← Book details Baya Da Kura Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 50

Sashe 8

Baya Da Kura Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Manal bata bi ta kanta ba ta tashi ta saka mayafi ta fita ta siyo ™osai dan shi take son ci, ta dawo ta zauna ta sha kunun ta ta ragewa Mama dan tasan Mubeena ba sha zata yi ba.

Tana nan zaune ta hango Mama ta fito tayi wanka a banWakin ta da yake da glasses Win ta a ido tana iya gani duk da ba sosai ba, ta ™araso ta zauna Manal tace, Mama barka da fitowa. Mama tace, Yauwa, ya jikin?.

Na warke.

Naga alama maganin da ya baki yana da kyau sosai, gashi kin ware. Allah ya sa kina aure ki huta da wannan ciwon.

Manal ta amsa da amin kafin ta kalli Maman taga fuskar ta babu walwala sosai tace, Mama Baba yace na faWa miki ya tafi Kaduna, ga kuWin magani ya bani ga na cefane. Yace in bai dawo da wuri ba mu kulle ™ofar. Mama tace, Allah ya kiyaye hanya ya dawo dashi lafiya. Ta amsa da amin kafin Manal ta sake cewa, Maganin ki ya ™are, Huzaifa yace in ya ™are na faWa masa saboda akwai wanda yake so ya baki, amma kafin nan bara na kira Surayya ta Wauki jinin ki muje a gwada mana.

Mama tace, ni kunyar Huzaifa nake ji, yaro kamar daman can ya san mu? Sai hidima yake mana baran ma yanzu da zaki auri abokin sa. Manal tace, ai yana da kirki sosai Mama, tun lokacin baya yake tausayina da farko ma na Wauka sona yake yi ashe ba haka bane. Mama ta girgiza kai tace, nima da farko nayi tunanin son ki yake yi, ashe tsantsar kirki ne da mutunci. Manal ta tashi ta fita ba jimawa suka dawo da Surayya ta gaisar da Mama ta Wauki jinin ta suka fita tare. A bakin titi akwai ™aramin lab a nqn aka gwada jinin suka dawo.

Bayan ta dawo ta buWe takardar tace, Mama ya Wan hau kaWan amma. Mama tace, shi ya sani, ke ba a gwada naki ba?.

Na riga naci abinci gobe ayi min.

Shiru ya biyo baya kafin Manal tace, don girman Allah Mama ki yi ha™uri, na saba da dariya ki wannan Waure fuskar yana cutar dani. Mama ta kalle ta tace, ya wuce ai Manal, kawai bana son naji kin sake yi min zancen mahaifin ki a gidan nan, bana so ba kuma na ™aunar hakan. Ke da Mubeena yara ne na halak, in ma kina shakku a kaina ki daina. Manal da sauri tace, ni na isa Mama? Ki yi ha™uri.

Mama tace, ya maganar Adnan Win na ki? Zancen ya wuce ko da saura?. Ina ji kuna waya ai nace munafuka daman kina son kayan ki. Manal tayi dariya ganin Mama ta dawo da abin wasa tace, Allah Mama shine yake nace min, amma ni da gaske da na fasa.

˜arya kike wallahi, kina son sa kamar yadda yake son ki. Shine mijin ki haka nake ji a zuciyata dan haka komai ya wuce ki manta kawai. Ai dan yayi hakan ba laifi bane, kece wacce zai aura ki haifa masa yara ai ba laifi bane dan yana so ya san asalin babar yaran sa.

Manal jin Mama tana cewa haka sai taji komai ya wanke a zuciyar ta tace, To Mama. Mama tayi dariya ta ja kunnen ta tace, ba wani to Mama, Daman kun shirya ai. Manal tayi dariya ta tashi tace, bara nayi sallah na kira Dr.

Wacce sallar kuma?. Jin hakan sai Manal ta tuna ashe ba bata da tsarki sai ta wuce ciki.

Waya ta Wauka ta kira Huzaifa ai kuwa ya Wauka suka gaisa ta faWa masa zancen magani da kuma sakamakon gwajin Mama, suka gama maganar sannan ta kashe ta fito wajan Mama tace, Mama yace min yana da aiki sosai yau, wai in zan iya anjima ko yanzu naje asibiti na karSa, da nace in ya tashi ya aiko min dashi sai yace a a tunda jiya baki sha ba kar ayi sake sosai, gashi daman na faWa masa sakamakon nan yace ya Wan hau kaWan.

Mama tace, To zuwan zaki yi?. Manal tace, shine nake tunani. Mama tace, ™yale kawai, babu inda zaki je. Manal ta amsa da to dan tasan daman baza ta barta ba ta shiga Waki.

Sai bayan sallar azahar ta kasa ha™uri da rashin maganin ta kalli Mama da take kashingiWe tana ja carbi tace, Mama zan je kawai ba karSo maganin nan kawai. Mama ta dube ta tace, bana son yawon nan ne Manal, ga hanyar asibitin nan nasu babu mutane, bana son kina zirga zirga ke kaWai a wannan waje mai ™arancin jama a.

Manal tace, To Mama ai dole sai na fita na siyo, gwara naje kawai ai ba wani nisa sosai. Mama tayi shiru ganin hakan sai Manal ta tashi ta wanke fuskar ta da sabulu ta saka abaya maroon kala cikin wacce Yaya Haron ya kawo mata a wancan dawowar ta shi ta yafa mayafin tace, Mama za je. Mama tace, kar ki jima Manal, ki kula don Allah kar ki tsaya a ko ina.

Manal ta amsa da to ta saka takalmi ta cross ta fita daga gidan. Wayar ta ta bayar a wajan masu chaji daga nan ta wuce asibiti su Bebi kai tsaye. Sai bayan ta sauka a napep kuma tayi tunani da wacce wayar kuma zata kira shi tace gata tazo? Dan gaskiya bata son shiga ciki. Tsaki tayi tana kallon asibitin daga waje tana jinjinga kyau da girman sa, a ranar ne ma ta ™are masa kallo yana da kyau sosai a iya gani da ido ma zai tabbatar maka da asibitin kuWi ne. Gama kallon tayi ta shiga ciki tana kallon ™ato filin asibitin ga motoci nan a ajjiye.

Allah ya sani bata son shiga ciki ta ja ta tsaya tana tunani abinda ya kamata ace tayi a wannan lokacin. Kamar ance ta juya ta hango shi ya fito yana sauri da alama akwai inda zai je, sai tayi dariya cikin Jin daWi yana zuwa gab da ita tace, Sannu Yaya Huzaifa. Da Sauri ya kalle ta yace, Haba Manal, ke da nake expecting Win zuwan ki tun Wazu sai yanzu?. Yanzu ma fitowar da nayi bayarwa zan yi a kai miki, kin san illar rashin shan maganin nan a wajan Mama?.

KarSar ledar da ya mi™a mata tayi tace, Sai yanzu na samu na fito. Huzaifa yace, ai kin kyauta, yanzu Ina zaki je?.

Gida zan koma.

Bara na saka a mayar dake rana tayi sosai. Kallon inda motar Bebi take yayi yaga bata nan ya kalle ta yace, ga mutumin naki baya nan, da yanzu ya fara harara ta. Tayi murmushi kawai shi kuma yana buga waya amma ba a samu wani a kusa ba balle ya kai ta. Manal ta kalle tace, Dr ka barshi kawai yanzu zan ™arasa gida.

Huzaifa yace, za a samu wanda zai kai ki. Manal tayi shiru yana waya amma shiru babu wanda yakd kusa cikin direbobin nasu, Manal ta gashi tace, ka barshi kawai zan wuce gida yanzu, na gode Allah ya saka da alkhairi.

Amin Manal. Zaki samu abin hawa kuwa?.

Bazan rasa ba in sha Allah.

Gashi aiki nake, amma muje na tare miki napep. Manal tace, wallahi ka barshi, in ban samu ba akwai gidan wacce zan je, nagode Allah ya bar zumunci. Ya amsa da amin ta fita shi kuma ya juya ciki.

A kan titin ta tsaya amma babu napep ko kaWan sai motoci da tsuke wucewa. Manal tayi ™aramin tsaki hanyar gabaWaya ba a samun napep sai kayi sa a. wata mota ce ta wuce ta sai kuma ta dawo aka faka daga gefe, na ciki ya fito ya ™araso wajan ta yana mata magana ita kuma Allah ya sani tsoron wajan take ji.

Bebi da shigowar sa layin kenan ya hango wata a tsaye kamar Manal Win sa a tsaye ita da wani, gaban sa ya faWi bai tabbatar ita bace sai da ya matso ya kalla yaga dai itace ga wani kusa da ita duk da yaga ta matsa amma ya sake matsowa inda take.

Wani irin abu mai Waci yaji yazo zuciyar sa da zafin nama ya tako motar ya ™arasa inda take tsaye kawai ya sauke glass ya kalle ta suka haWa ido, Ajiyar zuciya tayi ta gode Allah ba wata magana kawai ta shiga motar ya ja ya bar wajan.

BD˜B2P006

Tafiya suke bai ce komai ba bai kuma kalle ta ba amma kana kallon yanayin sa kasan ransa ya Saci sosai. Daman shi ba fuskar walwala ba gashi ya sake tamke ta sai taji ya bata tsoro sosai dan yanayin fuskar ma abin tsoro ne. Dogon tsaki taji yayi ya nemi waje ya faka motar ya juyo yana kallon ta yace, "meyasa kike son ganin raina ya Saci akan ki ne manal? Meyasa kike yin abu da gangan dan ki bani haushi?. Waye wannan yake tsaye a kusa dake har yana miki magana?."

Manal tace, "ni fa ban san shi ba kawai naga ya tsaya ne."

"Da ya tsaya me yake ce miki? Me ya fito dake daga gida ma har kika zo wajan nan?" A fusace yayi maganar sosai yana wara idanun sa a kanta ta kalle shi a shaagwaSe tace, "ni ban san abinda yake cewa ba, dan a tsorace nake sosai tsoro bai bari naji maganar da yake yi ba."

Ya daki sitiyarin motar har sai ta Wan firgita yace, "to me ya fito dake yanzu? Me ya kawo ki wajan nan yanzu kuma baki neme ni ba?." Manal tace, "to sai faWa ka ke min, ka yi a hankali mana sai nayi maka bayani." ta faWa kamar zata yi kuka tana kallon sa.

Kawar da kai gefe yayi bai ce komai ba tace, "Maganin Mama ne ya ™are jiya bata sha ba, shine na kira Yaya Huzaifa na faWa masa yace aiki ya yi masa yawa bazai samu damar zuwa ba nazo na karSa. Ni kuma gudun kar lokaci ya ™ure bata sha ba shine nazo na karSa, kaga maganin ma" ta faWa tana Wago masa ledar maganin.
Chapter 8 · 0% Book details