← Book details Baya Da Kura Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 50

Sashe 25

Baya Da Kura Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wannan ba damuwa bace mutuwa ce ai Adnan, in ka bar yarinyar nan tsaf zata iya rasa ranta a kan ka. Yanzu me ka yanke akan lamarin ta?." Yayi shiru bai ce komai ba Mama tace, "har yanzu baka karSi auren ta saboda kana so ba ko?, Shikenan ka aure ta saboda ni Win, ko da baza ka haWa Waki Waya da ita ba kamar yadda ta ro™e ka kayi mata."

Bebi maganar tayi masa nauyi sosai yace, "in sha Allah Mummy komai zai zo da sau™i."

"Hmmm! Ya batun lefen da nace ka dinga yin biyu?."

"Ai Mummy in lokacin yayi a rana Waya ma za'a haWawa in sha Allah."

"Gidan fa?."

"Shima sai a siya."

"Bana tunanin zan bari auren ku da ita ya kai shekara Waya bayan auren ka, zan je na samu Hajiya rana Waya nake so a Waura muku aure, in yaso sai ta tare daga baya."

Yayi shiru bai ce komai ba Mama tace, "ita Fatiman ta san da batun auren Rumana?." Ya girgiza kai alamun a'a tace, "Meyasa baka faWa mata ba? Saboda baka shirya auren ta ba ko?." Bebi yace, "wallahi ba haka bane ba, amma zan faWa mata in sha Allah." Mama ta girgiza kai tace, "ka kai musu keys Win gidan?."

"Eh na basu."

"Allah ya sa albarka."

"Amin Mummy."

"Kayi min al™awarin ko bani da rai ko yanzu na mutu ka tabbatar ka auri Rumana Adnan, shine zai saka ni farin ciki koda ina kwance a kabarina. Kaga ban ™yamaci auren ka ba, ban ™i wacce ka ke so ba, kaima kar ka ™yamaci abinda nake so, kayi min shi ko da baka so."

Bebi yace, "in sha Allah Mummy zan tabbatar da hakan." Tayi murmushi tace, "Allah ya yi maka albarka, naji daWin yadda ka rarrashi Rumana, Allah ya cigaba da kulawa da rayuwar ka." Yayi murmushin  farin ciki ya amsa sannan ya fita zuciyar sa cike da tunani kala-kala ya wuce asibiti.

Yana shiga asibiti kai tsaye wajan Hamza ya wuce ya samu Huzaifa ma yana ciki suna magana ya zauna suka kalle shi Hamza yace, "Ango ka sha ™hamshi, daga Ina haka?." Ya sauke numfashi yana kallon Hamza kafin yace, "Daga gida nake."

Huzaifa yace, "Ya batun dinner? Zaka yi ko ka fasa?." Bebi yace, "ba wannan ne a gabana ba yanzu, mafita nake nema." A tare suka kalle shi Hamza yace, "wacce mafita?." Ya zare glasses Win idon sa ya ajjiye akan table din gaban Hamza yace, "Ruman tana gab da da kamuwa da ciwon zuciya saboda dani, ko nace already ma ta kamu kawai abin bai yi zafi bane shiyasa ba'a fahimta ba." Hamza yace, "innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Abun har ya kai haka?."

Yace, "ni kaina nayi mamaki, ban Wauka haka take sona sosai ba, na Wauka duk kalaman ta na ™arya ne. Yanzu babu damar ayi maganar aurena a gaban ta, indai akayi koda da kuskure ne bata wuni lafiya. Abin ya zama yanzu dole rarrashin ta nake saboda lafiyar ta, a haka Mummy bata san da batun ciwon ba, amma ni na lura dashi tun ba yanzu ba." Huzaifa yace, "Tabbas ya kamata ka aure ta Bebi, ta cancanci soyayyar ka ko dan son da take maka."

Ya kalle shi yace, "taya zan iya auren ta bayan aurena saura kwanaki kaWan?. Ni ba wannan ne damuwa ta ba, Mama ta saka ni yi mata alqawarin ko babu ranta zan auri Rumana, ta kuma ce rana Waya take so a Waura aurena da mata biyu. Tsakani da Allah ta wacce hanya zan faWawa Manal cewa zan auri Rumana? Nayi mata adalci kenan?."

Hamza yace, "kaima tun farko da ka sani ka faWa mata batun tunda ka san da maganar auren."

"Haba Hamza, kawai sai na kalle ta nace mata in na aure ki da wasu kwananki zan sake yin aure?." Huzaifa ya girgiza kai yace, "to yanzu kai ya ka ke ganin zaka yi?." Yayi shiru na wani lokaci ya kulle fuskar sa da hannun sa yace, "ba auren nata nake ji ba yanzu, zan iya zama da ita saboda ciwon da yake barazana ga rayuwar ta, yadda nake ji a yanzu zan iya zama da ita koda babu Manal. In ba dan Allah ya kawo Manal ba da zan iya auren ta na zauna da ita kaWai saboda ina tausayin ta wallahi. amma ya zanyi da Manal! Me zance mata? Da wacce fuska zata Wauki abun?."

Huzaidq yace, "Gaskiya kamar akwai rashin kyautawa ita Manal Win." Ya kalli Huzaifa yace, "ka fahimci abinda nake nufi, Manal fa bata taSa aure ba sai a kaina, ta ya ya zan ce mata zan aure su rana Waya da wata wacce bata sani ba don Allah?. Ta amince dani, ta bani duk wata yardar ta, in na mata haka nayi adalci?."

Hamza yace, "to yanzu ya za a yi kenan?." Ya wara hananyen sa alamun bai sani ba shima. Hamza yace, "ni dai a ganina Manal ta san da labarin nan gaskiya, in ka bari sai ka aure ta ka faWa mata akwai tashin hankali, ka san mata akan kishiya balle ita da kishiyar zata zo mata wata™ila ko haihuwa bata yi ba."  Ya sauke numfashi ya mayar da glasses Win sa yace, "zan yi ™o™ari wajan ganin ba'a haWa bikin ba duk da ina tausayin Rumana. In yaso daga baya nayi mata bayani."

Hamza yace, "yanzu zata fi gane bayanin ka akan bayan auren ku, yanzu bata aure ka ba bata san meye asalin kishin ba, in ka faWa mata ta yarda kaga ko bayan auren wata fititar ta taso kana da hujjar da zaka ce ai kin sani tun kafin na aure ki. In ta aure ka ta san meye kishi, baza ta so wata mace ta raSe ka ba Adnan. FaWa mata yanzu shine mafita kaga tun farko ta sani."

Ya zubawa Hamza ido yana kallon sa cikin rashin sanin abinda zai yi a raunane yace, "Ina son Manal, bana son wannan maganar ya zama silar rabuwar mu, kar na sanar da ita wannan maganar tace  ta fasa."

Huzaifa yace, "baza ku rabu ba in sha Allah, zata fahimce ka kaje ka gwada." Ya sauke ajiyar zuciya yace, "in na bar nan zan wuce gidan su, Allah ya bani ikon iya faWa mata. Amma zuciyata bugawa take yi sosai, ni kaina hasaso kallon ta da zanyi nace mata zan auri wata nan gaba nake yi, yarinyar nan ™aramin abu ma babba take mayar dashi balle babba ne yazo da kansa, ya zanyi ni Adnan...?."

Hamza yayi murmushi yace, "zaka iya mana, kamar ba kai ba. Baka jin tsoron magana da kowa fa." Ya kalle shi yace, "kai ba wancan Adnan Win bane, duk zafin kan wancan, duk iya maganar wancan, duk dakiya da ™warin zuciyar wancan babu a wajan wannan. Soyayyar ta tsoron kallon ta nake na faWa mata wallahi." Huzaifa yayi dariya yace, "wanda zai auri mata biyu a rana Waya ai dole ya ajjiye zafin kai."

"Hmmm!" Shine abinda yace yana tashi tsaye kafin yace, "bara na bada magani a kaiwa Rumana na dawo." Huzaifa yace, "an gama angon uwar gida Manal, angon amarya Rumana, Sai ka dawo." Bai ce masa komai ba ya fita zuciyar sa babu daWi amma ya zai yi dole hakan zai aikata ko da baya so.

     Lokacin da ya bar asibitin gidan su Manal ya wuce yana zaune a mota yayi mata waya ta Wauka yace, "Partner zaki iya zuwa mota mu yi magana?." Manal tace, "baza ka shigo ba?."

"˜anunu kaya ne a jikina kin san ban iya shigowa dasu, gashi urgently ina son magana dake."

Manal tace, "to Ina zuwa bara na tambayo Mama." Ya amsa yana kashewa. Jim kaWan ya hango tahowar ta da abaya kamar ko yaushe, gaban sa ya tsananan ta faWuwa har ta ™araso wajan kallon ta yake yi zuciyar sa na hana shi yin abinda yazo dashi.

Kuna goyan bayan Bebi ya fadawa manal kuwa?>ØÝ

BD˜B2P15

Sallamar ta da kulle ™ofar motar ya saka shi jan dogon numfashi tare da lumshe ido, ™hamshin turaren gyara jiki da ake mata ne ya daki hancin sa, turaren babu ™arfi sosai yayi sanyi a hancin mai sha™ar sa hakan ya saka ya burge shi har ya lumshe idanun sa bai sani ba. A hankali ya buWe ido ya kalle ta sai yaga kamar an saka ta a machine an wanke ta hasken ta ya sake fitowa sosai kamar ´ar tsanar roba.

Waya ya kunna ya sake haska fuskar ta duk da hasken fitilar motar suka haWa ido ganin irin kallon da yake mata wanda bai saba yi mata irin sa ba sai tace, "Ina ta gaishe ka baka amsa ba." A sannan ya kashe wayar ya jinjina da kujera yace, "Ina zaki kai wannan kyaun?." Manal ta kalle shi tayi murmushi tace, "gidan ka." Šan wara ido yayi ya girgiza kai  yace, "Anya bai min yawa ba?."

"Zaka san yadda zaka yi dashi" ta faWa ba tare da ta kalle shi ba tana kallon hannun ta da ya fara komawa yellow saboda haske.

"Ba nace miki in aka miki wannan ™hamshin sai na saka ki a ruwa har sai ya fita ba?." Manal ta kalle shi kamar zatayi kuka tace, "to yanzu wannan yawa yayi? Saboda kai fa kaWan ma ake yi min" ta faWa tana turo masa small lips Win ta wanda suke jajaye tamkar na larabawa.

Saurin kawar da kai yayi, baya son bada kansa a wajan ta har sai ya aure ta shiyasa yake ™o™arin kiyaye duk abinda yazo ransa in suna tare,  kulle ido yayi ya buWe ya kalle ta yace, "yanzu haka kika wuce kowa yana jin wannan ™hamshin?."

"To ba kai kace nazo ba?." Ya zuba mata ido yana kallo itama haka sai ta janye nata idon tace, "ka daina kallona." Bai Wauke ido daga kanta ba kallon nata yake yi don in yace bai ji wani abu a kanta a wannan lokacin ba ™arya yake, ji yake kamar ya jawo ta jikin sa dan ta gama rikita masa lissafi.
Chapter 25 · 0% Book details