← Book details El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 80

Sashe 31

El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Noooooooo Ar..... tayi shiru sakamakon kukan bindiga da taji, ta bude idanuwanta dai dai lokacin da arham ya fadi ragwaf a jikin uwani dake kusa dashi,

Kurma ya maida bindigarsa ya ajiye yana fadin shima yana cikin Bill xaki biya kudin aikin sa,

Uwani ta dauki arham taje har gaban jiddah ta ajiye mata shi, jini ya taba gyalenta batare da ta sani ba, murmushi tayi tana kallon jiddah kana ta juya ga kurma.

Xan yi ma waya, kana kashe ta xan gayama inda xamu hadu na baka kudin bana son na cigaba da xuwa nan saboda xargi.

Ina sauraren ki cewar kurma, uwani ta juya tabar gidan.

Jiddah ta maida kallonta ga arham dake kwance a gabanta, ta rungumoshi tana kallon inda aka har besa a hannu ne,

Kurma ya dube ta yana fadin kuskure aka samu kika ga na harbesa a hannu, xuciyarsa na so harbawa aka sami akasi, amma ba komai tunda ya mutu ai shikenan, ya tashi ya bar falon yana wata tafiyar qasaita.

Kuka yaqi yaxo mata a wannan lokacin, sai jiri take gani, tana son tayi kukan ko xata sami sauqin xuciyarta amma ta kasa, kuka Ma rahamane, ta qara rungumeshi a jikinta bayan ta sumbaci goshinsa, addua take Allah yasa kar ya mutu, ina ma xata sami wanda xai taimaka yaje mata dashi asibiti, tana jin ihunsu a gida,

Ta soma jijjiga arham, bata yarda ya mutu ba, arham ka tashi, mummy is with you, dan Allah karka mutu ka barni, sai ta gigice tana neman xaucewa,

Help me, please help me and save his life, ta soma waige waige kamar me neman wani a gurin.

Uwani na isowa ta ci karo da motocin yan sanda a gidan, gasu tsatsaye birjik kamar masu biki.

Tayi parking ta fito tana Jan tsaki a xuciyarta, kicibis suka yi karo da juna,

Ina kika kai min arham shine abinda ya fada idanunsa akan fuskarta,

Tashin hankali ya bayyana qarara a fuskarta, ta soma musa bata ganshi ba, batare da tunanin komai ba ya dauke ta da Mari har biyu masu kyau.

Ina kika kai jiddah da arham nake tambayarki,

Ta dafe kuncin tana kuka lokacin el'mustapha ya lura da jinin dake gyalenta,

Jinin menene wannan uwani, ta xare idanu tana kallon wurin,

Ya shaqo wuyanta a gurin,

Kada kice kin kashe min yaro uwani, ina kika kai arham da jiddah, answer me please,

Ta soma kakarin mutuwa, ba qaramin shaqa yayi mata a wuya ba, duk wurin ba wanda yayi qoqarin karbanta hannunsa saboda duk yaran sa ne sai ibrahim kadai shima da kyar ya kwace ta hannunsa,

Ka barni na kashe ta ibrahim kafin naji mutuwar arham a bakinta, dama na gayama nine mutum na farko da xai fara kamata dumu dumu, ya xaro bindigarsa ya sai ta a goshinta.

Ibrahim yasha gabansa da sauri yana fadin,

Me kake yi el'mustapha, control your temper, idan ka kashe ta ina xamu sami inda arham da jiddah suke, baka tunanin abokan aikin nata suka ji mutuwarta su gudu dasu ko su kashe su.

Xamuje ta kaimu inda suke yanxu, kowa ya shiga mota cewar ibrahim yana kallon sauran yan sanda.

Pherty ta gaishe ku,

_Afuwan pls xaku ji ni shiru na kwana biyu, due to some problems, nagode da qaunarku ga littafin El'mustapha._

Pherty luvs you ol😀
EL'MUSTAPHA

Haske Writers Association
Home of experts and perfect writers

Fertymerh Xarah💞

38

Ba abinda ke tashi a gidan sai sautin kida da raye raye, abokansu daga wani gu sai xuwa suke, kowane da makamin sa hannu, suna tafe suna shan giya wasu na xuqar sigari.

Ko taron me suke yi yau? Kurma yaci gayu cikin wasu qananan kaya, wando three quarter na black jeans, rigar farar mai qaramin hannu, sai qafafunsa dake sanye da sneakers👟, baqin glass ne sanye a idanuwansa, sai wata shegiyar hula da ya dora akan sa, ya gogu fa sai Ma kun ganshi😀

Yana riqe da qugun wata budurwa tashi, bra ce kawai sanye a jikinta sai wani guntun buje ko pant babu a cikinta, tunda yasa hannu qasan bujen nata hankalinsa ya nemi gushewa,

Ta qara banqaro kirjinta tana xuqar sigari, hannunta daya na kan hannun kurma dake cikin bujen nata,

Baxan jure kallon wannan shashanci ba gwanda naje nayi kallon masu d'an kamfai🤧.

Har lokacin jiddah na rungume da arham, kanta yayi nauyi sosai, ga jiri da take gani idanunta sunyi jawur saboda kuka kuma har lokacin bakinta bai mutu ba wajen kiran wanda xai taimake ta.

Tana jin hayaniyar su, tana jin yanda suke shewa,

Help... Somebody help shine abinda goga yaji jiddah na furtawa lokacin da ya shigo da tashi budurwar.

Bai san wainar da ake toyawa ba ya qarasa yana fadin,

Ina kika sami yaro, ta bude idanu da kyar tana kallonsa, tana ganin goga ne jikinta ya dauki rawa saboda yana matuqar tausaya mata da taimakonta.

Yaro nane ya kashe min shi, ka taimaka ka kaimin shi asibiti, dan Allah ka taimakeni kada ya mutu.

Ya taba arham yana kallon inda kurma ya harbesa,

Shi wannan yaron menene laifinsa, meyasa kurma yake marar imani ne,

Numfashinta ya soma sama sama,

Tace ka taimakeni, ka kaimin shi asibiti kada ya mutu, dan Allah ka taimakeni.

Ina je dashi asibiti xaa iya kamani ai is very risk idan baki sani ba, bari naje na kira maki likitan dake duba mu a duk lokacin da aka harbi wani a cikin mu, ki kwantar da hankalin ki yanxu xan dawo.

Bai jira cewar ta ba ya tashi ya fice da gudu ko budurwarsa bai waiwaya ba cikin tausayin jiddah.

Jiddah ta qara rungume arham banda sumbatar sa ba abinda take sai kuka.

*

Suna qoqarin saka uwani motar sai ga su hajiya da abba, sunxo yiwa el'mustapha gaisuwar mama, sunyi masa a waya basu sami damar xuwa ba sai yanxu.

Hajiya ma jiki yayi nauyi, ciwon qafafu take fama dashi.

'Abba yace lafia el'mustapha na ganku haka.

El'mustapha bai yi magana ba, akwai kunya sosai tsakanin sa da surukin sa, ibrahim ne yayi masu bayanin komai.

Inna lillahi wa Inna ilaihir raji'un, iyayen suka juya suna kallon uwani tana tsaye abinta ba alamar nadama ko wani dana sani a tare da ita, ta dauke kanta gefe daga kallonsu tana tunxuro baki.

Hajiya kam har da kuka,

Tace duk yanda nayi dake uwani akan idan kina da sa hannu a batan jiddah kika musa, kika bar baiwar Allah da ciki cikin uquba, anya uwani xaki ga annabi kuwa, kwata kwata babu imani a xuciyarki, baxan taba yafe maki ba kije gaki ga duniya.

Allah baxai kamani da laifin komai ba tunda bake nayi mawa ba cewar uwani, a xuciyarta take maganar, sai anyi magana ki fara matsar hawaye kina kuka salon ace ni ke sakaki kuka saboda tsabar munafurci, ta gyara tsayuwarta hade da rungume hannayenta a qirjinta,

'Abba baiyi wata wata ba ya hau ta da duka, duk gurin ba wanda yayi qoqarin hanasa kuma duk dukan da yake mata bai raunana xuciyar uwani ba, bako digon hawaye a tare da ita haka take da taurin xuciya kamar namiji.

Shi da kansa ya barta shima dan ya gaji ne,

Tunda kika iya auren mijin jiddah na yafe ki a xuciyata uwani, na cire ki a raina bani da wata 'ya a duniyar nan sai jiddah kadai, yau kin cutar min da 'ya, kin cutar da baiwar Allah salihar mace mai haquri da kawaici akan duk abinda kike mata, kije gaki ga duniya alhakinta kadai baxai barki ba ballantana na iyayenki.

Duk jikinta yayi tsami saboda duka, gefen fuskarta Ma ya kumbura, ta gyara kallabinta ta shiga mota cikin jin haushin tsayuwa da su, ga wani takaicinsu daya cika xuciyarta, duk gurin kallon mamaki ake mata

'Abba yace el'mustapha kayiwa uwani duk hukuncin daya dace da ita a matsayin ka na dan sanda, kada ka tausaya mata ko nauyin dan tana tamu, Sam ba tamu bace kuma bamu Santa ba.

El'mustapha dai baice komai ba har lokacin bashi da wani buri a yanxu kamar ya ganshi tare da jiddah da arham,

Yace abba ku shiga gida tare da hajiya kafin mu dawo.

Ni xan biku naga wane hali jiddah take ciki.

El'mustapha ya riqo hannunsa cikin jin nauyinsa,

Yace baxaka bimu ba saboda bamu san yanda abin xai kasance ba, ko mu kashe ko a kashe mu yan ta'adda ne masu xaman kansu, idan suka mana gardama xamu harbesu ne suma xasu harbemu dan baxasu barmu ba, kayi haquri ka xauna tare da mana addu'ar nasara.

Allah ya kare ku kuma ya baku sa'a akan su, abba ya fada yana kallon el'mustapha uwa ya sa ihu dan baqin ciki da abinda uwani tayi.

Kowa ya shiga mota, suka dauki hanya, maimakon uwani ta basu direction na kwarai sai ta soma basu wrong direction.

Wasa wasa sun kusa xagaye Abuja sai faman tafiya suke a duk inda ta nuna masu, hankalinta kwance ba damuwa tare da ita xatace kubi wannan titin, sai wannan layin.

El'mustapha ne ya fara gano kamar tana yi masu wasa da hankali, ya daka mata tsawa yana tambayarta, ta tunxuro baki tana fadin,

Ni na manta hanyar ne, na manta inda ake shiga aje gurin.

Uwani hukuma cewar ibrahim yana kallonta cikin takaici.

A yanda el'mustapha keji kamar ya kashe shegiya a gurin, duk wani fushinsa da Jan idonsa baxai saka uwani taji tsoron sa ta gayamasu gaskiya gashi kusan awa daya suna yawo a titi, dole sai yabi da dabara da rarrashi, ya dube ta cikin kalar tausayi.

Uwani a hakan kike so na maida aure na dake?

Taji gabanta ya fadi, ta juya tana kallonsa, suna hada ido taji wani sabon sonsa da qaunar sa sun taru a xuciyarta, duk da ya rame wannan kwarjinin nasa yana nan, jikinta yayi sanyi taji kamar ta fada jikinsa saboda tsabar so,

El'mustapha na ganin tana masa wannan kallon ya cigaba da rarrashinta harda riqon hannunta wanda ya saka uwani yin hawaye saboda farin ciki.

Nan take tace su koma titin da xai fitar dasu Abuja, anan ta fara basu direction na gaskiya tanayi tana kallon el'mustapha, bata gajiya da kallon fuskarsa ko kadan.
Chapter 31 · 0% Book details