← Book details El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 80

Sashe 4

El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Jin kalmar matar aure a bakin el'mustapha ba qaramin mamaki ya sanya mahaifiyar sa ba, idan ta tuna shekarunsa da muqaminsa amma bashi da aure kuma baya da niyar yin auren sai a yau da taji mgnr a bakinsa.

'bana son kina min wannan kallon mama, I mean it nasami matar aure, very young, ina son mace mai nutsuwa da kunya, macen da xataji tsorona at anytime.

'kace qaramar yarinya ce, anya batayi Ma qanqanta ba, ba wannan bama ita tace tana son ka ne.

Ya tashi yana fadin koma menene mama ki shirya, very soon xaki sami in law, sai ki fara shirye shirye.

Ta bisa da kallo fuskarta dauke da murmushi, Allah ya karbi adduarta mustapha xaiyi aure, oh Allah ni har ina tunani ko aljana ta aure min shi, Allah ka nuna min ranar auren nan ka sanya alheri aciki.

Bayan kwana biyu....

Jiddah na kwance jikin hajiya tana tsifa sai ga Abban su ya shigo,

'ina jiddah?
'gani Abba ta fada bayan ta tashi tana kallon qofar shigowa,

'sanyo hijabinki ki sameni falo na yanxu,

Ta juya xuwa dakin ta, bata jima ba ta fito sanye da hijab din ta.

Tun da ta tunkari falon take jin bugun xuciyarta na qaruwa, da sallama ta shiga kanta a sunkuye, suka amsa mata sallamar.

Ta nemi guri ta xauna tana kallon abba,
'ga baqon ki, shi keson ganin ki.
'wata irin faduwar gaba ta dirar mata lokacin da sukayi four eyes da el'mustapha, jiki na rawa ta gaidashi kana ta juya tana kallon abba idanunta taf da hawaye.

'Abba wallahi na bashi haquri dan Allah  kace yayi haquri idan yaqi ka siya masa wata wayar ni ya barni.

Murmushi ya subulcewa el'mustapha, yana kallonta qasa qasa yana jin wani abu game da ita a xuciyarsa mai girma da nauyi, tabbas yana son jidda yana son kasancewa da jidda tana matuqar birgeshi.

'ba maganar waya taxo dashi ba jidda, maganar aure taxo dashi amma xan barki dashi kiji da bakinsa, idan kin amince shikenan dan baxan maki dole ba, bai jira cewar ta ba ya tashi ya bar falon, tsananin mamaki ya sanya jidda binsa da idanuwa har sanda ya bar falon kafin ta juyo tana kallon el'mustapha cikin son gasgasta maganar mahaifinta.

Da sauri ta maida kanta ta sunkuyar, baxata jure kallon kwayar idanunsa ba, ya tashi ya dawo kujerar da take xaune, da sauri ta matsa cikin jin tsoron sa, bai damu da hakan ba fatan sa ta amince da shi a matsayin mijin aure.

'ina son ki jiddah, taji muryarsa tamkar saukar aradu a kunnuwanta,

'aure nake so muyi jidda, kamata baxan tsaya ina jeka ka dawo ba kamar yanda samari keyi idan suna neman budurwa, banxo rayuwar ki dan na cutar dake ba, ina son kasancewa dake ne jiddah amma idan kin amince kamar yanda mahaifinki ya fada a yanxu, ya gayamin wacece jiddah tun farkon rayuwarta har xuwa yanxu.

Jikinta yayi sanyi, qamshin turarensa ke sanyaya xuciyarta, baxata ce bata da samari as her age ba, akwai su kam har masu son auren ta Ma amma batasan meyasa xuciyarta tafi amincewa da el'mustapha ba, bata san meyasa take jin sa axuciyarta a yanxu ba, tunaninta idan matar sa bata son ta fa.

'kinyi shiru jiddah, ko nayi maki girma ne? ta girgixa kanta, yace to menene?

'ina jin tsoron matar ka ta ganni qarama ta riqa dukana, dariya yayi sosai yana kallonta.

Funny jiddah, saboda me xata dake ki, ballantana banda mata ban taba aure ba jiddah, ta dago tana kallonsa da mamaki, ya gyada kansa cikin tabbatar da xancen sa.

'ba wai na rasa matar aure bane, ina dasu har masu roqon mahaifiyata na aure su ko na auri ya'yan su, ban sami wadda nake so ta kwanta min a xuciya ba kamar jiddah, aure lokaci ne, nikam yanxu nawa lokacin yayi Allah yasa jiddah xata soni.

Kafin kace me jiddah ta saki jiki sosai tana kallon el'mustapha yanda yake bata labarinsa da yan'matansa sai dariya take tana kallonsa musamman da yace itama sai ta bashi labarin samarin ta.

Ta tambayi kanta shin ko mutane nawa ne a duniyar nan irin El'mustapha?

yana da wasu ilhamomi na musamman a tare da shi da bata taba ganin su a ďa namiji ba, ko yanda yake duban mutane daban ne da sauran maxa,

Tsarin maganarsa cikin seriousness shine babban abinda ke burgeta dashi, ga kamun kai da sanin mutuncin kai, hadi da rashin son wasa ta ko ina, amma yana da fara'a sosai.

My wattpad Phertymerh1

*EL_MUSTAPHA*

HASKE WRITER'S ASSOCIATION
(home of experts and perfect writers)

Fertymerh Xarah 💞

13

Suna tsaka da firar su sai ga Uwani taxo dauke da qaton tire a hannunta, dawowar ta daga School kenan lokacin tana S.s.2,

Har qasa ta gaida sa cikin satar kallon sa, tana yaba sa a xuciyarta, cikin sakin fuska yake amsa mata yana kallonta kafin ya maida dubansa ga jiddah,

Gwiwoyinta sukayi sanyi, xuciyarta ta karaya, duk wata soyayya da Allah ya halitta a xuciyarta ta haďu ta tattare waje ďaya taji ba wani wanda take so a duniyar nan sama dashi batasan dalilin hakan ba amma haduwar idanun su ne sila.

bayan ta fito ta nufi cikin gida.

Hajiya kinga mijin anty jiddah kuwa?

'me akayi? Hajiya ta tambayeta bayan ta tsaida idanunta akanta.

Babban mutum ne fa, ya hadu amma da ganinsa baxai rasa mata da ya'ya ba.

Alhaji yace baida mata, police ne ai, nima yanxu yake gayamin.

Police fa hajiya? Me anti jiddah xatayi da 'Dan Sanda, mtsewwwww.

Bana son kinibibi da iyayi, d'an sanda ba mutum bane kinsan shi wane irin muqami ne atare dashi? Kar na qara jin wannan mgnr a bakinki.

Ta tabe bakinta batare da ta qara mgn ba, uniform na jikinta ta soma cirewa amma har lokacin xuciyarta fuskarsa take hasko mata, duk ta tuna dashi sai gabanta ya fadi har lokacin da jiddah ta dawo bayan ya tafi.

Kallo daya xakayiwa jiddah ka tabbatar tana cikin farin ciki, sai murmushi take, hajiya nayi mata dariya tana tsokanarta, Matar dan sanda.

Ranar jiddah da el'mustapha baxaa ce komai ba sai faman juye juye suke a gado tare da kewar juna, suna jin wani sabon al'amari a tare dasu.

A gurguje pls

Ana gab da bikinsu lokacin uwani ta jewa hajiya tana kuka, ita a duniyar ba wanda take so kamar el'mustapha.

Batare da tunanin komai ba hajiya ta dauke ta da Mari.

Kina da hankali kuwa Aisha, kinsan me kike mgn akai, mijin yar uwarki kike so, kul na qara jin wannan mgnr ko kika nuna wata alama da jiddah xata gane kina son mijinta wlhy da ni da ke ne a gidannan kuma har abban ku sai na fadawa.

'kiyi haquri hajiya, bansan yanda xanyi ba tun farkon ganina dashi na kasa cire sa a xuciyata ki taimaka hajiya kisa baki ya aure ni tare da anty jiddah tun..... Saukar Marin da taji a kuncin tane ya hanata qarasa mgnr ta, kallonsa take cikin mamaki bayan ta dafe kuncinta da tafin hannunta.

'Ashe baki da hankali ban sani ba Uwani? Mijin jiddah kike so yar uwarki? Wallahi na qara jin wannan maganar a bakin ki ban yafe maki ba, ni ba mutumin banxa bane da xanci amanar marainiyar Allah, kin manta dani dake da mahaifiyar ki a inuwar ta muke, dukiyar tace fa, bani da buri a duniyarnan na ganin na aurar da jiddah ga miji nagari kuma alhamdulillah na samu, ke baxaki sani jin kunyar idon duniya ba, kuma ki kiyayeni wlhy, ya juya ya fice da sauri.

Hajiya ma bata qara magana ba ta barta nan cikin qunci.

Ranar uwani tayi kuka kamar me, el'mustapha ya riga yayi mata nisa ta riga ta rasa shi a karo na farko amma bata debe tsammani da cewa watarana sai ta xamo matar el'mustapha.

Jiddah tayi juyin duniya tana tambayar uwani meya kumbura idanunta kukan me take gashi harda bakinta ya kumbura taqi magana,

Taje ta tambayi hajiya cikin nuna damuwa da halin da take ciki
Me akayiwa uwani ne take kuka tun daxu hajiya, kinga yanda fuskarta ta kumbura kuwa?

'kyale ta kawai jiddah kada ki matsa da tambayar meke damun uwani kinsan ba hankali ne da ita ba, yanxu haka daga makaranta ne.

Jiddah bata qara magana ba, ta xauna kusa da hajiya tana fadin.

'hajiya ya maganar mu, xaki bani uwani inje da ita, tun ina qarama na taso tare da uwani nayi sabo da ita sosai kibarni naje da ita.

'da so samu ne kibar uwani ta xauna anan jiddah, Uwani ta canxa daga yanda kika Santa, bana so taje ta jawo maki wata matsalar da xaa xo ana dana sani.

Babu wata matsala insha Allah hajiya, kiyi mana addua.

'amma ba yanxu xata xo ba har sai ta gama makaranta, idan ya so sai ta cigaba acan tunda kin matsa.

Murmushi jiddah tayi tana fadin Allah ya kaimu hajiyar mu ya barmu tare da ke.

A gurguje pls😊

Ranar da aka daura aure a ranar ake dinner da dare akai amarya gidanta.

Ranar dinner sunyi matuqar kyau, murmushin dake dauke a fuskarsu ke qara fito da kyawunsu,

Sai hasken camera kake gani a ko ina ana daukar su hoto, yayin  da wasu ke qoqarin uploading a status, Facebook da Instagram.

Duk abin nan da ake uwani na xaune da qawarta surry, idanunta kyam akan el'mustapha, duk wani motion dinsa akan idanunta ne, duk wani motsi da xaiyi tare da xuciyarta ne, kallonsa kawai yana sanyaya xuciyarta, hannunsa dake riqe dana jiddah ji take kamar ta rusa ihu a gurin saboda wani abu daya xo ya tokare a qahon xuciyarta.

'ke wai tunanin me kike ina ta magana kina can kina kallon mijin yayarki?

Uwani taja numfashi batare da ta kalle ta ba sai dai ta dauke idanuwanta daga kallon el'mustapha tana kallon wasu yan mata gurin.

'Surry son sa nake yi, idan ban same sa ba xuciyata xata iya bugawa na mutu, kowane daqiqa na xuciyata tare da tunanin sa yake tafiya, ki taimakeni ta wace hanya xanbi na mallake sa?

'ikon Allah, waye wannan kike so haka uwani harda hawaye?

*el'mustapha* mijin anty jiddah..... ta fada idanunta kyam akan na surry xuciyarta na tsananta bugawa.
Chapter 4 · 0% Book details