← Book details Baya Da Kura Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 50

Sashe 22

Baya Da Kura Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"0n dai ba lahira ya tafi ba sai na saka an hukunta shi wallahi, in dai ina sa rai sai yayi zaman prison. Ni zai yiwa wannan rashin mutuncin har gida? ³ar da na haifa ita zai yiwa fyaWe?.

Yaya Bilal yace, "Abba babu hujjar da za a kama Mujahid saboda laifin fyaWe, ba kokawa suka yi da ita ba, ba sace ta yayi ba, ba wani magani ya bata ba, da kanta da amincewar ta taje har inda yake. Kaga wannan ba irin fyaWen da za a yiwa wanda ya aikata hukunci bane. Da amincewar ta bamu da hujjar da zamu ce ya yi mata fyaWe.

Ran Abba ya sake Saci sosai, ™unar hakan yake ji a zuciyar sa yace, "ni ta tozarta kenan? Ni ta Satawa suna a duniyar nan?. Na hanata kula yaro amma da yake bata da mutunci ta Wauki ™afa ta bi shi har gidan sa ta bashi kanta da sunan neman mafitar auren ta.

Shiru suka yi dan sun lura abin ya yiwa Abba ciwo sosai ya sake cewa, "a tunanin ta an hana ta auren sa ne saboda jin daWin mu ko kuma saboda haka muka ga dama ko?" Ya kalli Mamy yace, "duk laifin ki ne, da baki bata goyan baya ba da yanzu hakan bata kasance ba, da kin nuna mata kuskuren ta kamar yadda muka nuna mata da wata maganar muke yi ba wannan ba. Sai kika sakawa idanun ki toka da wani kishin banza da wofi kika ce ke Adnan bai isa da yaran ki ba saboda ba uwa Waya su ke ba, gashi yanzu da matsalar da ake gudar muku ta faru shine dai yake ™o™arin gyarawa. Girman ki bai amfana miki da komai ba, tunda bakya tunani kafin ki aikata abu. A nan wajan kika dinga cewa akwai banbaci tsakanin Mimi da Lubna, su gashi da ya isa dasu in yace kar ayi basa yi gasu nan lafiya lau basu da wata damuwa. Yanzu wannan riba kika samu ko akasin ta?."

Kowa yayi shiru dan tabbas da laifin Mamy a lamarin itama bata ce komai ba dan ta san da laifin ta, Abba ya sake yin tsaki zuciyar sa zafi take masa sosai, bai san haka iyaye suke ji a duk lokacin aka lalata yaran su ba sai yanzu, bai san haka abin yake da ciwo sosai ba sai da ya faru akan jinin sa. Bai san haka ake jin zafi da raWaWi ba sai yanzu da aka yiwa ´ar cikin sa fyaWe.

Bebi yace, "Ha™uri za'a yi, komai ya riga ya faru itama ta gane kuskuren ta nan gaba baza ta sake aikata hakan ba. Don Allah Abba kar kace zaka mata faWa, nasiha da nuna mata kuskuren ta shine ya dace da ita ba faWa ba, kuma don Allah maganar nan ta tsaya a nan kar ta fita waje."

Abba a fusace yace, "ita zan tsaya na yiwa nasiha? To nace mata me? Nace mata kin ga abinda kika aikata abinda ya jawo miki ko?" Ya girgiza kai cikin fushi yace, "Wallahil azim da na ganta a yanzu babu abinda zai hana ban mata dukan tsiya, da girman ta ai da kuma hankalin ta taje ta aikata saboda cikar burin. ³ar da na haifa ace na yi mata umarni ta™i ji ta tsallake taje wajan saurayi har cikin gidan sa? Saurayin ma wanda na hana ta kulawa?. Adnan wa™a ka ke so nayi mata?."

Adnan ya fahimci ciwon Abban yace, "dukkan mu mun san tayi kuskure, kuma ko a nan ta fahimci illar ™in bin umarnin ka da tayi. Don Allah Abba kayi ha™uri, Ina baka ha™uri a madadin ta, ita kaWai tasan abinda take ji a zuciyar ta ,Abba don Allah ka sassauta mata."

Abba yace, "ka ke zancen kar kowa ya sani to abin arzu™i ne da za a faWawa mutane? Mtswwwww!. Kana ta maimata tafi kowa jin zafi a zuciyar ta uban waye ya kai ta? Ba ita ta kai kanta ba?. Dukkan su sun yi shiru babu mai magana a cikin su, shi dai Bebi a gajiye yake dauriya kawai yake yana magana kan sa ciwo yake yi saboda ya gaji.

Abba ya kalli Mimi da Kausar da suke gefe Kausar sai hawaye take yi yace, "gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah." Sunkuyar da kai suka yi basu ce komai ba. Kiran sallar magriba ne ya saka taron ya watse matan suka yi cikin gida mazan suka tafi sallah.

Bebi yana dawowa wajan Mama ya shiga ya same ta a zaune kamar ko yaushe an kunna haya™in turaren wuta wanda aka kawo na bikin Mimi ana gwada ™hamshin sa, dafe kai yayi yace, "Wayyo Allah!." Mama tace, "Au, yi ha™uri bamu Wauka zaka shigo yanzu ba. Farida maza ki kashe haya™in." Ruwan hannun ta ta zubawa wutar hannun sa yana kansa yace, "Mummy ba wani abinda zan ci?."

Mama tace, "sai dai a dafa maka bamu yi girki ba yanzu."

"Barshi kawai, ban san ma abinda zan ci ba." Mama tace, "Nima cake Win budurwar ka naci." Sai a sannan ya tuna ma da cake Win sai kawai ya juya ya fita.

Maryam yaji tana yi masa magana ya juyo tace, "jikin Lubna zafi Bebi, Sai kuka yake wai kanta zai cire."

"Subahanallahi!" Ya faWa da sauri yana yin hanyar Sangaren su ya shiga har Wakin Lubna ya same ta a kwance sai rawar jiki yake yace, "Lubna Sannu." Jin maganar sa sai ta kalle shi tana hawaye yace, "sau nawa zance miki ki daina kuka ne wai? An faWa miki shine maganin damuwar ki?. Na maimaita na sake faWa miki ki daina kuka amma bakya jin magana ko?" Ya faWa cikin faWa yana kallon ta fuskar sa a haWe.

"To Yaya na daina!" Ta faWa tana share hawayen ta, ya taSa jikin ta yaji zafi sosai bai ce komai ba sai ya juya ya fita bai jima ba ya dawo da allura yayi mata a jijiyar hannun ta ya fito daga Wakin ya kalli Mamy yace, "Mamy damuwa ce ba wani abun ba, amma zata dawo daidai in sha Allah" ya kalli Maryam yace, "Don Allah a samu tayi wanka in ta farka, zata ji daWi sosai." Kai ta Waga dan ita jikin ta ya gama yin sanyi, yadda Abba ya dinga faWa akan Lubna budurwa kuma fyaWe aka yi mata Ina ga ita in yaji abinda take aikatawa? Lallai dole ta samo mafita.

BD˜B2P013

Bebi yana fita Waki ya koma yayi wanka lokacin ake kiran sallah bai fito ba a Waki yayi sallah, bayan ya  idar ya Wauko cake Win wajan Manal a fridge yana ci.

Tunawa yayi bai kira Manal ba ya Wauki wayar sa ya kira ta amma bata Wauka ba, ya sake kira bata Wauka ba sai ya ™yale ta. Ba'a jima sosai ba ya kira kiran yana gab da zai tsinke ta Wauka kafin yayi magana tace, "na damu da damuwar ka shiyasa na kira ka tun da farar safiya naji ya ka kwana ya ka tashi, amma baka tashi kira na ba sai yanzu bayan na san ka gani, ka san a yadda na wuni kuwa? GabaWaya tunani nake ke ko wani abun ne ya same amma kai ko a jikin ka ko?" Yadda take masa maganar kamar zatayi kuka ya saka shi murmushi mai sauti zai yi magana tace,

"Okay, dariya ma na baka kenan ko? Shikenan to sai anjima" tana faWa ta yanke wayar bata bashi damar magana ba. Dariya yake yi cikin nishaWi yace, "Manal rigima, bata tsaya ma taji abinda zan ce ba."

Yana Wago kai suka haWa ido da Rumana da take tsaye tana kallon sa, ya kalle ta ya rausayar da kai yace, "kina son shigowa wajena babu sallama babu neman izini, ban san dalilin hakan ba." Rumana tace, "nayi sallama baka ji ba kana waya." Ya Wauke kai hawaye suka sauko daga idanun ta, soyayyar sa kullum yawa take a zuciyar ta amma ta lura shi da gaske yanzu ya manta da ita. Ido ta goge sannan tace, "Daman zuwa nayi na faWa maka abinda nake ji ko zaka iya faWa min abinda yake damuna."

Nuna mata wajan zama yayi ta zauna yace, "Ina Jin ki." Rumana murya a raunane tace, "Ina fama da ciwon ™irji sosai, Sai naji yayi min nauyi ko magana bana so nayi. Yana min zafi wajan musamman side Win heart Wina, ko numfashi na ja zafi yake min, kuma zuciyata na bugawa da saurin da ya wuce ™a'ida. Sannan in ina kwance ina wahalar yin numfashi sai na tashi zaune

Kallon ta yake yi ido cikin ido tun ba yanzu ba ya fahimci damuwar da ta sakawa ranta zata iya bata matsala, janye idon sa yayi yace, "damuwa ki ka sakawa zuciyar ki shiyasa, inda zaki cire damuwar zuciyar ki abinda ki ke ji zai ragu." Rumana tayi murmushi tace, "damuwa ta bazata iya fita daga raina ba Beb."

"Kin gab da kamuwa da ciwon zuciya" ya faWa yana kallon ta a nutse. Hawayen idanun ta suka sakko kan kuncin ta tace, "na Wauka ma na kamu Win."

Bebi shi baya son kuka, Waga masa hankali yake yi in yaga ana na yi, baya so yaga ana kuka ko kusa hakan ya aka ya sake sassauta murya tace, "wacce damuwa ki ka sakawa zuciyar ki haka? Ki faWa min as your childhood friend."

"Soyayya ce, ban Wauka tayi min wannan kamun ba sai yanzu da nake gab da rasa abinda nake so. Wallahi Beb zaafin da nake ji a raina Allah ne kawai ya sani, Ina son shi son da ban san iyakar sa ba, ji nake in wata ta aure shi ba ni ba mutuwa zanyi."

Ya shafa fuskar sa ya kalle ta sosai yace, "waye yace miki yanzu ana saka soyayya har haka a zuciya Ruman?." Gaban ta sai faWuwa yake yi saboda tsananin son sa take masa tace, "bani na sakawa kaina ba Allah ne."
Chapter 22 · 0% Book details