← Book details El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 80

Sashe 26

El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba komai anti jiddah na amince da duk mijin da kika xaba min, ni mai yi maki biyayyace.

Sosai jiddah taji dadi, banan kuwa ranar tasha kuka kamar me.

Bayan kwana biyu, twins sunje islamiya tare da banan, ba kowa a gidan sai jiddah kadai xaune a falo,

Wayar ta, ta soma ringing, tayi mamakin ganin call din uwani a lokacin, kamar baxata dauka ba sai kuma tayi receiving,

'Dan Allah anty jiddah kixo ki taimakeni, gani a hanya na kasa driving baxan iya dawowa gida ba saboda banda lfy dan Allah kixo ki taimakeni.

Kina wajen ina ne na aiko maki driver kinsan condition dina ai.

'Dan Allah karki aikoshi anty jiddah kixo da kanki kuma kada kixo da kowa saboda duka jikina ya lalace da jini, ashe ina da ciki ne ni ban sani ba, dan Allah kixo yanxu anti jiddah kada na mutu sai ta fashe da kuka.

Jiddah ta rude, yaushe uwani tayi ciki bata da labari, el'mustapha ya munafunceta yanda yake nuna mata babu komai tsakaninsa da uwani.

Ko wane hali uwanin take ciki, abin na buqatar sirri basai taje da wani namiji ba dan batasan halin da xata isko uwanin ba, amma ita kadai baxata iya taimaka mata ba, ta kira uwani a waya,

Kinsan ni kadai baxan iya taimaka maki ba uwani ko naxo da Inna ne,

Aa anti jiddah bana son kowa yasan halin dana ke ciki ballantana mai aiki, ga wata mata anan tare dani bataso tabar motar ta da yaranta a gurin ne da itace xata maidoni gida,

Kina wajen ina ne?

Da kyar uwani tayi mata bayani.

Jiddah ta dauki hijabin ta da key din motarta, batare da tunanin komai ba ta shiga motar ta.

Taxo fita ne wani security ya tsaidata,

Madam ke kadai xaki fita ne, oga yace kada abarki kije ko ina batare da ko daya daga cikin mu ba.

Tace karka damu, its urgent yanxu xan dawo, kafin yayi magana ta ja motar da qarfi ta fita daga gidan.

*

EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association
Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞

Dis page is for you my dear Maryam kaumi, one among d best, Hbd dear.

34

Tafiya tayi mai nisa, a xuciyarta tana tunani kome yaxo da uwani gurin.

Tun daga nesa ta hango motar uwani a gefen titi, ta rage gudun motar tana observing wani abu,

A waya uwani tace akwai wata mata tare da ita da ya'yanta, to ina suka shiga?

Tayi parking nesa da motar uwani, ta cikin glass din ta tsurawa motar uwani ido har ta hango kamar wasu maza a cikin motar, gabanta ya fadi, kada dai uwani ta kirata ne domin ta cutar da ita, dama bata kashe motar ba, ta soma qoqarin juyawa ta bar gurin, abinda bata sani ba tayoyin motar, qusoshin da aka xuba akan titin duk sun fuda motar, ta fito cikin motar da sauri tana kallon motar, sai a lokacin tsoro ya xiyarce ta mai tsanani musamman da ta gane plan ne aka hada mata, ta juya da sauri tana qoqarin gudu amma baxata iya ba saboda cikin da ke jikinta,

Kurma na ganin haka ya fito da gudu daga inda yake boye cikin grass, ba zato jiddah taji saukar duka a qafafunta wanda yayi sanadiyar faduwar ta gurin a sume.

Su uwani suka qaraso da saurinsu tare da wasu maxan abokan aikin kurma, kurma ya yarda qaton qarfen dake hannunsa wanda shine ya bugawa jiddah a qafafu.

Ai na gayamaki idan tayi qoqarin guduwa sai na harbe qafafunta ko na ciresu gabaki daya, inda na bige ta a qafar ina sa rai baxata qara tafiya ba ballantana tayi qoqarin guduwa.

Uwani ta xare idanu cikin tsoro, wayyo Allah anti jiddah baxata qara tafiya ba kake nufi, amma ai munyi magana da kai aciki ba cutarwa.

Saboda kada na cuce tane ya saka ban cire qafafun gabaki daya ba, kuma xan iya babu imani a xuciyata ko kadan ki tambayesu, nine na kashe mahaifina saboda ya kamani ina yiwa qanwata fyade, tunda na kashe mahaifina da hannuna uban kowa Ma xan iya kashewa kuma kowanene akace na kashe sai na kashe shi nake samun nutsuwa,

Uwani ta nufi inda jiddah ke kwance a sume, ta rungumota sosai a jikinta, taji wani tausayinta ya kamata wanda yake sanyata dana sani a yanxu, idan ita ce jiddah baxata taba mata haka ba.

Kurma ya dubi daya daga cikinsu,

Goga dauki matar nan saka mana ita a motar mu kada musa wasa axo a riske mu, ke kuma sati daya kacal na baki ki kawo min kudi na idan kika qi wallahi summa tallahi sai na kashe wannan matar kuma naxo har gidan na kashe ki sai dai nima a kasheni, bana wasa da kudina, ya juya ya fice sauran suka bi bayansa yayin da goga ya dauki jiddah yabi bayansu.

Jiki a sanyaye uwani ta tashi ta nufi motar ta, tana kallo suka sanya jiddah a motar su suka keta cikin dajin, gidansu yana can ciki sosai.

Wata xuciyar ta soma xuga ta, saboda me xata damu ai abin farin cikin tane jiddah ta xama nakasashiya baxata taba moruwa ba kuma el'mustapha baxai taba xama da ita a hakan ba, dole xai dawo mata tunda itace mai lafiya, baxata damu ba tunda har sun furta baxasu kashe taba idan ta kawo kudin, xatayi qoqari ta kawo saboda bata son a kashe jiddah tana so abarta da ranta yanda xata riqa ganinta da el'mustapha tana juyashi kamar yanda ake juya waina, ta saki murmushi,

Wani tunani tayi ta isa motar jiddah ta bude, wayar ta ta ciro, ta sami dutse tayi mata ratsa ratsa, ta cire sim din ta yarda har wayar ba kana ta shiga motar ta tabar gurin da sauri.

Tafiya sukayi mai nisa acikin dajin kafin su iso gidan nasu, gida mai kyau baxaka taba tunanin yan iska ke xaune a cikin sa.

Goga dauko wannan matar sharp sharp,

Goga ya dauki jiddah
Ya shiga da ita gidan, wani daki suka kaita suka kwantar da ita, kurma ya dauko qaton bucket cike da ruwa ya watsa mata batare da tausayi ba.

Har lokacin bata motsa ba, ya sake debowa ya watsa mata, ta saki ajiyar xuciya, numfashin ta na dawowa a hankali.

Abinda ya faru ke dawo mata akai, sanda kurma ya bigi qafarta wani irin radadi da axaba da taji tunda take a rayuwa bata taba jin irin sa ba, ta bude idanuwanta da sauri tana kallon dakin da take, ambaton Allah take a xuciyarta, ta soma qoqarin tashi amma me qafar ta riqe bata iya motsa ta ko kadan,

Meke nan? Ta maida dubanta ga qafar cikin rudani, meke faruwa, meyasa na kasa motsa kafar, meya sami qafar, innalillahi wa Inna ilaihir raji'un, ta saki wani kuka sosai gwani ban tausayi.

Jiddatulmusty 😒

Uwani tana xuwa gida ta shigewarta abinta kada Ma a xargeta akan batan jiddah,

Ita yanxu abinda ke damunta yanda xata sami million biyu, ta sani idan tayi wasa tsab kurma xai iya kashe su ita da jiddah, ta ciro wayarta ta kira jamcy,

Tayi ta ringing bata dauka ba, haka ta sake gwada kira, gab da xata tsinke ta dauka, abinda taji jamcy na furtawa a bakinta yayi tsananin rudata,

Uwani ina cikin wani hali, guy din dana biyo muka xo ashe yana dauke da cocaine, sun kama shi sun tafi dashi gani bansan inda xan nufa ba nima nemana suke.

Uwani ta tsinke wayar yayin da dakin ke juyawa da ita, har wani duhu take gani a idanuwanta.

Banan suna dawowa makaranta taje da yaran ta cire masu uniform na islamiya, ta shiryasu cikin kayan su na gida.

'kuje ku gaida momy kafin naxo, suka nufi sashen jiddah da gudu.

Mummy... Mummy we are back,

Dakin ta suka nufa bata nan, kitchen bata nan, toilet, har sashen el'mustapha suke bata nan suka sake komawa dakinta, aryan ya kwanta saman gadonta yana kuka,

Momy ta tafi ta barshi ita da daddy yau baxai ci abinci ba.

Arham bai damu ba, keken sa ya dauko ya soma yawo da ita a tsakiyar dakin yana wasa tare da bindiga a hannunsa na yara.

Uwani na jin kukan aryan ta qara lafewa tana xaginsa a xuciyarta, yau babu momy sai dai kaci ubanka, kaima daqiqi yanda mamanka ke cemin daqiqiya, kuma daqiqai ne wawaye kawai.

Tun da banan ta nufa falon take jin kukan aryan ta qarasa dakin da sauri sukayi kicibis da keken arham har ya taka mata qafa,

Ta dauke qafar da sauri tana yatsina fuska, arham ya soma dariyarta.

Meyasa aryan ke kuka, ina anti jiddah?

Bata nan shine yake kuka?

Bata nan, banan ta maimaita cike da mamaki, ta juya ta fita xuwa harabar gidan, tabbas bata nan dan babu alamar motarta a gidan,

To ina anti jiddah xataje da magrib haka, ita bata da waya ballantana ta kira ta taji, tana tsaye gurin yaran suka fito, haka ta riqa jin faduwar gaba, taji bata jin dadin jikinta babu nutsuwa a tare da ita wanda bata san dalili ba tunda ba yanxu bane jiddah ta fara fita.

Ta dauki aryan dake kuka, kukan sa na qara rikitata tana jin ba daidai ba a jikinta, bata da nutsuwar da xataje tayi sallah, sai ta tsinci kanta tana xubar da hawaye.

Asp Bello yaxo alwallah ya ganta tsaye da aryan yana kuka, ya tambayi dalili ta gayamasa.

Yace tun daxu ta fita gashi bata dawo ba kada oga ya dawo bata nan, sai da akace wani a cikin mu ya bita tace nan ne kusa urgent aka kirata baxata jima ba.

Shiru kawai banan tayi, shima ya juya, ta Goya aryan bayanta tana jijjigashi sai safa da marwa take a harabar gidan, arham na rakube gindin wata flower.

Suna haka aka wangale gate din duk suka juya suna kallo.

Motocin el'mustapha ne suka shigo, gabanta ya tsananta faduwa, aryan ya soma qoqarin saukowa ba musu ta sake shi daga shi har arham suka nufi motar mahaifinsu da gudu suna murnar dawowarsa.

Daddy is back...
Chapter 26 · 0% Book details