← Book details Baya Da Kura Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 50

Sashe 2

Baya Da Kura Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Na amince in ka aure ni ka auro wacce aka kaiwa kuWin auren ko da a ranar da na tare a gidan ka ne, Amma don Allah kar ka hukunta ni ta hanyar fara auren wata bani ba. Nasan zaka ce nima ai na auri wani kafin kai, ™addara ce Beb amma ina sonka Allah ma yasan da haka, rasa ka zuciyata zata iya bugawa a ko wanne lokaci, ka taimake ni kar na rasa hankalina akan soyayyar ka."

"In zuciyar ta buga ya shafe ni ne?, in kin rasa hankalin ki meye zai dame ni?. Ruman ki tashi ki bar min nan kafin nayi miki abinda yafi soyayyar da kike faWa tsayawa a zuciya, shi take zai tarwatsa zuciyar ki bazai jira wani abu ba, ki tashi ki bani waje bana son magana bana son ganin ki ko kaWan!" Ya faWa da ™arfi yana kallon ta itama shi take kallo ido cikin ido cikin tsoro. Duk da faWa yake mata amma kallon idanun sa nishaWi yake bata da tarin soyayyar sa da take huda ™irjin ta ta shiga cikin zuciyar ta a wannan lokaci.

"Ka taimaka min, na amshi laifina na baya, amma yanzu zan gyara komai, ka sake bani dama koda guda Waya ce."

"Oh my god! Meyasa kike insisting akan wannan abun ne? Na faWa miki bana sonki, bana son ki meyasa kike so ki takura min?. Ki tashi ki bani waje kafin ki ji saukar mari a kuncin ki."

"Asslamu alaikum, Yaya ga abinci." Jin muryar Kausar sai ya kalli wajan da take yace, "Koma da abincin bana ci" ya mi™e tsaya yace, "zo kija ta ku bar min falon nan kafin na fasa mata baki, bana son ganin ta, kuma kar wanda ya sake zuwa falon nan indai bani na k1ira shi ba" yana faWa ya shiga Waki ya bar su a wajan.

Rumana kuka take yi sosai sai ta bawa Kausar tausayi sosai, tunda ta guje shi da farko suke jin haushin ta amma yanzu tausayi ta bata ganin yadda yake mata tsawa ita kuma soyayya ta rufe mata ido tace, "ki daina kuka mu koma wajan Mama kar ya fito yace mun dame shi, yi ha™uri kizo muje." A haka suka fito zuwa wajan Mama suka same ta a zauna tana cin funkaso da miya ta bisu da kallo ba kamar Rumana da take kuka fuskar ta tayi ja sosai, kai tsaye inda Mama take ta nufa ta zauna a kasa tare da kwantar da kanta akan cinyar Maman tana sake fashewa da kuka.

"Ina son shi Mama, ban tabbatar da hakan ba sai yanzu da zan rasa shi, ji nake zuciyata zata iya bugawa na mutu in ban aure shi ba, Ina ji zan iya haukacewa a lokacin da wata ta shiga gidan sa a matsayin matar sa Mama. Mama ki taimake ni kar na rasa hankalina akan Bebi, Ina son sa amma shi baya sona" ta faWa cikin kuka sosai.

Jin abinda take faWa sai jikin Mama yayi sanyi sosai ta dafa kanta tace, "Haba Rumana! Sau nawa zan maimaita miki kalmar indai Ina da rai sai kin zama matar Adnan? Meyasa kike tantama Akan hakan?."

"Ba tantama nake ba Mama, Amma yanzu shi baya sona yace baya son ganina, ni kuma wallahi Mama ji nake kamar ana zuba min son sa a zuciyata, da gaske in na rasa shi ban san ya zanyi ba."

"Baza ki rasa shi ba in sha Allah, kar ki damu yana sonki kin san halin sa wata™ila yau ransa a Sace yake shiyasa, ki kwantar da hankalin ki ke matar Adnan ce, kar ki yi tunanin dan zai auri wata ba ke ba kamar baya son ki ne. Ramuwa yake akan abinda ya wuce na tabbatar Bebi yana sonki. Haba kar ki manta kece first love Win sa fa, kin san first love ba'a mantawa dasu saboda mahimmacin su, na tabbatar shima bai manta dake ba duk abinda kika ga yana yi yana sane, ki yi ha™uri lokaci ne."

Jin bata ce komai ba sai kuka Mama tace, "Tashi kije kiyi wanka ki kwanta wannan kukan ciwo zai saka miki." Da™yar ta iya tashi ta shiga Wakin da yake nata ko yaushe in tazo Mama ta bita da kallo. Kausar ta kalla tace, "me yayi mata haka?."

"Ban sani ba Mama, ni kaina bai tsaya ma yaji funkaso bane yace na dawo dashi a lokacin tana zauna tana kuka shi kuma yana tsaye. Amma kamar ransa a Sace yake sosai." Mama bata ce komai ba ta tashi ta shiga Waki itama Kausar Win haka.

Cikin dare Mimi ta fito shan ruwa falo taga Rumana a zaune sai rawar sanyi take yi alamun zazzaSi, da sauri tazo wajan taji jikin ta zafi sosai ta garzaya wajan Mama ta samu tana shirin kwanciya ta fito daga banWaki ta sanar da ita suka fito tare. A kusa da ita Mama ta zauna ta taSa jikin ta taji zafi sosai tace, "Mimi dau™o min waya ta na kira Bebi." Da sauri Mimi ta koma ta Wauko ta kira mata shi.

A lokacin yana zaune bai yi bacci ba yana sa™a da kwancewa akan abinda ya yiwa Manal yaga kiran Mama na zuwa, ai da hanzari ya Wauka yasan ba lafiya ba, Jin abinda tace sai ya tashi ya saka doguwar riga ya fito ya shiga falon da sallama suka amsa Mama tace, "zo ka duba ta da sauri, jikin ta yayi zafi sosai." ˜arasawa wajan yayi ya mi™a hannu ya taSa goshin ta da bayan hannu sa yaji zafi sosai ya kalli Mimi yace, "ki bata paracetamol ta sha zai sauka."

"Paracetamol kawai?" Mama ta faWa tana kallon sa cike da harara.

Ganin irin kallon da Mama take masa sai yace, "me yake damun ki bayan zazzaSin?." Rumana murya na rawa tace, "ciwon kai da ciwon ™irji." Yayi shiru na wani lokaci Mama tace, "ko asibiti zamu je?."

"A'a Mummy, akwai a Waki bara na kawo" ya faWa yana fita, ba jimawa ya dawo da magani ya bawa Mama yace, "ta sha yanzu zata dawo dai dai in sha Allah." Mama ta karSa aka bata tasha ya kalli Mama yace, "Allah ya ™ara lafiya. Sai da safe."

"Allah ya tashe mu lafiya" ta amsa a ciki ya fita dan shima magani zai sha kan sa ciwo yake.

Washe gari da ciwon kai da nauyin jiki ya tashi a haka yayi wanka ya fito ya shiga wajan Mamy suka gaisa ya tambayi Lubna tace taje makarnata daga nan ya wuce wajan Mama. Mama tana zaune ita kaWai ya shiga da sallama ta amsa ya zauna yace, "Barka da safiya, ban iya fita sallah ba yau saboda ciwon kai shiyasa ban shigo ba."

Mama tace, "Barka dai." Shiru yayi kafin ya kalli inda ake ajjiye abinci, yunwa yake ji sosai amma bazai iya cin komai ba gashi shi tea ba wani damun sa yayi ba balle yace zai yasha. Mama ta kalle shi tace, "in Rumana ta rasa ranta ta dalilin ka bazan yafe maka ba Bebi, ko wani ciwon ta samu ta silar ka bazan sassauta maka ba."

Da sauri ya kalle ta jin abinda yake cewa yace, "Mummy lafiya?."

"In da kana da mutunci kana zama a wajan nan ita zaka fara tambaya saboda a yadda ka barta jiya, ko baka Wauke ta matsayin wacce zaka aure ba ka Wauke ta matsayin ´a ta, kai ko bata kai wannan matsayin ba zaka iya mata kallon mara lafiya a matsayin ka na likita. Duk bata samu wannan darajar ba Bebi, wata bare a waje ta fita mahimmaci a wajan ka."

Bai iya magana ba yayi shiru dan bashi da abin cewa, koda akwai abin cewa Win ma Mama indai akan Rumana ne bata Waga masa ™afa ko kaWan.

Mama tace, "zuwa wajan ka da tayi jiya shine silar ciwon da ta kwana dashi ta kuma tashi dashi, Amma da ka shigo ko ka tambaye ta saboda bata da wnanan mahimnacin a wajan ka. Jiya kai ne ka faWa mata maganar da ta kai ta ga kwanciya zazzaSi" Mama ta girgiza kai ta kuma cewa, "komai in nace kana yi min a duk lokacin da nake so, amma akan Rumana ka gaza yi min abinda nake so saboda wani banzan tunanin ka da ya riga ya wuce, ka kiyaye ni wallahi, ka yi a sannu, yadda ka ke gasa mata aya a hannu akan soyayyar ka wallahi kaima zan gasa maka taka ayar tunda abin naka haka ne. Kuma wallahi ka sani ™iris nake jira na yanke ala™ar ka da wacce ka ke so Win, in na yanke sai naga na isa da kai ko ban isa ba."

Shi dai Bebi yayi shiru yana jin abinda take cewa yaji tace, "ka kiyaye ni wallahi, akan Rumana babu abinda bazan maka ba. Ka zaSi wata ta waje a kanta, duk tarin soyayyar da take mata ka rufe ido ka nuna kai baka santa ba, ka bani mamakk ban yi zaton hakan daga wajan ka ba."

Kansa yana ™asa bai ce komai ba ta harare shi tace, "Tashi ka bani waje." Jikin sa a sanyaye ya tashi yace, "ki yi ha™uri" yana faWa ya fita tayi tsaki tace, "ya zama dole ko ta wanne hali Bebi ya amince da auren Rumana kafin waccan da yake so ta shigo, hakan shine mafita. Ta bakin ita Rumana Win in ya auri waccan zai manta da ita ne, dole ya zaSa ko ya aure su Waya da Rumana ko kuma ya fara auren Rumana, in ba haka ba ya ha™ura da auren ita yarinyar, dan bazan zuba ido Rumana ta rasa ranta saboda shi ba."

BD˜B2P2

      Manal jikin ta babu ™wari ta farka dan bata yi baccin kirki ba ta fito tsakar gida inda take jiyo motsin Mama dan tasan ta tashi zuwa lokacin rana ta fito sosai. Ta ™arasa inda Mama take ta zauna tace, "Sannu Mama." Mama tace, "kin fito? Ya jikin naki?."

"Da sau™i."

"Tashi kije ki yi wanka zaki fi jin daWi." Da to ta amsa ta mi™e ta shiga banda™in ta fito ta Webo ruwa dan ita ruwan zafi ba wani damun ta yayi ba ta wuce da ruwan cikin falon su ta shiga Wakin Mama dake akwai banWaki tayi wankan.
Chapter 2 · 0% Book details