← Book details Baya Da Kura Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 50

Sashe 46

Baya Da Kura Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ranar talata da yamma bayan an tashi daga school Win ta dawo, a ranar bai je aiki sai da daddare zai fita, hakan ya saka ta same shi a falon farko a zaune yana kallon ball a tv da cup Win lemo a hannun sa yana sha. Kamar an cillo ta ta faWo falon ko sallama babu ta wuce shi a guje ta nufi sink Win da yake dining room tana amai.

Da sauri tashi ya bi bayan ta ya tsaya a bayan ta yana kallon ta yace, sannu" ya faWa lokacin da ta gama kuskure bakin ta da ruwa. Ya ri™o hannun ta zuwa falo ta zauna a kan kujera ya jawo ragowar ruwan da ya sha a roba ya bata ta sha yana zaune a kusa da ita yace, "Sannu, daman baki da lafiya yau ban sani ba?. Meyasa baki faWa min ba ki ka tafi school da ciwo?.

Ta girgiza kai tace, "lafiya ta lau, kawai makarantar ce yau ta saka ni amai, a can ma sai da nayi."

"Subahanallahi! Kuma bayan shi bakya jin komai?" Ya faWa yana dafa kanta kafin ya ce, "jikin ki da zafi kuma. Me yake damun ki bayan wannan? Babu abinda ki ke ji?.

Manal tace, "bana ji, kawai ina ji kamar na rufe kaina na duka, kaima ji nake yanzu kamar na zane ka wallahi, na rasa me yake min daWi komai haushin sa nake ji." Duk da dariya da ta zo masa sai bai yi ba ya danne yace, "Ayya sorry, kin san haka yanayin yake zuwa wani lokacin in zaka yi period." Manal ta kalle shi kamar zata yi kuka tace, "to ya™i zuwa sai wahalar dani yake, zuciyata har tafasa take dauriya kawai nake. Wallahi makaratar ma ta fita daga raina" ta faWa tana hawaye cikin rashin sanin abin yi.

Ya fakaici idon ta yayi murmushi kafin ya kalle ta yace, "ha™uri zaki daina ji, da zarar yazo zaki daina jin abinda kike ji daman rashin zuwan ne ya kawo haka." Manal tayi shiru bata ce komai ba sai kuma ta kalle shi tace, "kuma daman ana haka? Period ya™i zuwa gashi ina jin alamun ciwo mara?, hakan normal ne ko naje naga likita dai?."

"Ni ba likita bane?."

"Amma kai zuciya ka sani."

"Koma meye ai likita sunana. hakan kuma normal ne, in dai bai zo ba baza ki daina jin haka ba, kawai ki cigaba da daurewa da yazo shikenan fa."

Manal ta girgiza kai cikin ™in amincewa da maganar sa tace, "bai taSa yi min irin haka ba fa, ni dai tsoro nake ji kar naje wata cutar ce da ni." Ya girgiza mata kai yace, "kar ki damu babu wani ciwo."

Kallon ban yarda da kai ba take yi masa hakan ya saka shi kallon ta shima yace, "baki yarda ba?."

"Gaskiya ina kokwanto, bara na tambayi Mama naji me zata ce akan abinda nake ji" ta faWa tana Waukar wayar ta kafin ya gama mamaki har ta kira Mama.

Bai hana ta ba ya gyara zama dan yaji dramar ta da Mama dan yasan tunda tace zata kira sai ta kira ta. Mama ta Wauka da sallama Manal ta amsa suka gaisa kafin tace, "Mama daga makaranta nake ina ta amai."

Mama tace, "Ayya sannu, Daman baki da lafiya?."

"Lafiya ta lau, bana faWa miki ina jin ciwon mara ba?." Mama tace, "kin faWa min." Cikin shagwaSa tace, "Wallahi Mama ya™i zuwa har yanzu, gashi wahala nake sha ko yaushe a cikin ciwo nake, kamar ana ™ulle min mara haka nake ji, kuma kusan sati huWu fa ina jin ciwon amma har yanzu bai zo ba. Ni na gaji Mama haushin kowa nake ji wallahi, ji nake kamar na dinga marin kai na."

Mama tayi dariya tace, "ke da kike da likita a kusa dake Manal, shi zaki faWawa wannan damuwar taki bani ba."

Ta kalle shi shima kallon ta yake yi ta turo bakin ta gaba tace, "na faWa masa yace wai ai hakan ba abin damuwa bane, amma ni na damu gabaWaya wannan ciwon ya canja min yanayina, makarantar ma wallahi na tsane ta Mama. Kowa haushi yake bani, wani iri nake jina kamar ba ni ce Manal Win ki ba."

Mama tace, "gaskiya dai yana baki wahala, gashi kin ce min ke baki da ciki ko?." Manal tace, "eh mana."

"To ki cigaba da ha™uri zai zo."

"Ni na gaji da ha™urin, asibiti zan je." Mama tayi dariya tace, "sai kin dawo Manal, nayi ba™uwa sai anjima." Manal tace, "To Mama, a gaida Yaya Mubeena" ta faWa tana yanke wayar ta ajjiye a gefe gabaWaya ta rasa abinda yake mata daWi.

Shi dai kallon ta yake yi ganin tayi waya da Maman da alama bata samu mafita ba, tsabar taurin kai irin nata ga gaskiya amma ta™i yarda ita, ita a lallai bata da ciki gashi nan tun ba'a je ko ina ba ya fara nuna kan sa amma ta™i yarda har yanzu.

Ganin yayi shiru bai ce mata komai ba kallon tv yake yi sai ta kalle shi tace, "kai ko a jikin ka ko?, duk abinda yake damuna ni kaWai ya shafa, kallon ball Win ka ma ka ke yi wato na mutu kawai" ta faWa tana kallon sa a ™ufule. Ya rausayar da kai yace, "haba dai Partner, ni kuwa nake ji a jikina in baki da lafiya ai ni ne bani da lafiya."

"To kayi min abinda zan ji na daina jin komai don Allah, wallahi ni kaWai na san abinda nake ji" ta faWa a sanyaye tana kallon sa tana hawaye.

Kusa da ita ya dawo sosai ya ri™o ta ta kwanta a jikin sa ya goge mata idanun ta yace, "ki daina kuka, kar ki damu ki kwantar da hankalin ki zaki daina jin abinda kike ji sai a hankali."  Manal tana kwance a jikin sa tace, "amma ban taSa jin irin haka ba, sai dai nayi ciwon da yafi haka zafi amma bana jin wannan yanayin."

"Banbancin wancan lokacin baki da aure, yanzu kuma kina da aure shiyasa kike jin haka." Manal ta ri™e shi sosai tace, "amma nafi son wancan duk da nafi shan wahala bana jin irin haka, yanzu fa komai haushi yake bani ji nake kamar an canja ni." Bayan ta yake shafawa a hankali cikin shigar rarrashi yana murmushi cikin farin ciki yace, "Wannan Win ma zaki daina ji in sha Allah, ki yi ha™uri na Wan lokaci. Yanzu me kike so kici?."

Manal tace, "babu komai, kawai bana so naji kayi nisa dani, ka zauna a haka don Allah." Ya sake ri™e ta sosai a jikin sa yace, "ai gani a kusa dake, Amma ki faWa min abinda zaki ci."

"Tea nake so na sha, amma a saka min sugar don Allah."

"Kema kin san hakan bazai yu ba, Ta ya ya zaki sha sugar?."

"Shi nake so nasha, a saka madara da coffee a saka min sugar a ciki."

"Zaki sha madara dai amma banda sugar." Manal a sanyaye tace, "Shikenan na ha™ura." Numfashi ya sauke ya janye ta zai mi™e tsaye ta ri™e shi yace, "zan kawo miki tea Win ne, ga lokacin sallah ma yayi."

"Ka bar tea Win kawai, in ka dawo daga masallaci na sha."

"To sai na dawo" ya faWa yana kallon ta ta Waga masa kai yayi murmushi ya fita.

Yana fita ta tashi ta shiga kitchen da sauri ta haWa tea Win yadda take so, ta zuba sugar son ranta da madara ta bar shi ya wuce ta tayar da sallah. Tana idarwa jikin ta har rawa yake ta fara shan tea Win saboda yadda take ji in bata sha ba zata iya mutuwa, tashi tayi ta Wauko cake ta dawo tana sha da tea Win tana cin cale har lumshe ido take saboda daWi.

Kwace cake Win taji anyi an karSi cup Win hannun ta ta kalle shi a tsorace gaban ta yana faWuwa. Tea Win ya kai bakin sa ya haWWiye da™yar ya kalle ta cikin rashin fara'a yace, "haba Manal, meye haka? Wannan sugar ko mai lafiya ya sha ya za'a cika dashi balle ke? Meyasa kike wasa da lafiyar ki ne? Kina so ciwon nan yayi miki illa ne?."

A shagwaSe tace, "to shi nake so na sha ya zanyi?."

"Ba sai ki Wauki Waya ba ko tea Win ko cake? Sai ki haWa biyu ko wanne da sugar a ciki?." Manal ta Wauke kai gefe dan ita kam bata ga tayi laifi ba dan abinda take so ta aikata.

Tsaki yayi ganin abinda tayi ya wuce ta ya kai kitchen ya zubar da ragowar shayin da cake Win ya dawo inda take ya Wauko laptop ya zauna yana aiki tana gefe tana kallon sa.

Tana nan zaune shiru yana aikin sa tana gefe har akayi sallar i'sha bai ce mata kanzil ba ya tashi yaje  sallah ya dawo ya shiga Waki, tana zaune ya fito daga Wakin cikin ™ananun kaya yace, "zan tafi aiki, bazan dawo ba maybe sai cikin dare ko gobe, zan turo miki Ummi yanzu in akwai abinda kike so ki min waya."

Kallon sa tayi tace, "don Allah kar ka tafi ka barni." Ganin har ta fara hawaye sai yace, "aiki zanyi Manal dole naje." Ta taso ta dawo kusa dashi ta ri™e hannun sa tana narkewa tace, "nidai don Allah kaje dani bana so kayi nisa dani, ka tafi dani bazan iya zama baka nan ba."

Rungume shi tayi tana kuka a jikin sa dan da gaske bata so ya tafi ya barta. Yace, "Manal asibiti zan je fa ba wani resturant Win ba, Taya zan je dake ni da zan yi aiki?." Bata Wago ba sai kuka da take yi yace, "shikenan Wauko hijjabin ki mu je, amma kar kizo kina cemin na barki ke kaWai a office na je wani waje." Da sauri ta shiga ciki ta Wauko hijjabin ta Wauki wayar ta tabi bayan sa ya kashe hasken gidan suka hau mota suka tafi.

BDKB2P28
Chapter 46 · 0% Book details