← Book details Baya Da Kura Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 50

Sashe 16

Baya Da Kura Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Amma Bily ina son sa wallahi." Banzar hararar tayi mata tace, "wannan son dashi zai yi amfani ya same ki wallahi a banza ba tare da sadaki da shaidu ba, in dai baki watsar dashi kin manta dashi ba kina tare da wahala. Kuma shi wallahi bazai aure ki ba saboda ya san ke ba ta gari bace ta banza ce, ya riga ya gama latsa jikin ki tun a waje ya za'a yi ya aure ki?. Malama in zaki dage da addu'a ki dage, in baza ki yi ba ke kika sani." Mubeena tace, "zan yi, ki taya ni addu'a." Bily ta amsa ta cigaba da kallon ta Mubeena tayi shiru tana tunani don da gaske tana son sa wallahi.

Bily ta raka Mubeena har gida ta bawa Mama ha™uri harda kukan ta mai nuni da tsantsar nadama a bayyane. Mama tayi farin ciki duk da bata tabbatar da shiryuwar ba amma taji daWi sosai. Manal ma haka ta dinga murmushi itama tana yi mata addu'a. Bayan tafiyar Bily a lokacin yamma tayi Mama ta kalli Manal tace, "ke ba kin ce yau Dr zai zo ba?."

Manal tace, "eh Mama."

"Amma ban ga kina Wan haWa masa wani abun ba? Ke kullum haka yake zuwa ya koma bakya bashi komai?. Ki duba har iphone 14 ya aiko miki da ita fa" Mubeena da ta faWa tana daga gefe a Warare kamar ba ´ar gidan ba. Mama ta kalle ta tayi murmushin jin daWi tace, "gaskiya ya kamata Manal ki yi wani abun." Jin haka sai Manal ta turo baki tace, "To ni Yaya me zan yi masa?."

Mubeena tace, "ke da ki ke hajiyar girki? Ki yi tunani." Tayi murmushi cikin jin daWin sakewar Mubeena Win tace, "ni ban san me zan yi ba." Mubeena tace, "to ki yi cake mana ko?, naga ana son sa sosai." Manal ta kalli Mubeena tace, "in nayi cake ni bazan ci ba Mama ma haka."  Mama tace, "dan tani kin san bai dame ni ba balle ga lalura, ki yi kawai zai ji daWi tunda yana kyautata miki. Wayar da ya baki fa Haron yace ta kusa miliyan. Kuma in yazo baya tafiya sai ya baki wani abun."

Manal tace, "To Mama zan yi." Mubeena tayi murmushi ji take ina ma itace Manal Win,zuciyar ta sam babu daWi in ta tuna abinda ya faru sai taji hawaye ya cika mata ido.

Tashi tayi ta shiga Waki Mama ta kalli Manal tace, "Me ya kawo wannan canjin na ta?." Manal tace, "Addu'ar ki Mama, don Allah kar ki zaton komai wallahi addu'ar ki Allah ya amsa. Shiyasa ake so iyaye su dimga yiwa yaran su addu'a ba aibata su ba, yanzu gashi da ki ke yi mata lokaci Waya canji yazo." Mama ta girgiza kai bata ce komai ba Manal ta tashi don ta fara abinda aka ce.

Nan da nan ta haWa cake mai yawa Allah ya taimake  ta aka kawo wuta ta shiga gidan su Surayya suna gasawa a oven suna hira. Bayan sallar magriba ta dawo gida tana numawa Mama duk da duhu yayi ganin Mama ya ragu amma khamshin cake Win ya burge ta. Bata Wauka ba ta hana ta ci saboda ciwon ta, Mubeena ce take ci ta bar mata a kusa da ita ta shiga wanka.

Bayan ta fito sai da tayi sallar i'sha ta kai cake Win falon baba ta dawo sannan ta shirya cikin doguwar riga ta atampa Winkin mai aljihu ta Waura Wankwali Mubeena ta kalle ta tace, "kin yi kyau. Kawai bakya ™hamshi sosai." Manal tace, "ai baya son turare, yanzu in naje ina khamshi sai ciwon kai." Mubeena bata ce komai ba ta girgiza kai kawai Manal tace, "Don Allah Yaya in ya shigo gaida Mama ki zo ku gaisa, bai taSa ganin ki ba yana tambaya ta ke."

Mubeena tayi murmushi tace, "Wannan ai dole ne. Amma ki zuba cake Win ya kaiwa Maman su hakan zai ™ara miki girma a idon sa." Manal tace, "haka Maman Surayya tace, har na zuba nata a foil paper ma zan bashi." Mubeena bata ce komai Manal ta yi murmushi a lokacin Baba ya shigo yana cewa, "Manal ke kullum sai anzo an faWa miki ana jiran ki?." Jin haka sai ta saka mayafi tayi kyau sosai duk da ko hoda bata saka ba amma tayi kyau, a haka ta fito zuwa falon.

Yana zaune kamar ko yaushe yana aikin danna wayar sa ta shiga da sallama ya amsa tare da Wagowa yana kallon ta. Sakin baki yayi yana sake ™are mata kallo domin bai taSa  ganin ta da atamfa ba sai hijjab da kuma abaya. Tayi masa kyau sosai don shi in kina so ki burge shi kawai ki yi kwalliyar atamfa hakan ya saka yake kallon ta har ta zauna suka haWa ido tace, "ka daina kallona." Janye idon sa yayi kamar ba shi ba tace, "ina wuni."

wani irin kallo yake mata na ™asan idanu mai ciki da ma'anoni kala kala kafin yace, "kin wuni lafiya?." Wani iri take ji in yana mata wannan kallon hakan ya saka ta nutsu sosai tace, "lafiya lau. Ya aiki?."

"Alhamdulillah." Juyawa bayan ta tayi ta Wauko castrool mai kyau wanda aka siyo a cikin kayan auren ta, Surayya  ce ta Soye a hijjabi aka zuba cake ko Maman su bata gani ba.

Ajjiyewa tayi da ruwa da lemo akan ™aramin tray tace, "Bismillah ga cake." Kallon cake Win yayi dan casrool Win transferring ne ana kallo abinda yake ciki, cake Win ya burge shi ya kalle ta yace, "da kan ki ki ka yi?." Ta Waga kai alamun eh yace, "Allah ya sa baki ci ba." Ta girgiza kai tace, "ban ci ba."

"Allah yasa hakan. Na gode."

Muryar Surayya taji tana kiran Milky tun  daga tsakar gida jin shiru bata amsa hakan ya bata tabbacin an faWa mata tana ina. Kallon ta yayi yace, "Meyasa ake ce miki milky?." Manal tayi farrr da ido tace, "cewa suke haskena ne kamar madara."

"A ina kika samo sunan?."

"Secondary school, duk wanda kaji yace milky beauty to tare muka yi makaranta.

Yayi ™asa da idanun sa yana kallon ta yace, "da gaske milky Win ce?." Sai ta kalle shi suka haWa ido tayi murmushi tace, "nima ban sani ha." Yayi dariya kaWan yace, "baki taSa bani labarin saurayin ki na farko ba."

"Kaima Baka bani labarin buduwar ka ta farko ba."

"Ai ni na fara tambaya."

"Sai ka ci girma ka fara faWa min."

Kawar da maganar yayi yace, "me kike shiryawa?." Manal tace, "akan me?."

"Auren ki." Kawar da kai tayi tana murmushi tace, "babu komai."

"Ki faWi gaskiya" ya faWa yana buWe kwanon ya Wauki paper cup cake Win guda Waya ya ciri kaWan ya saka a bakin sa  dan kar tace bai ci ba, ya kalle ta yace, "Allah yasa ba a wani  bakery Win kika siyo ba."

Bata ce komai ba sai yace, "Yayi daWi sosai ´an mata." Dariya ya bata tayi dariya amma shi bai yi ba yace, "Seriously ya kamata ki fara shirin abinda ki

Ke ganin zai yu." Manal tace, "to in sha Allah." Wayar ta ce take ™ara sai ta kashe ya kalle ta yace, "waye yake miki waya?." Ta girgiza kai tace, "ba waya ake ba, film ne."

"Kina kallon film?." Ta girgiza kai alamun eh yace, "Kdrama?" Ya tambaya dan a bakin ™anen sa yake ji. Ta girgiza kai tace, "ina ganin kdrama amma ba sosai ba, nafi ganin American series." Ya Wan wara ido yace, "Meyasa sai America? Naga mata kun fi son kdrama."

"Baya burge ni sosai."

"Meyasa America yake burge ki?."

"Saboda ina gyara pronouncing sosai, su English suke yi ina sanin yadda zan faWi kalma sosai."

Ya girgiza kai yace, "hakan yayi kyau. Wanne film ki ke gani yanzu?."

"The virgin and the billionaire." Bebi ya kalle ta jin sunan da ta faWa yace, "The Virgin and the billionaire" ya maimaita sunan yana kallon ta sannan yace, "waye virgin Win waye billionaire Win?."  Shiru tayi bata amsa ba sai a sannan fassarar sunan film Win yazo ranta sai tayi shiru yace, "ina jin ki."

Manal ta Wauko wani abun a baya ta tayi cikin foil paper tace, "Ga cake Win Mummy a kai mata."

Murmushi yayi yace, "Mummy ta gode, kamar kin san mummy na son cake especially wannan chocolate Win." Tayi murmushi bata ce komai ba ya lura ta kawar da maganar film Win sai bai sake dawo da maganar ba, zai yi magana aka kira wayar sa ya Wauka yana magana kafin ya kashe ta kalle shi tace, "Emergency ne ko?."

Kai ya Waga yace, "daga nan ma can zan yi." Ta taSe baki tace, "kuma sai yaushe zaka koma gida?." Ya kalli agogon hannun sa kafin yace, "maybe sai gobe."

"TabWijam! shiyasa bana son aikin asibiti tun farko."

Ya kalle ta ta cikin glasses Win sa yace, "sai Allah ya baki likita." Tayi murmushi aka sake masa waya ganin daga asibitin ne yayi tsaki kaWan ya kashe ™arar wayar tace, "wai kuma har da daddare kana zuwa? Ko da yake hakan ya faru akan Mamana."

Bai ce komai ba yace, "zan je na gaishe da Mama daga nan zan wuce. Amma nima wannan cake Win ki saka shi a foil paper nan kamar na Mummy zan tafi dashi, in naje aiki na huta."

Ta amsa da to ya kalle ta yace, "Manal!." Ta kalle shi suka haWa ido sai ya lumshe ido ya buWe a kan fuskar ta yace, "ina son ki, ina son ki son da ban son adadin shi ba. Ina kishin ki, bana so naga kowa a kusa dake. Pls Manal ala™ar ku da Huzaifa bana so, na faWa masa kema na faWa miki bana so, ki san irin zumuncin da zaku yi."

Manal jikin ta yayi sanyi saboda yadda yake furta kalmar yana son ta ya kashe mata jiki sosai. Ba kasafai yake faWar kalmar ba sai yaga dama, shiyasa ko a rubuce in ya tura mata tana matu™ar jin daWi. tace, "to ai ba......" katse ta yayi yace, "shiiii! Manal bana son musu, just say to."
Chapter 16 · 0% Book details