← Book details El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 80

Sashe 14

El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Shikenan ta faru ta qare dama tasan el'mustapha baxai so ta ba, ya karbi auren ne domin ya wulaqantata, ai kuwa kansa yayi mawa saboda takardar jiddah xata bawa ita acewar ta tace, dan wlhy bai isa ya sakeni a farkon daren aure na ba.

Ta dauki takardar da sauri ta sakata cikin wardrobe din ta, baxan nuna masa na karanta takardar ba dan Ma karnaga sakin, jiddah xan bamawa ko saki nawa ne ya xamto itace yayi Ma bani ba, sai inga yanda xaiyi Allah yasa saki uku ne aciki ta tafi ta barmin shi har abada inga qarshen soyayya, ingani idan baxasu iya rayuwa ba kamar yanda suke fada.

Da wannan tunanin uwani ta kwanta barci, mafarkinta a ranar duk cike yake da el'mustapha, gani kawai take suna ta xuba soyayya ita dashi.

Jiddah kuwa a ranar ta kasa barci, tayi kuka harta gode Allah, once in life el'mustapha din ta kwance da wata macen ba ita ba, tunani iri iri, ganin bata da mafita ya sakata shiga toilet ta dauro alwallah taxo ta fara sallah.

El'mustapha kuwa bashi da damuwa illah ta kewar jiddah sa, rigar barcinta ya sakawa pillow ya rungume, barcinsa yake hankalinsa a kwance batare da tunanin komai ba.

'Washe gari jiddah ce a kitchen tare da banan suna hada breakfast suna hira abinsu.

'Anty kinga har yanxu kaka bata xo dubiya ta ba, ta dade sosai wannan karon kuma ina so na ganta.

'kibari idan kukayi hutu bata xo ba sai kije, ai ba abin damuwa bane banan, meyiwuwa wasu hidimomi suka yi mata yawa.

'hakane anty, amma a makaranta an fara mana maganar kudin waec da neco.

'eyyeh ashe Banan an xama yan mata, na manta ai wannan shekarar kike gamawa,  kice su arham sun kai ga babbar anti.

Murmushi banan tayi tana kallonta,
'Anty ai xaki sakani University nima kamar anti uwani.

Me xai hana banan, inaso kiyi karatu, kinga ni banyi ba iyakar secondary ne kawai dani, kuma bayan nayi aure banyi qoqarin shiga ba kasancewar el'mustapha baya so, Uwani kuma kinga saboda bata da aure ne har kika ga ta cigaba kuma yanxu xata cigaba tunda kinga tana kai ya aure ta, dan haka kema ina so kiyi karatu koda kin sami mijin aure ki cigaba, ilimi yana da matuqar muhimmanci ga 'ya mace, ina so watarana kaka tayi alfahari da bokon ki.

Banan tayi dariya tana kallon jiddah cikin tsananin qaunarta,

'Anty jiddah rayuwarki daban ce, halinki mai kyau ne kuma kina da kirki, shiyasa nake matuqar sonki, mutanen gidannan Ma basu da magana sai ta alherin ki, baxan iya cutar dake ko cutar da jinin ki ba shiyasa kika ga ina matuqar qaunar yan biyu saboda mamansu bata kyamace ni ta soni da xuciya daya.

Jiddah ta wanke hannuwanta a sink, kafin ta juyo tana kallon Banan,

Nagode da kulawar ki sosai akan twins, Allah xai saka miki, taimaka ki kwashe kayan ki jera a dining, ni xanje wanka.

Cikin shirinsa na uniform ya fito, suna hada ido da jiddah ya sakar mata murmushi,

'Uwargidan el'mustapha, amaryar el'mustapha, mata kadai a xuciyar el'mustapha da fatar kin tashi cikin qoshin lafiya,

Murmushi tayi tana kallonsa,
'Good morning my cwt, angon uwani.

Bai wara mgn ba ya qarasa dining yana duba abubuwan da ta hada masa,

Xama yayi yana fadin, all dis for me jiddana, gashi kuma am late ina sauri.

Ta qaraso tana fadin, all for you an your bride, ka jirata ta fito mana.

Hannu yasa ya mintsineta, ya jawota kacokan ya dorata akan qafafunsa,

Bari na duba ki matata nagani wai akwai sona kuwa a xuciyarki, jiya kin barni cikin kewa da kyar na sami barci, kafin tayi magana ya hada bakinsa da nata.

Suna haka uwani ta fito cikin shirinta, ganin su a haka ba qaramin tada hankalinta yayi ba, haka taji falon na juya mata, ga wani uban kishi daya danne mata qirji.

Ai wallahi sai dai na katse maku abinda kuke amma baxan koma ciki ba, ta qarasa dining da sauri.

El'mustapha sarai ya ganta amma jiddah bata ganta ba kasancewar bayanta ke fuskantar uwani,

Tana isa dining ta daga murya sosai yanda xasu ji ta,

'Anty jiddah sannu da aiki,

Sosai jiddah ta jiyo ta sai dai batayi yunqurin barin jikin el'mustapha ba kasancewar bai bata wannan damar ba ya riqeta sosai a jikinsa,

Uwani ta xauna ji take kamar ta fashe masu kai a yanda suke, da kyar jiddah ta tashi, ta xauna gefensa tana qoqarin hada masa tea,

'is ok jiddah, sauri nake kuma tuni na qoshi tunda na sami abinda nake so daga jikinki, taji nauyin maganar sa saboda uwani amma bata nuna ba,

Tace amma kasan xan shiga damuwa idan har bakaci abinci ba, tukunna Ma idan kaje me xakaci haka xaka xauna a office da yunwa.

Bani farfesun naje dashi ya isheni, da kanta ta hada masa ta bashi, xata raka sa ya dakatar da ita.

'Na hutar dake xauna kiyi breakfast dinki, kafin tayi magana ya juya da sauri ya fice.

Dogon tsakin da uwani taja ne ya dawo da hankalin jiddah xuwa gare ta, batayi magana ba kuma bata qara kallon uwani ba,

'An shiga haqqina Allah ya gani, abinda ke xuciyata kuma na barwa kaina sani, na yafe ko ban yafe ba, ta murguda bakinta tana qoqarin ture kayan dake gabanta.

Kallonta jiddah tayi cikin son gasgasta abinda taji uwanin na fadi,

Me kike cewa uwani?

Cewa nayi an min shige, kwana bakwai ne girkina saboda kowa yasan ni budurwace, amma saboda me xaa xauna da mijina ranar girkina ana tsotsar bakinsa, nima sai na rama wlhy.

Murmushi jiddah tayi cikin mamakin uwani, wai mijinta, a yanda tasan halin uwani iyayenta Ma bata raga masu ba wurin maida masu magana ya saka ta ja bakinta tayi shiru, ta dauki kofin tea ta kai bakinta tana sha.

'Wannan halin ko in kula da jiddah tayi akan uwani yayi matuqar bata mata rai da fusatata,

Ni dama nasani ba saboda tausayina yasa aka aura min shi ba sai dan a qara cusa min baqin cikin da xai sa xuciyataa ta fashe na mutu a huta dani an yarda kwallon mangwaro, to yanxu na fara rayuwa, kuma ba wanda ya isa ya rabani da mijina, ta bigi table din ta tashi a fusacce ta bar gurin.

Binta da kallo jiddah tayi har ta bacewa ganin ta, batayi mamakin abinda uwani tayi mata ba a yau domin shine karo na biyu, sun taba irin wannan fadan kamar uwani xata dake ta saboda ta gayamata gaskiya akan iyayenta da take Ma rashin kunya, tun daga lokacin bata qara mata magana akan ta daina ba, sai yau da ta qara mata wannan, dama tasan halin uwani idan tana neman abu a gurinka xata riqa baka girma kamar xata hadiye ka amma da xarar buqatarta ta biya to ba shege a gurinta sai kai.

Allah ya shiryeki uwani shine abinda jiddah ta fada tana qoqarin cusa arish a bakinta.

A gurguje🙄

2 month

'Surry ke kallon uwani tana yatsina fuskarta,

Dube ki dallah malama, kin bata wayonki da qurciyarki, dubi yanda kika dawo, son maso wani qoshin wahala, kuma abinda aka gina da cin amana ai baya kyau.

Ko ma me xakice kice, ban kiraki kixo gidana ba ehe, wanda nake so tunda bake bace akansa ba ruwanki.

Hakane, ni uwar karambani da cusa kai,  maganar makaranta kindai na xuwa tunda kikayi aure, ko miye dalili.

'Na ajiye karatu, bautar aure nake yi.

'ni badan na ganki da casbi a hannu kina a ba da na soma xargin kin fara shaye shaye, yaushe Ma kika fara riqa carbi a hannunki ne, ko duk el'mustapha ne ya sauyaki.

Shiru uwani bata tanka ba,

Saboda auren kike cewa kin fasa karatu uwani, kima kanki fada uwani ynxu kike da damar karatun kafin ki fara haihuwa, shekarun da kikayi a baya kina nufin sun tafi a banxa?

Karatu dai nikeyi ba wani shege ke min ba, kigayamin tun da nake xama a ajin me nake fahimta ko kin manta irin kwakwalwata ne, dana bata lokacina ina shiga aji bana fahimtar komai gwanda na xauna nayi bautar aure tunda har nayi secondary, kin manta semester can da result ya fito duka c.o ne uku kawai nayi passing na kawo result gidannan matar nan harda dangwara ta tana cemin takkwala ko ban gayamiki haka ba?

Dole xataji haushi saboda kudin da take kashe maki na School uwani wlhy ko nice xan qara da ce maki mai kwakwalwar kifi saboda naki daqiqancin yayi yawa, abinda ke qara bani haushi akanki ayi maki dictation baki iya rubutawa copying Ma da kalma daya daya kikeyi shiyasa nake juya maki baya idan aka shiga jarabawa.

Yanxu sai dai ki juyawa iska baya, uwani ta daina shiga aji ni bautar aure nake yanxu, wannan casbi da kika ga ina ja kariya ce daga sharrin aljannu ko wani sihiri da kishiya ke aikowa amarya dan ta hana mata xaman gidan miji.

Lallai uwani, ai kowa yasan xuciyar jiddah abinda kike fada baxata iya aikata maki ba kuma insha Allah xan sanar da ita yanxu cewa kindaina xuwa makaranta.

Kifi ruwa gudu, kada ta barni da rai tunda tasan gaibu kotasan dalilin qin xuwana.

'Surry ta tabe baki, idan kika ce kina bautar aure dariya Ma kike bani, keda miji baya kulawa bai masan da xamanki a gidan ba, is better ki koma makaranta ko kin sami abinda xaki taimaki kanki watarana, kafin uwani tayi magana ta ciro mata katunan auren ta ta miqa mata,

Ina miki albishir aure na da Yusuf wani sati.

Wane Yusuf din?uwani ta tambaya tana kallon katuna,

Yusuf dai wanda kika sani..... Ashar din da uwani ta dura ya katse surry,

'Dan kaza kaza...... Ni xaki ci amana ki yaudara, saurayina xaki aura.

Auren soyayya kuwa xamuyi, ba auren ina so baya so ba, saurayine kuma ni kadai a gurin sa mu murji quciyarmu da soyayyar mu son ranmu.

'ashe dama ke macuciya ce, ina tare dake kina cin amana ta kina soyayya da saurayina, wlhy sai na rama.
Chapter 14 · 0% Book details