← Book details Baya Da Kura Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 50

Sashe 14

Baya Da Kura Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

****** Maryam kuwa bayan ™arfe biyar na yamma ta fita napep ma ta hau saboda kar ma a gane ta kai tsaye guest house Win ta nufa kamar yadda yace. Tana shiga ta same shi a falo yana kallon ball cikin nishaWi yana ganin ta sai ya tashi tsaye yace, "Barka da zuwa Masoyiya a bar ™auna."

Maryam tana kallon sa cikin rashin walwala tace, "gani, me kake so dani?." Ya bita da kallo yace, "abinda nake so a bayyane yake ai Maryam, kece ki ke gardama da hakan bata faru ba. Da yanzu mun wuce wajan amma sai dawo da hannun agogo baya kike."

"Ka bani mamaki Kamal, ashe daman zaka iya amfani da tsaraicina wajan tozarta ni?."

Yayi murmushi mai sauti yace, "Ba tozarci bane, soyayya ce."

"Wannan ba soyayya be ce Kamal" ta fada cikin tsawa tare zama a kan kujera tare da dafe kanta. Ya zauna kusa da ita yace, "kar ki wani damu wannan ba abin damuwa bane." Ta kalle shi tana hawaye yace, "meye na kukan kuma?."

Maryam tace, "gida zan tafi, ka faWa min abinda zaka ce."

"Ai na faWa miki ki zo da shirin kwana."

"Ni ba karuwa bace ka sani."

"Nima ba Wan iska ba ne kin sani."

"Ka canja daga yadda na san ka. Don girman Allah, don darajar annabi, don darajar iyayen ka, don darajar yaran da muka haifa ka bar wannan maganar Kamal, ka ajjiye ta a gefe na tabbatar maka zan yi auren kisan wuta nazo na aure ka, wallahi zan bi ko wacce hanya wajan ganin na dawo gidan ka matsayin matar ka. Ka rufa min asiri ka adana wannan hotunan ko dan darajar haihuwar da muka yi, tsaraicina ne in ya fita na gama tozarta a duniya, ™arshen tozarci a duniya a yaWa hotunan tsairaicin ka. Don Allah kar ka yi min haka, ni tsohuwar matar kace da muka yi zaman lafiya ™addara ta raba mu, ka yi min rai ka fasa aiwatar da hakan don Allah."

Kamal yace, "na faWa miki bazan yi posting hotunan amma sai kin amince dani mun kwana yau kamar lokacin da kike gidana, hakan yana faruwa ni kuma zan goge." Ta rausayar da kai tace, "yanzu baza ka goge ba sai nayi zina da kai? A wancan lokacin na Wauka tura maka hotunan tsaraicina soyayya ce ashe wannan ranar ka ke jira?." Yayi murmushi yace, "Ki daina wannan maganar Maryam, ki amince da abinda nake so in ba haka ba wallahi sai ´ar ki taga video nan."

Maryam ta lumshe ido jin bazai saduba ba ita kuma bata san me zata ce, bata san abinda zata yi ba, bata san abinda zata aiwatar ba a wannan lokacin. Yanzu me zata yi?saSon Allah ko martabar ta da ta yaran ta?. Ganin ta tafi tunani sai ya tashi ya shiga ciki yace, "in kin shirya ki same ni" ya faWa yana barin wajan ta bi shi da kallo zuciyar ta na zafi sosai ta sake fashewa da kukan da bashi da amfani a yanayin da take ciki.

******* Rumana da ™awar ta suna zaune a mota a ™ofar gidan su Manal ta kalle ta tace, "da gaske ki ke nan ne gidan su?." ˜awar ta mai suna Zuby tace, "ai bazan miki ™arya ba, nan ne." Rumana ta sake kallon gidan tace, "kalli gidan fa." Zuby tace, "ni na kawo ki gidan ai, ™arshen kenan." Ta girgiza kai tana sake kallon gidan tace, "ni na Wauka wata ´ar masu kuWi ce ko ´ar masu sarauta ashe a nan ya ™are?." Zuby tayi dariya tace, "a ganin ki su talakwa ne amma ba haka abin yake ba, suna da rufin asiri sosai fiye da tunanin ki. Iya sutturar da suke sakawa a nan zaki tabbatar da su Win ba talakawa bane, dan zan iya cewa abayoyin da yarinyar take sakawa ke baki dasu. Tafi saka hijjabi da abaya, ke in kika ga abayar jikin ta wani lokacin sai kin yi mamaki. Wannan dalilin ya saka kai tsaye in kika ganta baza ki ce a nan take kwana ba."

Manal Win ce ta fito a lokacin sanye da hijjab jalbab kalar ja yayi mata kyau sosai ya haska milky face Win ta Zuby tace, "Gata nan, sunan ta Fatima amma Manal ake ce mata saboda sunan Maman ta ne da ita. Bata da wasu shekaru sosai, tana da kirki da yawan fara'a. Fannin karatu a secondry school ta tsaya, amma da yake private school tayi in tana turanci zaki Wauka wata mai ilimin gaske ce. Itace wacce Bebin ki yake so." Sake wara ido take a kan Manal lokacin da take karSar sa™on da Bebi ya turo mata ba tare da ta san dasu ba, sake kallon ta Rumana take daga sama har ™asa ta kalli Zuby tace, "wannan farin na ta ni kaWai nake gani?."

Zuby tayi dariya tace, "ba ke kaWai bace ba, haka kalar ta take, fara ce ita ba farin gama garin fari irin na ku ba. Shiyasa ´an makaranta su suke mata take da milky beauty saboda wannan hasken nata yayi kama da madara. Kallo Waya zaka yiwa wannan hasken ya Wauki hankalin ka, in ka tsaya ka nutsu kana ganin ta a lokacin zaka hango ™aramin bakin ta wanda yake ja sosai kamar na larabawa."

Rumana jikin ta yayi sanyi tana kallon Manal a lokacin da ta shiga tace, "Zuby shiyasa Yaya Bebi baya ta ni yanzu, kalli wacce ya Wauko fa?. Ga kyau, ga hasken da ni mace ma ya burge ni balle shi, ga idanu, ga bakin ta mai kyaun gani, gata mai ™arancin shekaru. Ta ya zai saurare ni yana ganin ni kusan sa'ar sa ce?." Zuby ta tausasa murya tace, "bata fi ki kyau bafa Rumana, wannan hasken ne ya saka ki ke ganin kamar ta fi ki, amma tsahon hancin ki yafi nata."

Rumana tace, "ta ya zaki ce haka? Kalle ta fa?." Zuby tace, "Yayarta ta fita kyau ni a idona, ita kawai wannan hasken nata ne yake da Waukar hankali." Rumana ta kalli Zuby tace, "gadon kyau suka yi?." Zuby tace, "Maman su kyakykyawa ce sosai, dan naji ance ana tunanin halfcast ce, a wajan ta suka gado wannan kyaun. Duk da bata da wannan hasken wata™ila ita Manal Win a wajan baban su ta gado wannan hasken."

"Zuby a haka ma babu hutu fa kenan, in ta samu hutu wanne irin haske zata sake yi?."

"Ke dai tunda zai aure ki ai shikenan, kin takura an nemi miki ita gashi kin ganta kina kishi."

Ruamana tace, "Dole nayi kishi Zuby" ta faWa tana sake kallon ta inda Manal take taga bata wajan. Rumana tace, "wannan fa daga asibitin su Bebi yake, ga logo Win asibitin nan a bayan rigar sa, duk yadda aka yi shine ya bada wannan sa™on a kawo mata. Zuby Bebi ya iya soyayya, Bebi ™arshe ne wajan soyayya, iya kallon da zai miki na soyayya shi kaWai ya ishe ki balle ya buWe bakin sa. Soyayya yake yi hankali, a nutse yake gabatar da ita babu shirme balle wani abu na banza, soyayya yake da zuciya Waya in yana so kawai yana so. Tun a lokacin baya na shaida baya wannan haukar soyayyar balle yanzu da ya sake hankali. Ina kishi da hakan sosai Zuby."

Zuby tace, "ki yi ha™uri haka Allah ya yi."

"In ya auro yarinyar nan zan iya samun ciwon zuciya, domin yana da kamar ta ne zai yi dani bazawara?." Sai ta bawa Zuby tausayi tace, "Yana son ki fa, ke ya fara so babu ruwan sa da kin taSa aure wannan soyyayar na zuciyar sa, ke kin san meye first love?." Murmushi kawai tayi tace, "mu tafi kawai Zubaida." Zuby ta kunna mota taja suka tafi zuciyar Rumana sai bugawa take yi.

                     Bayan kwana biyu.

Tana tsaye tana amsa waya a banWaki murya ™asa-™asa tace, "to ba kaine kwana biyu baka min waya ba, ba dole na Wauka ka manta dani ba." Daga can Sangaren yace, "haba ni na isa nace na manta dake? Abubuwa ne suka yi min yawa shiyasa. Yanzu yaushe zamu haWu?."

Mubeena  tace, "ni na gaji da wannan abun, kawai kazo gidan mu ayi maganar aure a wuce wajan. Kana gani ™anwata har an kusa bikin ta amma kai ko yaushe zancen ka a ina zamu haWu, ka san bana kula kowa sai kai." Yayi murmushi yace, "har yanzu bamu gama fahimta juna dake ba ta ya zamu fara batun aure?."

"Me baka sani ba a kaina? Ni dai kawai ka turo indai kana sona."

"Shikenan Baby, amma kafin nan ina so mu haWu mu yi magana."

Mubeena tace, "na faWa maka ba'a barina fitowa." Yace, "ki san yadda za ki yi ki fito sai ki min waya so nake mu yi maganar sosai." Mubeena tayi ajiyar zuciya tace, "ko yanzu ne na fito?."

"Eh mana Baby, in kin samu kin fito ki faWa min." Mubeena bata ce komai ba ta kashe wayar ta fita taga Manal bata nan sai Mama kawai itama bacci ya Wauke ta kasancewar lokacin aka idar da sallar azahar.

Ganin ta samu dama sai ta saka mayafi ta fita daga gidan da sauri. Sai bayan ta bar unguwa ma sannan ta yi masa waya ta faWi a inda take, ba jimawa ya turo da driver ya Wauke ta aka wuce da ita gida yake dan ba gidan da suka saba haWuwa bane wani ne daban da ya canja.

BD˜B2P009

Mubeena lokacin da ta shiga gidan a zaune ta same shi ganin ta sai ya murmusa yace, "barka da zuwa Baby." ˜arasowa tayi ta zauna nesa dashi tace, "bana son zuwa gidan nan, in dai kana sona kayi abinda nace kawai shine mafita a gare mu, yawan ganina da ake a nan yanzu sai ayi min fassara ta daban." Murmushi yayi shi wallahi dariya ma take bashi, ko faWa mata akayi ya shirya aure oho mata.

Kallon ta yayi yace, "har yaushe muka saba da zaki dinga batun aure? Ko Abuja baki raka ni ba fa har yanzu." Mubeena ta kalle shi tace, "Sai na raka ka Abuja zaka aure ni?." Ya girgiza kai alamun a'a yace, "at least yana da kyau mu fahimci juna sosai kafin maganar aure tazo tsakani."
Chapter 14 · 0% Book details