← Book details El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 80

Sashe 7

El-mustapha Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna xaune cikin farin ciki da soyayyar juna, sai dai abinda jiddah ta lura dashi game da el'mustapha yana daya daga cikin irin maxan nan da Sam ba koyaushe suke son kasancewa da matansu ba kamar ita da Allah yayi ta cikin rukunin matan nan masu tsananin buqatar miji.

El'mustapha daya fuskanci haka a tare da jiddah bai taba bari ta nemesa yaqi biya mata buqatarta ba koda kuwa he is not in need, dole sai ya sauke wannan haqqin dake kansa, baya son batawa jiddah ko kadan haka yake ji kamar xuciyarsa tana tafiya ne tare da ta jiddah.

Sanda ta haifi twins maza a lokacin akayi masa qarin girma xuwa AIG na police, tym din uwani ta gama skul sai  jiddah ta maidata nan gidanta abuja ta cigaba da xama tare da ita tana xuwa skul har lokacin da xatayi miji.

Yanda jiddah ta dauki uwani tamkar qanwarta da suke uwa daya uba daya kasancewar hajiya da abba sunyi mata riqo irin na amana da babu xalunci aciki kamar sune suka haifeta, wannan dalilin yasa jiddah tayi alqawarin kula masu da uwani harta maidota inda take da xama.

*

Dawowa daga labari

Bayan kwana biyu uwani ta murmuje ta saki jikinta tana dan fitowa falo ta xauna tare dasu Aryan,

Sai dai har lokacin bata qara sanya el'mustapha a idanunta ba wannan ya qara shigar da ita cikin wani hali.

Daga lokacin sai ta daina fitowa ko falon sannan ba inda take xuwa makaranta Ma ta daina xuwa, jiddah na damuwa da halin da uwani take ciki kuma tayi tambayar duniya tace mata ba komai sai ta xuba mata idanu.

Da dare suna tare da el'mustapha bayan sun gama komai na al'adarsu sun kwanta, matsawa tayi ta shige jikinsa sosai,

Ya matsota xuwa jikinsa yana fadin, jiddana ina jin barci sosai gashi gobe ina da tafiya tunda sassafe.

Murmushi tayi hade da Jan dogon hancinsa tana kallonsa, abinda kake tunani ba shi bane tunda ka maidani banda wani aiki sai akan wannan abin.

Shima murmushin yayi hade da hada hancinsa da nata yana gogawa a hankali, to menene jiddana?

'Na rasa gane kan uwani kwana kinnan, bata da aiki sai kuka a koda yaushe, sannan bata fitowa tana daki xaune babu walwala a tare da ita, nayi tunanin bansan laifin me nayi mata kuma nasan bana tauyeta akan komai dake gidannan, ina tsoron kada wani abu yaje ya sameta shiyasa na gayama ko xan fadawa su hajiya ne su san halin da take ciki?

Ikon Allah, ya fada bayan ya tashi xaune yana kallonta,
Bata gayamaki meke damunta bane?

Nayi ta tambayarta tace ba komai, yauma ko da naje dakin tana kuka, Banan ta gayamin ta daina cin abinci sosai.

Yayi shiru yana tunanin, kafin yace kuma ke bakiyi mata komai ba, kinsan xaman tare yau da gobe dole anan samun sabani, meyiwuwa ke xaki iya mata wani abin da xai bata mata rai baki sani ba.

Wlhy banyi ba nayi tunani ban gane komai ba, nayi tambayarta ko Yusuf din tane duka tace aa am totally confused, pls help me out.

Gobe kije da ita asibiti, qila akwai abinda ke damunta ne batason fada, idan kuma babu ki sanarda iyayen ta da wuri.

Nima haka nayi tunanin cos abin yabani tsoro sosai.

Ki kwantar da hankalin ki kinsani bana son damuwar ki ko kadan, insha Allah komai xaixo da sauqi.

Allah yasa, ta fada tana qoqarin gyara kwanciyarta a qirjinsa.

'Washe gari bayan ya fita office, su Aryan sun tafi makaranta, wanka tayi ta shirya tsaf cikin shirin fita asibiti da uwani.

Sai da ta nufi sashen masu aikinta tayi umarnin da abinda xasu dafa a gidan, kana ta nufi dakin uwani.

Photo ne manne a qirjin uwani tana kwance ta lumshe idanuwanta, ko kadan batayi xaton ganin jiddah a wannan lokacin ba illah motsinta da taji, da sauri ta tashi tana qoqarin boye photon hade da share hawayen fuskarta.

Good morning sister, yau fita xakuyi ne haka.

'eh amma dake, xamuje asibiti ne a duba agani meke damunki.

Uwani ta dabirce, ni.. ni.. 'Anty ba abinda ke damuna na gayamaki lafia na qalau,

Idan ba abinda ke damunki, menene dalilin canxawarki uwani? Idan ni da nake yar uwarki bansan damuwar kiba to waye kike so yasani, ko hajiya xan kira a waya ne ita ki gayamata.

Aa dan Allah kiyi haquri anty baxan qara ba, ta fada tana qoqarin share wasu hawaye a fuskarta.

Da alama damuwar ki nada nasaba da Yusuf ne, naganki da photo ina da tabbacin nasa ne, ya fasa auren ne kome, meya hada ki dashi.

Bugun xuciyar uwani ya tsananta, ta gyara xamanta tana kame kamen abinda xata fada, lura da yanayinta ya sanya jiddah xarginta tana kallon photon da uwani ta juya bayansa kamar ta sanshi, ta kauda xargin xuciyarta batare da sanin uwani ba ta shammaceta ta kwace pic din da sauri tana dubawa.

Wanda ta gani ya sanyata kallon uwani da tsananin mamaki hankalinta a tashe, yayin da numfashin uwani ya sarqe saboda tsananin tsoro.

Me kike yi da photon el'mustapha a qirjinki, menene alaqarki da wannan hoton uwani?

Tambayar da taji jiddah nayi mata ne ya sanya ta saki fitsari a inda take xaune batare da ta sani ba.

Pherty... ✍🏻
*El'mustapha*

*Haske Writers Association*

Fertymerh Xarah💞

17

'Anty kiyi haquri bada son raina bane, nima ban san yanda akayi ba, laifin xuciyata ne.

Laifin xuciyarki da tayi me uwani? Jiddah ta tambaya tana kallonta cikin rudewa, me kike nufi.

wlhy sonsa nake bansan yanda akayi xuciyata ta kamu da soyayyar sa, anty kiyi haquri wlhy xanyi qoqari na cire amma shine asalin damuwa ta.

Photon dake hannun jiddah ya subulce ya fadi qasan tiles, me take ji a bakin uwani haka, idan mafarki takeyi Allah ya farkar da ita daga wannan mummunan barcin, uwani ke son el'mustapha din ta, mutumin da bata hada shi da kowa da komai ba, mutumin da batason ko wacce mace ta rabe sa, mutumin da take gani ita kadaice a xuciyarsa har qarshin rayuwarta, taya xata iya rayuwa dashi da wata mace, macen ma uwani yar uwarta, impossible, juyawa tayi ta fita jiri na neman kada ta, she can't say anything for now amma uwani tayi mata baxata kuma ta cuceta idan har da gaske tana son el'mustapha.

Kallonta uwani keyi har lokacin da ta fice, tausayinta da dana sanin furta mata ya sanyata fargama amma ya xatayi tunda ta kamata dumu dumu da hotonsa a hannu meyiwuwa hakan xaisa ta amince mata ga auren mijinta.

Maida kanta tayi jikin pillow tana kuka sosai, bata iyayen ta takeyi ba yanda el'mustapha xai amince da auren ta shine matsalar, babu boka babu malami alqawari ne na daukar wa kaina ko ta halin qaqa sai na auri el'mustapha, sai ya xamo mallakina a gidannan, ta share hawayen fuskarta, ai ba dan mace daya akayi namiji ba, kowacce kissarta ta fiddata amma ina son el'mustapha kuma sai na rabi inuwarsa, ta share hawayen fuskarta hade da shigewa toilet.

Jiddah kuwa tunda ta shiga dakinta kanta ke mata wani irin nauyi, ta kasa gasgasta abinda kunnuwanta suka jiye mata a yau, uwani ke son mijinta, to ko uwani ta manta dangantakar su ne ta manta matsayinta na yayarta har take son kishi da ita.

Nan take ta fara tunanin take taken uwani akan el'mustapha tabbas biri yayi kama da mai, idan hakane uwani ta cuce ta batayi halin iyayenta na amana ba.

Yinin ranar gabaki daya a daki tayi sa ko abinci bata ci ba har lokacin da su Aryan suka dawo, su kansu sunsan mamin tasu tana cikin damuwa a yau duk surutun da suke mata shiru take a yau sai faman tunani, har lokacin da el'mustapha ya dawo.

Tunda ya shigo falonta yake kiran sunanta cikin muryarsa mai sanyi da dadin sauraro, tayi qoqarin sai ta xuciyarta kada ya gano tana cikin damuwa amma kallo daya yayi mata ya gano hakan a idanuwanta,

Da sassarfa ya isa gareta, ya dora hannunsa akan fuskarta yana kallonta sosai,

'meke damun jiddana, meyasa idanunki sukayi ja haka.

Da kyar ta hadiye kukan ta haqe da qago murmushin da iya karsa lebbanta,

'tun daxu nake fama da ciwon kai, dana sha maganine na sami barci inajin wannan daliline ya sanya sauyawar idanuna.

Allah ya baki lfy jiddana, gashi yau ina buqatar kulawar ki, ya xakiyi dani.

Dogon hancinsa taja tana dariya, abinda kake so shi xaa yi idan dai inada wannan iko, shima dariya yayi yayi gaba tana biye dashi a baya har dakin su,

Juyowa yayi yana kallonta, kinsan me Ibrahim yayi kuwa?

Ta girgixa kai tana kallonsa yayin da take qoqarin balle masa botiran rigarsa,

'aure xai qara next week, har ya bada sadaki amma bada sanin matar sa ba hadixa.

Jiddah ta xaro idanu tana kallonsa, yayin da gabanta ya tsananta bugawa,

'shi ibrahim din, amma meyasa xaiyiwa hadixa haka?

'dole ne xai qara kin sani, shekara nawa babu haihuwa sai daga baya nan suka gane ba matsalarshi bace ita keda matsala, as his age ya kamata ace yana da yara yanxu kinga kuwa dole xai qara aure banga laifinsa ba.

Jin kalamansa taji kamar shine xai qara auren da uwani kukan da take dannewa batasan sanda ta fashe da kuka ba, kacokan ya juyo yana kallonta da tsananin mamaki,

Kuka jiddana, meyasa, bafa kece xaa yiwa kishiya ba kinsani, ibrahim nace fa,

She can't control her tears batasan dalili ba sai xafi xuciyarta ke mata ta riqo hannunsa tana kallonsa,

Bana son kishiya el'mustapha ko wace iri ce, dan Allah kada kamin, ni kadai ce matar ka, ina son ka sosai.

Ya rungumeta sosai yana shafar bayanta cikin shigar rarrashi, namiji na qara aure ne bisa wani dalili nashi, bani da wani dalili da xai sanyani qara aure, bani da wata kalma da xan kare kaina a gaban Allah na rashin adalci tsakanin su, jiddah kadai nake so a rayuwata, jiddah kadai ce matata ba kuma wadda xanso bayanta sai ya'yana, ki cire wannan tunanin a xuciyarki kin sani bana son damuwarki kisa a xuciyarki ke kadaice matar el'mustapha kamar yanda UMMY take *Matar sadiq* ita kadai.
Chapter 7 · 0% Book details