← Book details Baya Da Kura Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 50

Sashe 13

Baya Da Kura Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da yaje babban asibiti ya jima a ciki sai azahar sannan ya tafi gidan Hamza don a can suka yi zasu haWu kamar yadda aka saba in zasu tattauna abinda ya shafi asibitin su. A falon Hamza ya same su dashi da Huzaifa suna hira da alama sun gaji da jiran sa.

Yana shiga ya zauna bai ce musu komai ba Hamza ya fara magana akan abinda ya ajjiye su suka fara tattaunawa shida Huzaifa. Ko me zasu ce yana ji baya dai magana sai dai yace eh da a'a. Ya ™ular da Huzaifa har ya kasa shiru ya kalle shi yace, "wai kai meyasa ka ke haka ne? Sai a Sata maka rai a wani wajan kazo kana Waurewa mutane fuska har muna magana baka tankawa daga eh sai a'a?. Ina ruwan mu da Sacin ran ka?."

"Lallai ne sai nayi magana?" Abinda yace kenan ya Wauki lemon da yake ajjiye yana sha. Hamza yace, "Kai kullum ranka a Sace yake a yanzu, mun zo muna tattaunawa kamata yayi ka ajjiye Sacin ran ka faWi shawarar ka, abu ne da zai amfane mu gabaWaya. Da gaskiyar Huzaifa da yace ina ruwan mu da Sacin ran ka? Abinda ya shafe mu muke yi a nan kaima abinda ya da ya shafe ka ne ya Sata maka rai."

Bebi ya kalli Hamza yace, "ka faWawa abokin ka, ala™ar da take tsakanin sa da partner, ina nufin my life partner ya kawo ™arshe ta ko kuma ya rage ta, I can't tolerate komai ace Huzaifa, komai ace ai na faWawa Huzaifa, ya kamata ya sassauta ya san cewa she's my wife to be. In ma da yuwa a ajjiye ta a gefe ai ba dangin uwa babu na uba."

Huzaifa ya ™yal™yale da dariya yana kallon sa cikin sha™iyanci yace, "Kaga masu life partner, Daman akan Manal ne ka ke wannan Waure fuskar?. Ai daman nasan tunda ka ganta jiya tazo karSar maganin Maman su na san sai an yi haka. Bebi kafin ka san ta na riga ka sanin  ta ya kamata ka tuna wannan. In da ace soyayya zan yi da ita da wata™ila ba wannan labarin ake ba yanzu."

Wannan kalmar ta ya riga shi sanin ta haushi take bashi amma yaga alama shi baya ganewa bai kuma san kara ba, hakan ya saka ya ce, "Yanzu na santa, shiga rayuwar ta da lamarin ta ba baka bane. Kai ba Wan uwan ta ko wani nata ba meye na ka na shiga rayuwar ta?."

"Mutunci da girmamawa ne a tsakanin mu."

"You have to cut it off, abin is too much na lura baka son a yi shiru ba baka san kara ba kuma."

Huzaifa dariya ya bashi sosai ya dara, so yake ya tunzura shi ya sake zuwa wuya hakan ya saka  ya ce, "To ai ko ka aure ta bana tunanin zaka datse wannan ala™ar balle baka aure ta ba."

Numfashi ya sauke baice komai ba ganin ya mayar da abin wasa shi kuma da gaske yake. Gani yayi Abba yana yi masa waya ya Wauka ya fita. Hamza ya kalli Huzaifa da yake dariya yace, "ba abin dariya ba ne Huzaifa, ka san Bebi a kan ™annen sa ma ya aka cika balle wacce zai aura?, ya kamata ka rage Win tunda baya so har gashi ya kasa jurewa ya faWa maka. Kuma wacce zai aura ce, matsayin ka na likita shima  haka duk abinda zaka yi dan ka taimaka shima zai iya. Duk da Sangaren ka ne amma ka ™yale shi in abin ya kakare masa watarana zai nemo ka."

Huzaifa yace, "wallahi rigima ce kawai irin ta sa, amma ni ban da wata ala™ar da ita da har zata Sata masa rai haka, na san yana da kishi zai yi kishi dani amma ni wallahi taimakon ta nake ita da Maman ta  ba wani abun ba."

"Nima ban ce wani abun ba Huzaifa, zaku iya zumunci saboda baza ta manta da kai ba a rayuwar ta dan ka taimaka mata kai da mahaifiyar ta, amma ka san yadda zaka yi zumunci da ita Win kar ana wasa da dariya yazo ya zama matsala, kai kasan ko ™annen sa baya so a kula balle wacce zai aura, in ya bawa ™annen sa tsaro na kashi sittin cikin Wari ita zai bata Wari bisa Wari ne saboda auren ta zai yi.."

Huzaifa yayi dariya a lokacin Bebi ya dawo yace, "in ya kwantar da hankalin sa ma na kusa tattarawa na koma Qatar, kuma ya san ina da wacce zan aura tun ba yanzu ba balle shaiWan ya dinga kawo masa wani abu mara kyau a zuciyar sa. Manal kuma akwai kyakykyawar ala™a tsakanin mu, akwai girmamawa da mutunta juna wani bai isa ya hana ba" ya faWa yana kallon sa dan wallahi daWin tsokanar sa yake ji.

Bebi bai ce masa komai ba dan yaga so yake ya saka shi magana shiyasa ya share shi,  Hamza yayi dariya yace, "Huzaifa baka da kirki. Bebi kayi ha™uri Huzaifa zai daina shigewa wacce ka ke so."

Huzaifa yace, "ni mamaki ma yake bani, ya manta lokacin da yake cemin son ta nake?, in auren nata nayi niya da yanzu ba wannan maganar ake ba." Bebi baice komai ba kawai ya Wauki key Win motar sa da wayar sa ya fita, suka  sake yin dariya ba kamar Huzaifa da yake tunzura shi da gangan.

       ********* Mujahid da yake jira Lubna tayi magana yace, "Ina jin ki Sweet, kin ce min zamu yi magana yau kuma gashi na zo amma kin kasa cewa komai." Lubna ta kalle shi ta kalli titin da yake gaban su tace, "Yaya Bebi ya kai ™ara ta wajan Abba a kan ka, Abba kuma yace babu ni babu kai."  Ta faWa murya tana rawa sosai.

"Innalillahi! Meyasa Adnan baya sona ne? Me na aikatawa wannan bawan Allah baya ™aunar farin cikina?." Jin a yadda yayi maganar cikin tashin hankali da ruWani Lubna tace, "shiyasa na amince da shawarar ka, hakan shine mafita kawai a cikin lamarin mu."

Mujahid ya girgiza kai yace, "ki bar wannan maganar, bakya so baki amshe ta ba tun farko gwara a dakatar da ita kawai. Bana son mu aikata abinda zuciyar ki take rawa a kai, gwara a ha™ura tunda kina ganin kamar zan cutar dake ne." Lubna tace, "yanzu na karSi shawarar hannu biyu, na fahimci itace mafita bamu da wata hanya bayan ta ita."

Ya kalle ta ya raunana murya yace, "da gaske ki ke?." Ta Waga kai alam1n eh ya sauke numfashi yayi shiru kamar mai tunani kafin ya kalle ta yace, "Kin shirya?." Ta Waga kai alamun eh ya kulle ido ya buWe ya sake cewa, "zan tambaye ki wani abu ki bani amsa duk yana cikin mafitar da nake nemar mana, kar ki manta ni likita ne." Ta Waga kai alamun to yace, "yaushe ki ka gama period Win ki?." Lubna tayi shiru alamun tunani kafin tace, "na manta, amma kamar za'a yi sati biyu." Ya girgiza kai yace, "okay. Yaushe ki ke tunanin zamu aiwatar da neman mafitar ta mu? Bana so a Wauki lokaci gaskiya."

Lubna dai zuciyar ta bugawa take amma ta daure tace, "ko yau ma." Murmushi yayi yana mata wani irin kallo na kin shigo hannu yarinya yace, "bai yi kusa ba?."

"Bai yi ba." Ya sauke numfashi yana lumshe idanun sa ya kalle ta yace, "amma kamar kina jin tsoro, yanayin maganar ki ya nuna hakan." Ta sauke numfashi tace, "ban san meyasa nake jin hakan ba."

Yayi murmushi yace, "kar ki damu ni na sani." Kallon sa tayi sai ya sake yin murmushi yace, "eh na sani." Kawar da kanta tayi zuciyar ta ta rabu biyu akan lamarin, Sangaren dama tana hanata aikatawa, Sangaren haggu kuma tana tabbatar mata da hakan ne ya kamata, hakan ne zai bata damar mallakar masoyin ta. Wannan tunanin ya rinjayi na farkon hakan ya saka ta kulle ido tayi shiru. Ganin tayi shiru  bata cewa komai ya saka yace, "yanzu ya mu ke ciki?."

"Abinda kace." Mujahid yace, "mu wuce kawai?." Kai ta Waga alamun eh kafin tace, "ina zamu je?." Yace, "Gidana." Jin abinda yace sai tayi shiru ya kunna motar suka nufi gidan sa kai tsaye, shi kansa zuciyar sa rawa take yi akan lamarin amma bazai rasa wannan damar ba.

******** Bebi koda ya bar gidan Hamza hanyar gidan su Manal ya bi haka nan yake son ganin ta ko zai ji sau™in Sacin ran da yake zuciyar sa, daga can baya ya tsaya yana kallon layin su ko zai ganta amma babu ita babu alamun ta.

Lumshe ido yayi ya Wauki waya ya kira ta bata Wauka ba ya sake kira sai a lokacin ta Wauka da sallama. Bai amsa sallamar ba ya yi shiru zuciyar sa na bugawa sosai, shau™in soyayyar ta yake ji yana fizgar sa zuwa  gare ta, daWin sallamar da tayi sanyi yaji a zuciyar sa lokaci Waya hakan ya saka ya kasa cewa komai. Manal jin yayi shiru tace, "Baka jina?." Numfashi ya sauke murya a can ™asa yace, "Manal I'm in love with you so much, kin san da hakan?."

Jin abinda yace sai tayi murmushi tace, "ko sallamar baka amsa ba." Ya sake lumshe idanun sa yace, "ki gaishe da Mama."

"Zata ji." Ta faWa murya a sanyaye sai ya murmusa shima yace, "what wrong?." Manal tace, "babu komai." Yace, "akwai abinda zaki ce."

"Babu komai, a gaishe da Mummy."

"Bayan kin ™i zuwa wajan ta." Manal tayi murmushi tace, "Zan je."

Bebi matu™ar daWin magana da ita yake ji hakan ya saka ya gyara zama yace, "Yaushe?." Manal tace, "ko yaushe."

"Ba zuwa zaki ba." Kafin tayi magana ya rigata yace, "zan bada sa™o a kawo miki anjima, zan je asibiti yanzu." Ta amsa tana cewa, "Asibiti dai." Bai ce komai ba yayi murmushi ya karshe wayar yana Jin zuciyar sa abinda yake ji ya ragu sosai ya ja motar sa ya tafi.
Chapter 13 · 0% Book details