← Book details El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 80

Sashe 41

El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tace oh ashe yaxo, sai kuma ta dubi yanayin el'mustapha sai Ma qoqarin rufe laptop din yake, ta qara kallonsa gabansa na tsananta bugawa.

Tace me ya same ka el'mustapha, meyasa kake rufe laptop din bayan kace aiki kake da shi.

Anjima xan qarasa, ya ajiye ta gefe yana qoqarin kwantawa a kusa da ita.

Tace ko ka damu da baqon banan ne, meyasa ka damu da yawa haka, kada kace dai kana son banan ne.....

Gabansa ya tsananta bugawa ya tashi da sauri yana kallonta,

Ni jiddah.... ni kuma kike xargi akan banan saboda me xan damu da baqon ta?

Tace nasani ne el'mustapha, tun asibiti ina lura da yanayinka daga lokacin da ka gane banan tana tare da Islam, yanda ka fita yanxu ba haka ka dawo ba, daga yanayin yanda kake mgnr banan tana da baqo mai hankali xai gane.

Yaja numfashi jikinsa na rawa xai yi magana tayi saurin tsaidashi da hannunta.

Ba sai kayi min bayani ba, nasan dole xaka buqaci mace mai lafiya ba Irina ba, kuma nasan komai daren dadewa dole xaka qara aure, amma yaushe ka fara son banan el'mustapha?

You are not serious jiddah, baki san me kike yi ba, something is wrong with your brain, bana son wannan maganar kwata kwata kuma kada ki taba tunanin ina son banan I don't.

Batayi magana ba ta kwanta jikin pillow tana kuka sosai,

Jikinsa yayi sanyi yaji hankalinsa ya tashi, shi kam baya son wanna kukan na jiddah ko yaya ne,

Ya hau gadon kacokan ya rigota,

Wallahi jiddah babu wata yarinya da nake so a yanxu bayan ke, bana son banan reaction dina akanta ba shi xai saka ki yanke min hukunci akan ina sonta ba, yaushe kika fara xargina Hakan jiddah, Wallahi bana son ta kuma ban taba tunanin qara aure ba saboda kin nakasa jiddah, cikin kowane hali kike ina son ki, xan kasance dake a hakan har qarshen rayuwa ta ki yarda dani jiddah....

Ta xame jikinta a hankali daga garesa, Allah yasa abinda el'mustapha ke fadi har a xuciyarsa ne baxata taba yarda ya auri banan ba, idan ma auren xaiyi ta fiso ya auro wata bare yanda ko ta cuce ta baxata damu ba kamar yanda uwani tayi mata, amma me el'mustapha xaiyi da banan, kai baima isa ba wlhy ba macen da xai aura.....

Wallahi baka isa ba el'mustapha, babu macen da xaka aura a gidannan ba banan ba kowace iri ce kuwa idan kana da wannan niyar is better ka kunce ta a yanxu.

Yanda take maganar cikin seriousness ya saka shi dariya harda tafa hannayensa.

Nagane ba komai ke damun jiddah ba sai rigimarta bnda hakan taya xaki hadani da banan for goodness sake, ki daina sako min ita a xance just relax kwanta ki huta.

Ta tunxuro baki tana kallonsa,

'Na dai gayama inma akwai wannan niyar ta aure a xuciyarka ka cire ta na dawo jiddana as before, indai akan kan baxan qara haqura da wata mace ta rabe ka ba, is better ka shirya xama da jiddah a duk yanda take kamar yanda kace as before cikin kowane hali you will be with me.

Yace insha Allah jiddatulmusty, ya sumbace ta yana murmushi itama murmushin take tana kallonsa.

Comment an Vote😀
EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association
Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞

45

Yaja numfashi a hankali hade da sarqe hannuwanta da nasa yana murxawa.

Kallon sa tayi,

Mama bata xo asibiti ta duba ni ba, kuma bata kirani a waya ba sannan ba wanda na ji yace mama tana gaidani, Allah ya sa ba laifi nayi mata ba el'mustapha.

Gabansa ya tsanan ta bugawa ya juyo yana kallon ta a hankali, yama rasa me xai ce mata, yayi shiru yana kallonta.

Ko tana fushi dani ne, nidai ban san nayi mata wani laifi ba.

Mama bata fushi dake jiddah, saboda me Ma xatayi? Ita ma jikin nata ba sauqi shiyasa kika ga bata xo ba amma kullum naje sai tace a gaidaki,

Baya son gayamata gsky saboda halin da take ciki ya fiso sai ta haihu tukunna.

Tace to kabani ita a waya mu gaisa, ko ka kaini wajen ta mana.

A hakan xan dauke ki na kaiki, kin fiye sakawa ranki damuwa ita mama da kanta naji tana maganar xata xo idan jikin yayi sauqi.

Allah ya bata lafiya,

Amin kawai yace a hankali ya koma ya kwanta, mgnr mama da tayi duk ta tada masa wata kewa ta mahafiyarsa, ya soma yaqi da xuciyarsa na ganin yayi mata addua batare da wata alama ta damuwa ta bayyana a fuskar sa ba.

Ta sa hannu tana Jan yatsun qafarsa a sanyaye.

*

Tun da Uwani ta sami labarin kowa tayi sanyi, babu komai a tare da ita sai tsananin nadama sannan duk a cikinsu tafi tausayawa ladidi ina Ma tana da wata hanya da xata taimaka mata na ganin ta fitar da ladidi ko da ita xata dauwama a prison din.

Ta share hawayenta tana kallon ladidi.

Anti ladidi dan Allah ki yafe min abubuwan da nayi maki a nan, nikam ina ji qarshe na yaxo mutuwa xanyi, baxan taba yafewa kaina ba domin na cutar da rayuwata.

Ladidi ta dafa ta tana fadin, baxaki mutu ba uwani sai lokacin ki yayi kuma kowane mutum da kike gani a rayuwa yana kuskure kuma ya nemi gafara a yafe masa, kada ki karaya tun yanxu ki fara istigfari kuma idan Allah yasa kin fita daga gidannan kije ki nemi gafarar iyayenki da jiddah.

To wai ke ina jamcy ne cewar aj tana kallonta,

Nima ban sani ba kuma bani da labarin ta tun ranar da mukayi waya tace an kama saurayinta kuma inaji itama din xasu kama ta ne tunda neman ta suke a yanda ta gaya min.

Runkes tace amma fa ta cutar dake ba qawar arxiki bace surry ce tafi dacewa dake domin itace mai gayamaki gsky.

Aj ta tabe bakinta bayan ta gyara kwanciyarta nifa duk wannan muqu muqun da kike na tuban muxuru baya tasiri a gareni idan kika cigaba da min iskanci a gidannan ubanki xanci na gyara ki bana daukar raini ko kadan kuma bana so a rainani, idan kina so mu xauna lfy dake ki kama kanki da bakinki ga maidamin magana.

Insha Allah anti aj xan kiyaye baxan qara maki iskanci ba.

Kimayi din kigani, taja tsaki.

Runkes ma ta tashi tana yan waqoqinta tana gyara gurin da xata kwanta.

*

'Washe garin ranar suna xaune suna cin abincin da suka karbo amma banda uwani ta takure guri daya sai tunani take,

Ita fa tun da take a rayuwa tana jin bata taba abinda iyayen ta suka ji dadi suka yaba ba amma tana ganin yanda suke sanyawa jiddah albarka, taya xata gyara rayuwarta a sota kamar yanda ake son jiddah?

Aj ta dube ta rai a bace, wai ke uban waye ya saka ki a damuwar ne da xaki xo kina mana kuka anan?

Xaki matso kici abincin ne ko sai na tattakaki, wlhy sai in cinyeshi gabaki daya ba damuwa ta bane, muguwa mai manta alheri, matso nan ta fada cikin tsawa.

Uwani ta matsa da sauri hade da tsoma hannunta cikin plate din, jikinta na rawa take cusa shinkafa a bakinta babu ko taste ballantana taji dadin ta abaki.

Bata taba tunanin akwai ranar da xata iya cin wannan abinci ba, dama haka rayuwa take watarana da dadi watarana ba dadi.

Suna haka wani police yaxo ya bude qofar yana kiran waye Aisha Adam anan?

Uwani tayi xuru tana kallonsa gabanta na tsananta faduwa, jikinta ya dauki rawa.

Nace waye Aisha Adam anan dakin kun min shiru.

Nice.... Uwani ta fada tana hawaye.

Xo.. Kin wani tsare ni da ido sai kace mayya, kada ki batamin lokaci.

Ta tashi tana kallonsu cikin wani irin tashin hankali, shi kenan qarshen ta yaxo, ta hade hannuwanta guri daya tamkar mai neman gafara a gurin su sai dai ta kasa furta kowace kalma a bakinta saboda tsananin tsoro da fargaba.

Ta soma tafiya a hankali idanunta akan na ladidi, xaman da suka yi da ita taji tana son ta tana matuqar tausayinta,

Haka ya cusa qeyarta gaba suka fito.

Tayi mamakin ganinsa a wannan lokacin, gabanta ya tsananta bugawa ta xubawa kyakkyawar fuskarsa idanuwa kamar xata hadiye sa dan so.

Yana tsaye yana rubutu a wani littafi da bata san kona menene ba, duk da yaji alamun tahowarsu hakan bai sa ya dago ya dube su ba.

Fuskar nan tasa ba walwala sanyi da farin glass,

Sir gata na xo da ita....

Bai dubi inda take ba ballantana ya san wane hali take ciki.

Yace ina inspecta kabir,

Sir gani,

Xo nan akwai wani case da nagani ranar a wannan littafin, yaron da aka kama yayiwa yarinya fyade ya akayi aka sake shi bada sani na ba, waye ya bada izinin hakan?

Sorry sir, amma... Amma?

Amma me? Ya katse sa bayan ya kafe sa da idanuwansa.

Kun saki yaron ne ya tafi a banxa bayan ya cutar da yarinya, kada kuce min kun karbi cin hanci ne?

Kabir yaji gurin na juya masa yasan waye el'mustapha Sam baya wasa da aikinsa haka kuma duk wanda ya kama da cin amana a gurin korar sa yake yi ba ruwansa, ya rikice yana rantse rantse.

Sir ni bansan komai ba akai, bani ne on duty ba ranar, ka duba kagani nima koda naxo an sake shi.

Waye da duty ranar?

Inspecta Ayuba  ne, ya qara nuna masa jikinsa na rawa,

Idan yaxo ya same ni office ina neman sa.

Ya soma tafiya a hankali batare da ya kalli inda uwani take tsaye ba.

Sir wannan fa a maida ta ne?

Ku barta idan taga dama ta kwana a gurin.

Ta bisa da kallo har sanda ya isa motar sa,

Kinji dadi oga yace abarki ki tafi, sai ki kama hanya in kuma anan xaki kwana ne sai naxo na tayaki kwana.

Ta dubesa tana xabga masa harara tamkar idanunta xasu fado, taja dogon tsaki bayan ta soma tafiya jikin ta ba kwari.
Chapter 41 · 0% Book details