwani ta maka, amma meyasa xaka min haka, shekara biyu da watanni da auren mu xaka ce xaka min kishiya, kishiyar ma irin uwani ballagaza, me nayi maka yusuf?

Hankalinsa ya tashi sosai, ya matso kusa da ita da sauri ganin yanda take kuka,

Yace wallahi surayya idan nace maki bana son uwani na maki qarya, itace mace ta farko dana fara so, duk haukan ta haka nake son ta tunani watarana Allah xai shiryata idan muka yi aure, sai nagane daga baya uwani el'mustapha take so qanin matar yayana, ban gasgasta ba sai bayan ta aure sa, na shiga damuwa da tashin hankali sosai lokacin shine dalilin da yasa na aure ki saboda nima na baqantawa uwani, kuma ke da kanki kin gayamin yanda kuka yi dalilin haka har kuka sami sabani, amma wallahi ina son ki surry, ba dadin baki ba kuma ba ina gayamaki ne dan ki yarda dani ba, har acikin xuciyata a yanxu nafi son ki akan son da nayi wa uwani a baya, ni kawai dai ina so na aure tane.

Ta share hawayen ta, ta tashi tana fadin,

Shikenan baxan hana maka auren first love din ka ba, sai dai ni baxan xauna da kai ba, baxan xauna nayi kishi da wannan mahaukaciyar ba, indai har uwani ta iya cutar da anty jiddah saboda el'mustapha tabbas ni qona ni xatayi saboda kai, dama tana jin haushina tsab xata iya saka a kashe ni, baxan xauna ba sai ka sake ni.

Ya tashi ya riqo ta, haba surry idan kika tafi kika barni ya kike so nayi ne, idan ba kyason xama da uwani a gida daya ne wallahi xan ware maku pls surry,

Lallai yusuf ashe abin naka da gaske ne, Uwani kake so, wallahi baxan yarda ba ko ni ko ita.

Yace wallahi na xabe ki na gayamaki ke nake so surayya, ina jin tausayin uwani ne kowa baya sonta ya guje ta saboda halinta.

Ina ruwanka dole sai kai xaka aure ta, maxa nawa ne a duniya, bana son wannan maganar kada ka qara tada min xancen uwani a gidannan idan ba haka ba xan barshi.

Ya xauna yana fadin shikenan ba damuwa na amince.

Taja qaramin tsaki cike da haushi ta bar dakin.

Ranar barci sai dai barawo a idanunta, har mafarki tayi uwani ta biyo ta da wuqa xata kashe ta, ta xabura tana addua, yusuf ya bude idanuwansa yana kallonta,

Me ya faru surayya?

Wallahi mafarki nayi uwani tana bibiyata da wuqa xata kashe ni,

Yayi shiru yana kallonta ta cigaba da fadin wallahi uwani annobace baxaka gane ba yusuf, qawatace na fika sanin wacece ita.

Yace Allah ya kyauta ya gyara kwanciyar sa.

Ta koma ta kwanta cike da tunani iri iri, wani mafarkin tayi wannan karon uwani ta biyo ta da qatuwar tabarya tana faduwa ta fara dukanta da ita har sai da ta daina numfashi.

A xabure ta tashi tana kyalla ihu, yusuf Ma ya tashi a firgice yana kallonta,

Ta fashe da kuka tana kiran, ina wallahi uwani baxata shigo gidan nan ba, tsab xata kashe ni, tun a yanxu ta hanamin sukuni tana bibiyata a barcina.

Yace kin dai saka abin a xuciyarki ne, kiyi addua ki kwanta.

'Washe gari ya nufi jiddah da mgnr,

Kallon sa tayi da murmushi a fuskarta,

Baxan ce komai ba a yanxu  yusuf sanda na nema mata auren ibrahim akace na so kaina, ina mata baqin ciki da komawar ta dakin el'mustapha, ni kuma bana daya daga cikin masu yiwa uwani baqin ciki kamar yanda take fada, ba abinda xance illah addua Allah ya xaba mata mafi alkhairi.

Yace aa anty jiddah kinsan yanda xaki taimaka min, yayana bashi da matsala kamar yayar mijinki, yanxu da ta furta baa yi tabbas yayana xai dauki maganar tane saboda yana ganin tafi shi sanin wacece uwani tunda ta auri qanin ta dan haka baxai amince da ni na aure ta ba.

Idan ta wannan ne duk mai sauqi ce yusuf xan Ma el'mustapha magana ya yi wa anty ikram magana, amma surry tasan da maganar kuwa.

Yace wlhy tasani kuma bata amince ba, ina sha'awar auren uwani ne saboda ina tausayinta a yanxu amma nafi son surayya da uwani ina fada maki gsky ne ba dan cin fuska ba.

Allah sarki surry, yarinya mai hankali xaa hada ta kishi da mahaukaciya, Allah ya basu xaman lafiya.

Yace amin...

Baban twins, yusuf yana neman alfarma ka saka bakin ka a neman auren sa da uwani... Jiddah ta fada lokacin da take qoqarin xama a kusa da shi.

Kallon ta yayi bayan ya cire watch din dake hannunsa, ya tashi yana fadin.

Babu wani hannuna da xan qara sakawa a al'amarin uwani again kafin axo ana kuka da qananun maganganu cewar ina son uwani.

Murmushi tayi tana kallon sa bayan ta tashi,

Haba Musty na, ina ji ko kai xaka iya bada auren uwani a yanxu, mgn kawai muke so kama anty ikram ta saka baki a ciki.

Believe me jiddah ba wani baki da xan saka a lamarinta, na cire hannuna akan komai nata, amma na amince maki ke kije da kanki ki mata magana

Ta saka hannunta ta xagayo dasu a qugunsa tana kallonsa cikin langabar da kanta.

Fushi kayi el'mustapha saboda na nuna kishina a soyayyar ka akan abinda ni kuma xai cutar dani.

Yace ba fushi nayi ba jiddah,

Idan ba fushi kayi ba meyasa xaka ce ka cire hannunka akan komai nata.,

Saboda jiddana ta yarda dani, ta yarda farin cikin ta kawai nake so,

Tace ba wani ni na gane kana kishin uwani ne saboda ta sami wani mijin.

'Wannan yarinyar ko.... yaja dogon hancinta yana fadin watarana sai nayi kullin kubura dake.

Tayi dariya tana qanqameshi a jikinta.

A gurguje pls😏

Bayan an gama solving komai aka tunkari abba da maganar.

Sanda uwani taga baqi sunxo inda abbanta har da el'mustapha ta fara tsalle tana murna, xaa fitar da ita daga gidan ta huta da axabar da ake mata, dama tasan wannan baturen yana son ta dole ne ma yaxo neman auren ta, ashe shiyasa jiya ta ganshi a mafarkinta bawan Allah ashe auren ta xai xo nema.

Su el'mustapha na barin gidan taje inda abbanta tun bai dawo rakiyar su ba ballantana ta jira har a kirata,

'Abba wannan baturen suke magana kenan,dama nasan sona yake ashe ba baqin ciki yake min ba da ya rabani da El..... bata qarasa ba ya wanke fuskar ta da mari.

'Ashe baki da kunya uwani.

Nan da nan ta shiga cikin nutsuwar ta, ta tuna yanxu fa ba irin da bane da ake kyaleta kuskure daya tayi jikinta sai ya gayamata, da sauri ta soma bashi haquri.

'Ko da taji yana fadawa hajiya yusuf ne xai aure ta harda kukan ta, bashi take so ba abokin el'mustapha take so, ita baxata aure sa ba.

'Abba yace to shikenan xan kira el'mustapha in basu haquri su haqura dama jiya Malam guzuma yayi min mgnr yana so ya aure ki tunda ya dauko hanyar shiryaki.

Ta ware idanunta sosai tana kallonsa, Malam guzuma wannan mugun malamin fa mai dukanta da abba ya hada ta dashi, ai da ta aure sa gwanda ta mutu,

'Abba kayi haquri kada ka kira ina son yusuf dina, shine masoyina na gaske dan Allah abba.......

Yusuf kuwa tunda yaga ya sami uwani hankalinsa ya dan kwanta, yana xuwa gida ya rungume surry yana fadin ya biya masu umara xasu je tare, sosai tayi murna sai kiss take ta xuba mashi...

Yace kuma xan canxa maki wannan gidan, ke xan saka a wancan sabon.

Tayi tsalle ta dira daga jikinsa tana kallonsa,

Bangane ba duk wannan kyauta haka ta mecece, meyasa xaka canxa min gida, shi wannan fa.

Gabansa ya fadi, yace aa da wancan da wannan duk nawa ne surry, xamu koma wancan ne na saka yan haya anan kingane.

Sai a lokacin ta saki fuskarta.

*

Yau ya akayi haka ka dawo da wuri baban twins,

Ya soma qoqarin cire rigar jikinsa yana fadin, tashi ki shirya, ki shirya airah ni xan ma su twins wanka na shirya su fita xamuyi,

Ta tashi da airah a jikinta tana fadin ai nayi masu wanka sai idan wasu kaya xaka canxa masu.

Yace to shikenan jiddatulmusty, bara na shiryasu, ya nufi dakin su suka nishi da gudu suna tsalle.

Daddy ina xamu je?

Daddy xamu je shan ice cream ne?

Duk bai amsa su ba, ya jima sosai kafin ya gama shirin su, sunyi kyau sosai har ya dauke su pic,

Daddy muje cikin garden kayi mana mai kyau, bama son dakin mu.

Yace tor shikenan wait at the falo kafin na gama nawa shirin.

Suka fito da gudu shi kuma ya nufi nashi dakin, bai jima ba ya fito cikin tsadaddiyar shaddar sa, yayi matuqar kyau sosai sai kace ango, inama uwani xata ganshi😉.

Suka nufi garden sai pics suke dauka.



har lokacin jiddah bata fito ba.

Meya tsaida jiddah haka, el'mustapha ya tambaya lokacin da yake qoqarin shiga dakin.

Jiddah taja tsaki, kasan shirin wannan yarinyar aiki ne.

El'mustapha ya qarasa yana fadin sai kukan tsiya tun daxu muryanta kadai ake ji a gidannan, ki xauna ki bata tasha da kyau kar muje gidan mutane ta nuna halinta.

Jiddah ta xauna da kyau tana kallonsa bayan ta sakawa airah mamma a baki.

'Wannan kwalliya haka el'mustapha duk ta mecece, wai ina xamu je?

Ya tashi ya qarasa bakin mirror yana gyara xaman hularsa,

'Ashe ko dana ji twins na fadin daddy is looking beautiful dai gaskiya suka fada min tunda gashi jiddah ta yaba.

Ni bance kayi kyau ba fa, kasan na fika kyau ai.

Wasa kike jiddah, ai inaji airah kawai xakice kin fi kyau na yarda ke ita ma din ban yarda ba.

Ba wani, nasan na fika kyau.

Dariya yayi ya juyo yana kallonta, El'mustapha yafi jiddah kyau ta sani kishi ke hana mata fadin gsky.

Ta tunxuro baki batayi magana ba.
Chapter 66 · 0% Book details