← Book details Daga Ruga Nake Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 50

Sashe 14

Daga Ruga Nake Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

'' Daman dan wannan ne gaskiya Ashrap ba ka kyauta ba me ya sa za ka tsorata,ta har haka, kin ga wasa yake miki ba wanda zai sha miki jini kin ji ko? ku fito muntafi." Amma sam Dagori ta kafe akan ba za ta fita ba daga
arshe, ma da ta ga ana matsa ma ta kuka ta saki har sai da Mami ta je ta labartawa Abbi abin da ke faruwa ya zo ya rufe Ashrap da fa
a da
yet da su
in goshi a ka samu shiga.

Su na shiga Dagori da Salame sai faman ware ido suke ganin makeken restaurant mai kyau da tsari ga shi tsaf da shi kuri na musamman a ka ba su wanda ba ruwanka da sauran jama'a, an zo an tambayi kowa abun da yake bu
ata ko da aka zo kan Dagori dake ta faman dube-dube sai ji ta yi an ce.

'' Madam, do you need me?.'' Da sauri ta zaro ido tana duban mutumin dake tsaye yoo ko ka sheta za'a yi ai ba ta ce ga abun da yake fa
a ba fahimtar haka da Mami ta yi ta ce.

'' Mi ke ke son a kawo miki?.''
Da sauri ta ce.

'' Lemun jarka da burodi da nama.'' A yadda ta yi maganar sai da ta ba su dariya tuni ta tuna maganar Ashrap a ranta.

'' A'a ba na son burodi, amma duk abun da aka kawon zan ci.......

Dan Allah ku
an yi ha
uri da wannan ba na da lafiya ne ban samu yi ma ku mai yawa ba
DAGA RUGA NAKE
*NA*
*A'ISHAT SALISU UMAR NA DANGO*
*(Mrs Awwal)*
*HABIBTYN JAJIRTATTU CE*
*JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*
*(J.W.A)*
_Rubutu baiwa ce daga Allah, jajirtattu ne kawai kan iya amfani da wannan
asaitacciyar baiwa suka sauya tunanin al'umma cikin sau
Abbi ya du
eta cikin kulawa, ya furta.

'' Mai babban suna mene ne ya sa kika canza ra'ayin ki?."
'' Ba komai kawai yanzu na daina cin burodi, da lemu har abada." Aimanah da Inty suka she
e da dariya tun da su sun san dalilin da ya sa ta ce hakan.

'' Haba Mai babban suna jiya fa kika gama fa
in, duk cikin abinci kin fi sonsa yau kuma ki ce kin sauya ra'ayi?.'' Mami ta yi maganar ta na
an nazarinta.

'' Wallahi Mami Yaya Ashrap ne ya ce da ita duk wanda ke yawan cin bread da lemu har da nama wai 'yan shan jini sun, fi son jininsa duk fa shi ne dalilin da ya sa kika ganta ta tsure haka, ta ka sa sakewa.'' Aimanah ta fa
a tana dariya.

'' Kai Ashrap mine ne haka so kake ka sa ma ta tsoro a zuciyarta,? haba dan Allah da girman ka kake abu tamkar
aramin yaro?

To kada na sake jin haka.'' Mami ta yi maganar cikin nuna
acin rai, shi ma Abbi ya
an masa fa
a daidai nan aka kawo ma su abinci kowa a ka ajiye masa, abun da ya bu
ata Dagori da Salame Abbi fraced rice and chicken ya masu over Flash
in gaban Innaya ta kalla ta ce.

'' Ke kam Innaya wace aiki aikan ka ce ta ba ki shawarar ki sa a kawo miki tuwo?

Kaf wannan uwar da gwagwajiyar ki rasa mi za ki sa su kawo sai tuwo haba.'' Duban ta ta kai kan na ta ta saki wani murmushi ko kula zancen Maamah dake ba ta amsa, ba ta yi ba ta kaiwa namar kazar wawura sai kuma ta du
i mutane ta ga su Aimanah duk ita suke kallo, wuyan hijab
inta ta zame ta shige ciki tare da bu
e hijib
in ta saka Flash
in ciki ta shiga cin abincita tamkar ba gobe.

'' Wayyo Allah na garin da
i na ne sa a kai da
i kashe ni na huta, Allah sarki Baffa da Nene, Wayyo Hamma Habu...

Da
i ya barku banza ta fa
i kai kai.'' Saubatun da take fa
a kenan Cikin santi wanda duk a tunaninta a cikin zuciya take yin su, alhalin afili take abinta.

Sosai ta ba su dariya barima daga
arshe da ta zare hijib
in za ajiye a
asa, sai da ta cinye abinci ta tass har da si
e kwano ta sha lemu ta saki gyatsa gami da hamdala sai a lokacin ta lura da ba ta da hijabi jikinta amma ku san duka suka wayance,ma ta Abbi ne ya du
eta.

'' Mai babban suna ko za'a
ara miki ne?." Ta washe baki.

'' A'a Abbi na kishi amma shi naman kazar a
aran shi amma ba yanzu zan ci sa ba a sakan a leda sai 'yan jima zan ci.'' Ta
arasa maganar tana lasar baki ta lumshe ido, dan tun da aka haifeta ba ta
a cin abinci mai da
i irin wannan ba.

'' To shi ke nan ku je mota ku zauna? za'a kawo miki."
'' Amma Sister ba kin ce ba za ki sake cin nama ba dan...."
'' Wai ni kam Inty ba za ku daina tsorata ta ba?

Ba ku jin magana ko?.''
'' Mami bar ta kawai Aradun Allah ba 'yan shan jini ba ko 'yan yakan kai ne, wallahi sai na ci naman kaza ai aradu an yi kuskure da aka bari na tauna gar
insa, ai ni da kaza yanzu muka kulla ala
a ko za su shanyen jini gwanda su sha mai da
i ah to.'' Ta fa
a ta na shan fuska a dole ita ba da wasa take ba, dariya su ke yi ma ta dan kam ta ba su dariya.

'' Lallai cike kin shiryama mutuwa?

To ya yi kyau.''
'' Wai Ashrap ba ka ji ko?."
'' Sorry Abbi mu tafi ko?." Ya fa
a yana barin wurin suka bi bayansa.

Ko da suka kama hanyar Kaduna Dagori kam ba ta gane komai ba dan bacci ta sha abun ta musamman da
oshi da sanyin AC suka ha
e ma ta haba sai bacci, ita ce ba ta farka ba sai da suka
arasa.

'' Sister ki tashi mun kawo gida?."Aimanah ta fa
a tana tashinta, mi
a ta yi tana tashi zaune tara mutsutsika ido.

'' Wai har mun kawo ashe ma ba ni sa?."
'' Ai kuwa ba ni sa tun da kin ishe mu da nasarin bacci ki da sambatu.''
'' Yaya Ashrap wai da gaske bacci na yi?."
'' A'a ba bacci ki yi ba, kun ga ni ku fita zan rufe mota." A hankali ta fito
arfarta ta fito dan dama tuni kowa ya fita ita kawai ta rage, tana fitowa ta fara ware ido tana kallon makeken gidan da sam ko a mafarki ba ta ta
a hasaso kalarsa.

Kata faren gida ne mai girma gaske wanda iya parking lot zai iya
aukar motoci sama da goma ba tare da ta kura ba ginin bene ne wanda aka tsara shi daidai da zamani fa
in kalar tsaruwar ginin tamkar
ata lokacin ne tsarin ginin sam ba ka ce a Nigeria kake ba dan bai yi kama da tsarin irin namu ginin ba tsarin ginin irin na kasashen Turai kallonta ta mai da ita aka jera wasu kujeru tare da table a cikin wata runfa da aka yi ma ta wani irin ado mai
aukar ido a gefe an
awata wurin da adon flower's masu kyau da
awa.

Hannunta ta ji an kama.

'' Mu je ko?." Ta
ago ta kalli Aimanah da ta rikota haka take bin bayanta hannunta na cikin na ta suna tafe ta na dube-dube ashe ba ta ga komai ba sai da suka shiga farlon makeken farlon ne wanda ya ji kujeru har two set farin fant ne sai Chairs da suka kasance Black and Gold color har labulan
akin haka kalarsu take, ba wani taikace ne a cikin farlon ba amma an tsara shi daidai da zamani a gefe dama da hagu matakale ne na bene kowa ne da bangarensa sai gefen gudu dake da dinning area sai kitchen, sai gefen arewa da ke
auke da wani korido mai
auke da
akuna har uku kowane
auke da toilet a cikinsa.

'' Aimanah ki haura sama da su, ki kai su
aki su yi wanka, sai su sauya kaya kin ga duk sun kwaso gajiya.'' Mami dake haurawa benen da ke bangaren dama ta fa
a tana kuma gama fa
in haka ta ci gaba da tafiya.

Aimanah ta dubi Salame dake tsaye ta na kale-kale.'' Aunty mu je ko?." Ba ta fahimci abun da take nufiba sai da ta ce.

'' Aunty Salame.'' kamin ta
an razana su ka nufi
ayan benen dake gefen hagu su na taka matakalar farko ta biyu za su ta ka ta uku Aimanah ta ji ihu.

'' Wayyo Allah Innalillahi wa inna illahirin rajiun Wayyo Allah na shiga tsaka mai wuya Wayyo Wayyo!.'' Da sauri Aimanah ta juyo jin ihun Dagori dake sake ri
e mata hannu tamkar za ta karyasa ta ga ta wani duge ta na hawaye sha
e-sha
e tare da rufe idota.

'' Sister lafiya mene ne?." Cikin Muryar kuka ta ce.

'' Aradun Allah ba zan wau wannan abun ba Aradun jana yake yana juya ni kuma fa sama na ga muna yi Aradu ba za ni ba.'' Daidai nan Abbi da Mami suka sauko dan duk sun jiyo ihunta.

'' Lafiya mi ke faruwa ne?." Abbi da ke gaban ya fa
a yana
arasa saukowa.

'' Aradun Allah ku yi ma ta magana ta sauko da ni akan wannan gajimare da ta
ora ni Yiiiiiii Wayyo Allah na.'' ta fa
a tana fashewa da kuka.
Chapter 14 · 0% Book details