← Book details Baya Da Kura Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 50

Sashe 44

Baya Da Kura Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Manal tace, "in sha Allah babu wanda zan faWawa har Mama, kuma ni na yafe ma." Yayi murmushin takaici jin abinda tace zuciyar sa na hasko masa mata irin ta nawa aka kai masa, zuciyar sa na hasko masa wata™ila kokawa suka yi da Manal Win ta gudu bata bashi haWin kai ba. Wani irin takaici yaji bai san ya runtse ido ya furta, "hasbunallah!." Ya sauke numfashi mai ™arfi yana ji kamar ya zubar da hawaye. Wai mahaifin ka ne yaso lalata matar da ka ke aure, wanne irin abin kunya ne wannan? dole yaji Waci a zuciyar sa Wacin da bai yi tunanin zai taSa jin irin sa a duniya ba.

Sum-sum Manal ta tashi ta fita cikin nauyi da jin kunya, sai da ya nuna hoton mata Abban a waya take ganin kamar sa da Mimi da kuma Yaya Farida wanda a baya bata gani ba. sai a lokacin lura har shi Adnan Win suna yanayi da Abban, kawai yafi kama da Mama ne. Salati kawai take a zuciyar ta domin kuwa ko sakin ta Bebi yayi a jiya baza ta ga laifin sa ba dan irin kalaman da tayi amfani dasu wajan zagin mahaifin sa masu muni ne.

Haka Bebi ya kwana biyu babu walwala ko aiki baya zuwa mgagana ma ba sosai yake yiwa Manal Win ba balle a zauna su yi hira kamar yadda suka saba. A cikin kwanakin sai da ya tabbatar ya gano inda mahaifin sa yake zama ya kuma tabbatar da batun Manal gaskiya ne babu ™arya a ciki mahaifin sa neman mata yake yi yara da anya, ´an bariki da wanda shine yake zama silar fara barikin nasu.

Su Huzaifa da Mummy babu wanda bai tambaye shi abinda yake damun sa ba amma sai yace babu komai. Manal kam sai dai ta bi shi da ido ko abinci baya iya ci ko ta dafa, ™o™arin da take yi ta san yana son kunu sai ta dama ta zuba masa a flasks shi kawai yake sha sai abinda baza'a rasa ba.

Ranar asabar da yamma ranar yaji sau™in zuciyar sa saboda addu'ar da yake yi a kan lamarin, ya shiga Wakin ta ya same ta a zaune tayi shiru alamun tunani take yi ya kalle ta yace, "Manal ki shirya zamu je mu gaida Abba." Gaban ta ya faWi sosai ta kulle ido ta buWe ta girgiza kai alamun to daga nan ya fita.

Kaya ta canja ta saka lace Winkin doguwar riga butterfly ta yafa mayafi a kanta ta fito falon a lokacin ya shirya shima yana tsaye yana jiran ta, ya kalle ta sai ya Wan saki fuska kaWan yace, "kin yi kyau." Murmushi tayi bata ce komai ba suka fito suka shiga mota zuwa gida.

Shi kansa ™irjin sa bugawa yake yi baya son haWuwar Abba da Manal, baya so Abba ya gane ta balle ya tuna abinda ya faru a tsakanin su, in hakan ta kasance bai san wacce irin kunya zai ji ba.

Yana faka motar wajan Mummy suka shiga da sallama ta amsa tana bin su da kallo tace, "Bebi ku ne tafe?." Ya amsa suna gaisawa kafin yace, "Mun zo mu gaishe da Abba."

"Ya kamata kam, tunda akayi auren ku baku gaisa ba. Ai yana falo ku je kar ya fita sai ku dawo nan Win in Kun gaisa." Jiki a sanyaye ya tashi Manal ma ta tashi suka fita, Mama ta bishi da kallo da tunanin abinda yake damun sa, dan yau ta yi kuWurin sai taji abinda yake damun sa duk kauce-kaucen sa.

Abba yana zaune yana waya suka shiga da sallama ya amsa yana ajjiye wayar yana cewa, "Adnan ni da na ce zan zo da kaina sai ku ka riga ni?." Bebi yayi murmushin ya™e ya zauna a kan carpet kana yace, "Mun hutar da kai zuwan." Manal kanta na ™asa bata Wago kai ba suka gaisa da Abba, ta tabbatar bai ga fuskar ta ba dan kanta na du™e sosai. Abba ya amsa da fara'a yana tambayar ta mutanen gidan su da yanayin zaman nasu tace Alhamdulillah.

Ta™aitacciyar nasiha yayi musu duk ba jin sa suke ba saboda hankalin su baya jikin su, kowa da tunanin da yake hakan ya saka har ya gama maganar bata ji ba sai gani tayi yana mi™o mata kuWi, a nan ta fahimci ya gama faWar abinda yake cewa. ta saka hannu biyu ta karSa tayi godiya shima Adnan Win ya gode Abba yace, "Wazu Mimi ma da mijin ta suka zo." Bebi yace, "ai dole, baka nan akayi biki gabaWaya."

"Bari kawai, abubuwa sun min yawa ne sosai." Bebi yace, "Allah ya taimaka." Ya amsa da amin kafin yace, "lafiya dai ka ke?." Ya amsa da Lafiya lau daga nan suka koma wajan Mummy.

Manal ta takura saboda yanayin da take ciki, gashi su Kausar basa nan, ga Mummy ta shiga Waki shi ma yabi bayan ta, gabaWaya zaman ya ishe ta kawai daurewa take. A haka ta zauna tayi shiru ta rasa abinda zata yi taji daWi.

Yana shiga Waki wajan Mama tace, "Bebi me yake damun ka? A karo uku nake tambaya." Bebi yace, "Mummy babu komai fa."

"˜arya ka ke. Ka faWa min abinda ya faru har ka koma wannan yanayin."

"Mummy babu komai fa, kawai yanayi ne."

"Hmm Adnan kenan, na haife ka kace zaka min ™arya dan ka Soye min damuwar ka, kawai baza ka faWa min abinda yake faruwa bane. Kuma na Lura damuwar ka ta shafi matar ka, itama yadda jikin ka yake a sanyaye itama haka, bata da walwala kamar yadda ku ka saba zuwa, gabWaya a Warare take. Na san halin ka Sacin ranka na shafar kowa na kusa da kai haka damuwar ka, to kar ka shiga ha™™in ta, kar hakan ya saka ka canja mata saboda wani dalili na ka, damuwar ka taka ce kai ka Worawa kan ka, in damuwar ka ta shafe ta ka shiga ha™™in ta."

Bebi ya girgiza kai yace, "babu abinda yake damuna Mummy."

"Kai dai ka sani" ta faWa tana fita daga Wakin. Ya fito shima ya kalli Manal da take zaune yace, "zan je asibiti na dawo." Ta amsa da to ya yiwa Mama sallama ya fita.

Mummy ta kalle ta cikin nutsuwatace, "me yake damun ku gabaWayan ku ne Manal?.Ke a cikin damuwa shima haka, na damu da yanayin ku ba haka ku ka saba zuwar mana ba."

Manal ta sauke numfashi tace, "Mummy ni babu abinda yake damuna, shine dai ban sani ba in na tambaya sai ya ce babu komai."

"Kema hakan yake ce miki kenan? Bebi akwai rainin hankali." Manal tayi shiru bata ce komai ba Mummy tace, "Allah ya kyauta. Yau kin zo abokan hirar taki basa nan naga duk naga kin takura."

Manal tayi murmushi kafin tayi magana Mama tace, "Akwai zoSo mara sugar da na yiwa Abban su a fridge in zaki sha yana ciki sai ki Wauka, akwai abinci ma a kitchen in kina jin yunwa." Manal tace, "to Mummy." Hira suke yi kaWan-kaWan, Mummy tana so ta Webe mata kewar su Kausar ita kuma nauyin Mummyn take ji, ba laifi ta sake da Mummy kafin Mummy ta shigaaki.

Maryam ce ta shigo da sallama Manal ta amsa suka gaisa kafin tace, "Ina Bebi?."

"Ya tafi asibiti." Maryam tace, "Shikenan bara na kira shi a waya" ta faWa tana fita Manal ta Wauki waya tana dannawa cikin rashin sanin abinda zata yi. Mummy ta fito daga Wakin tace, "Manal in kin gaji da zaman shiga Waki ki kwanta, wannan tafiya asibitin na sa ya kai dare bai dawo ba." Manal ta amsa da fara'a tana jin daWin yadda Mummy take ke yi mata kamar ba sirikar ta ba.

A can asibitin ma ko wajan su Huzaifa bai je ba a office yayi zaman sa sai dai ya shiga nan ya fita nan bai bar asibitin ba sai bayan i'sha ya dawo gidan Mummy ya Wauki Manal suka tafi gida.

A ™ofar gidan sa ya ga Huzaifa da Hamza suna ™o™arin shiga da alama sun Wauka yana nan. Ya shiga da motar sa gidan ya faka motar Manal ta shiga ciki bayan suma sun shigo harabar gidan. shiga babban falon nasa suka yi suka zauna. Manal ta kawo musu ruwa harda lemo da cake Win da tayi masa bai ma kalle shi ba saboda damuwa. Bayan barin ta wajan Hamza ya kalle shi yace, "Bebi baka Soye mana damuwar ka, dukkan mu bama Soyewa juna damuwar junan mu, me yake damun ka ka koma haka har ya shafi aikin ka?."

Huzaifa yace, "damuwar ka ta saka mu a damuwa, bamu taSa ganin ka cikin wannan yanayin ba. Dan duk damuwar da ka ke ciki bata hana ka aiki, wannan ta hana ka aiki Hakan ya tabbatar mana da ba ™aramin abu bane ba. Me yake damun ka?." Bebi ya sauke numfashi yana kallon su yace, "babu abinda yake damuna, kawai yanayi ne yake kawo hakan amma ba wani abun bane."

Hamza yace, "Yanayi fa kace? Babu wani yanayin da ya taSa saka a wannan damuwar, ko lokacin damuwar Lubna baka shiga wannan damuwar ba balle yanzu. Kawai baza ka faWa mana abinda yake faruwa ba ko hankalin mu zai kwanta."

Ya sake kallon su yace, "Ba haka bane Hamza, kawai dai abubuwa ne sun fita daga raina, sai dai a hankali kawai." Huzaifa yace, "Shikenan, Allah ya yaye maka. Daman damuwa da damuwar ka ce ta saka mu zuwa dan mu ji lafiyar ka shirun naka yayi yawa."

"Na sani, na gode kuma Allah ya bar zumunci."

"Amin. Hamza tashi mu je" ya faWa yana tashi tsaye sai kuma ya kalli abinda Manal ta ajjiye yace, "sai naci dan ya burge ni." Bai ce komai ba ya Wauka zai fita Manal ta fito da hijjabi tace, "Yaya Huzaifa Mama ta faWa min ka sake canja mata da magani har gida, na gode sosai Allah ya bar zumunci."
Chapter 44 · 0% Book details