← Book details Baya Da Kura Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 50

Sashe 15

Baya Da Kura Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ba wani fahimtar juna, ™anwata daga haWuwa da saurayin ta kwanaki kaWan har an saka ranar auren su. Ni na gaji in kana sona kazo gidan mu wajan Baba."

Girgiza kai yake ya lura yarinyar nan da gaske take sosai akan maganar auren sai yayi murmushi yace, "to yanzu haka za'a yi auren ba wani lokaci?." Kallon sa tayi tace, "me ka ke nufi?." Ya taso yazo inda take yace, "Haba baby ke fa babbar yarinya ce ya kamata tun wuri ki fahimci inda na dosa, amma sai wani kaucewa ki ke kamar ba ni da ke mu ka Wan taSa soyayya ba kwanaki. So nake soyayyar ta wuce ta ranar mu san junan mu sai auren ya biyo baya."

Mubeena tace, "ban gane ba."

"So nake kawai ki amince dani, ni kuma zan miki duk abinda kike so, har auren mu sai ayi a sati biyu mai zuwa." Mubeena tace, "wacce amincewa?" Ta faWa dan ™irjin ta ya fara bugawa sosai, tsoro ya fara shigar ta haka kawai ba kamar lokacin baya da take rasa tsoron ba. Kallon ta ya sake yi ya ri™e hannun ta yace, "ki bani aron yau kawai, ni kuma na tabbatar miki zan nuna miki so da qauna irin wacce ki ka jima kina neman ta, zan nuna miki soyayyar da film ma ba'a yin irin ta, zan gusar da hankalin ki da soyayya, sannan zan baki duk abinda ki ke so."

Mubeena ta zare hannun ta daga ri™on da yayi mata tace, "Daman abinda ka ke so kenan ba aurena zaka yiba?."

"Haba Baby waye yake ta aure yanzu? Wannan rayuwar itace jin daWi meye baza ki samu ba?, zaki samu farin ciki fiye da wanda masu aure suke samu." Mubeena ta tashi tsaye tana kallon sa cikin tsoro da fargaba tace, "to shikenan baza ka samu abinda ka ke so ba, ni na tafi."

Shima tashi yayi yace, "ki bar wasa mana, hakan ba ajin ki bane." Ta kalle shi tace, "sai an jima." Kafin ta motsa ya ri™o hannun ta yace, "babu inda zaki je, tunda kika zo nan yau sai na karSi abinda na jima ina so. Ko ta lallami ko ta ™arfi."

Ganin da gaske yake fa sai ta fara ™o™arin ™wace kanta amma ta kasa dan ya ri™e hannun ta duka biyun yana ™o™arin haWa jikin sa da nata. Cizon hannun sa tayi ya sake ta da sauri tare da ja baya yana yarfe hannun, da hanzari ta buWe falon ta fita a guje. Cikin takaici ya yun™ura zai bita wayar sa ta fara ™ara ganin mai kiran bazai iya sharewa ba dole ya tsaya ya Wauka wayar ran sa a Sace.

     Mubeena a haka ta fita tana gudu sai da ta Wan yi nisa ta tsaya ta yau napep kai tsaye gidan su Bily ta wuce har lokacin ™irjin ta bugawa yake tsoron ya™i barin ta gani take kamar zai biyo ta. Babu kowa a gidan sai Bily kawai a zaune a akan kujera tana kallo ganin yadda Mubeena ta shigo ya firgita ta ta bita da kallo tace, "ke wani abun ne ya biyo ki?." Mubeena bata ce komai ba ta ™arasa wajan fridge ta sha ruwa ta dawo ta zauna ta dafe kanta bata ce komai ba.

Ganin hakan sai Bily ta share ta cigaba da kallon ta sai da taji alamun kukan da Mubeena take yi sai ta kalle ta tace, "lafiya?." Mubeena cikin muryar kuka da fargaba haWi da nadama tace, "da gaskiyar ki Bily, Alhajin nan so yake ya lalata min rayuwa ba aurena zai yi." Bily ta taSe baki tace, "ba gani ki ke ba™in ciki nake miki ba Mubeena?. Meye abin ba™in ciki a wannan tsohon banzan? Kai da ka gan shi ka san cikakken Wan bariki ne amma kika toshe kunne ki kuWi ya rufe miki ido. Ai duk magidancin ko saurayin da ba zai nemi ganin iyaye ki ba da aure yake son ki ba, duk wanda zai dinga miki zancen yaushe zaku haWu ko yaushe zaki zo inda yake wallahi ba na gari bane, maganar aure ba a gaban sa take ba iskanci ya bawa mahimmaci. Amma ki ka ce ke inaa ai auren ki zai yi."

Mubeena tana kuka tace, "Ya nuna min alamun hakan a baya ban kawo komai ba, amma yau da ya so keta min haddi sai tsoro ya shiga raina, wallahi ban san lokacin da na gudo ba."

"Baki daina zuwa gidan sa ba kenan ko Mubeena? Ke ko tsoro bakya ji a dinga ganin ki kina shiga gidan nan sa kina fitowa?."

Mubeena ta share hawaye tace, "Ina son sa Bily, ina son sa shiyasa duk abinda yace nayi nake yi. Ke kin san daman bani da burin kula samari sai irin su shiyasa haka."

"KuWin sa ki ke so ba shi ba, shiyasa shima da ya lura da hakan yake baki kuWi ya siya miki abubuwa mai tsada saboda ya saka ki saki jiki dashi. Wani irin son kuWi ki ka Worawa kan ki wanda yafi ™arfin shekarun ki."

"Allah ya sani ina son rayuwar kuWi Bily."

"Sai ki yi addu'a Allah ya baki miji mai kuWin halak kuma na gari ba ki fara zuwa gidajen masu kuWi ba."

Mubeena tayi shiru kafin tace, "Yau Allah ya kare ni da yanzu na rasa mutuncina. Nayi dana sanin fara kula shi, nayi dana sanin abinda na aikata tare dashi. Allah ka yafe min." Bily tace, "me kika aikata?." Ta kalli Bily tace, "bazan iya Soye miki ba Bily,Mun yi romancing kwanaki. Bily hannun sa har cikin rigata."

"Baki da hankali wallahi, gabaWaya kan ki dusa ce a ciki bakya ganewa. Idanun ki sun rufe saboda kuWi har bakya gane daidai da ba daidai ba. Hakan ta faru tsakanin ku amma baki daina kula shi ba?." Kuka take yi Bily tayi tsaki cikin fusata tace, "tun daga charting Win da ku ke yi tun farkon haWuwar ku na faWa miki ba na gari bane ba, samari da magidantan yanzu rabi da kwata sun lalace, da namiji yazo zai fara miki hirar banza ko ya fara ™o™arin ri™e hannun ki, in yaga kin bada fuska a ri™e hannu gobe rungume ki zai yi, in yaga ya rungume ki baki Wauki mataki ba jibi zai shiga inda mijin ki kawai Allah ya halattawa shiga. In kuma ya fahimci irin ku ne lashe money da kuWi za'a yi amfani a lalata ki, mazan yanzu kaWan ne na gari. Na karanta miki haka amma baki gane ba sai kike ganin ba™in ciki nake miki, ke yanzu hannun ki ya ri™e yau baki Wauki mataki ba, ya ri™e gobe baki hana ba, jibi ya rungume ki baki nuna bakya so ba, gata zai miki kiss ki nuna hakan daidai ne ba dole a kai ga shafe-shafe ba?. Ya shafa ki kin shafa shi hakan bai saka kin daina zuwa inda yake ba  gani kike soyayaya ce, sai ma Waukar ™afa da kika sake yi yau kika je. Anya kina da hankali?."

Mubeena tace, "nayi nadama Bily."

"Ta banza ce, a lokacin da ake faWa miki gaskiya toshe kunne ki ke yi kike ganin kamar Mama da Baba da Manal basa son ki ne ko kuma sune gidadawa basu waye ba?. Ita Manal haka tayi?. Ita da ta killace kan ta take kula samari na gari ba gashi yanzu maganar aure ta za'a yi ba? Ke ko da ita baza ki yi ko yi ba?. Ko da yake dole Manal ta fi ki samun nasara a rayuwa saboda tarbiyya da biyayya ga mahaifiya."

Mubeena ta goge idon ta tace, "wallahi na daina."

"˜arya ki ke, ko yanzu ya baki kuWi zaki iya kwnaciya yayi abinda yake so dake. Tunda har aka je ga romancing wallahi zaki iya kwanciya dashi Mubeena, ke kika bada fuska da tun farko kin nuna masa ke mai tarbiyya ce da yanzu yaje ya samu Baba da maganar aure, amma sai kika nuna ke ta banza ce ta ya zai aure ki?. Bazan iya ™awance dake ba Mubeena, ki kama gaban ki kawai tunda hakan kika zaSa."

Mubeena tace, "na daina wallahi na daina, haka kawai Allah ya saka min tsoran sa a zuciyata, gabaWaya naji kuWin basa raina a lokacin,  mutuncina yafi min komai. Ki amince dani wallahi nayi dana sani hakan bazai sake faruwa ba."

Bily tace, "har fa hannun sa kika ce a rigar ki, an yi kiss anyi komai abinda ya rage a cika aiki. Amma baki kama kan ki ba kika sake zuwa inda yake, ni tantama nake anya ma komai bai faru ba?."

Mubeena tace, "babu abinda ya faru. Inda ya faru ke kin san bazan Soye miki ba. Allah ne ya kuStar dani kuma nayi nadama zan nemi yafiyar Allah." Bily tace, "in har zuciyar ki ne da kin ji daWi, kuma addu'ar Mama ce ta saka kika kuSta wallahi, itace take kwana tana faWawa Allah damuwar ta a kan ki tunda kullum cikin Sata mata rai ki ke."

Mubeena tace, "Shima na daina daga yau in sha Allah, har wayar da ya bani na cillar da ita a hanya zan yi duk abinda Mama take so. Zan zamarwa Manal Yaya irin wacce take so, in sha Allah zan samu kaWan daga cikin ladan da Manal ta samu. Zuciyata har yanzu bugawa take saboda tsoro."

Bily tace, "da kin kyautawa kan ki duniya da lahira. Baki da kamar Mama da Manal wallahi, na sha yin gulmar ki a raina in naga yadda ki ke girmama Mummy kuma bakya girmama Mama, sai nace wannan yarinyar bata sharar masallaci sai ta coci." Mubeena ta sauke ajiyar zuciya tace, "nayi hankali wallahi yanzu, har zuciyata zan gyara kuskurena, zan bi Mama nayi duk abinda take so. Allah na gode maka da ka bar min Mamana a raye, Allah na gode maka da bata rasu da ba™in cikina ba. ki raka ni na bawa Mama da Baba ha™uri."

Bily ta sauke ajiyar zuciya tace, "Zan je ai tunda kin gyara."
Chapter 15 · 0% Book details