← Book details Baya Da Kura Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 50

Sashe 47

Baya Da Kura Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kwanaki na ta tafita manal ciki na ta ™ara kwanaki a jikin ta har lokacin bata yarda ba shi kuma ya share ta yana bita a babu Win amma duk abinda take so babu abinda baya mata, cikin nata ma mayen sane duk inda yake bata son yin nisa dashi sai dole, makaranta kuwa ta daina zuwa sai online take lectures dan tace ta tsani school Win.

Shigowar sa gidan kenan ya tarar da Maryam a zaune a falo ita kaWai, ya shigo da sallama cikin falon yana bin ta da kallo ganin gabaWaya ta canja ta koma wani iri kamar ba ita ba. Sallamar ta amsa ya kalli falon yace, "ina matar gidan ta bar ki ke kaWai a zaune?." Ya faWa yana zama a kan kujera yana kallon ta. Maryam tace, "Yanzun nan ta shiga ciki."

Manal ce ta fito a lokacin ya kalle ta sai tace, "sannu da zuwa" ya amsa kafin ta juya ta koma ciki.

Ya kalli Maryam a nutse yace, "hankalina ya tashi tunda kika ce kina gida kina jirana, me yake faruwa haka? Me ya same ki kika canja kamar wacce tayi rashin lafiya?."

Maryam ta sauke numfashi ta kalle shi tayi shiru na wani lokaci tace, "Bebi Kamal ne." Gaban sa ya faWi mutu™a ya kalle ta yace, "wani abun ne ya faru?." Ajiyar zuciya tayi ta goge idanun ta da suke zubar da hawaye bata ce komai ba ta sunkuyar da kai.

"Kin yi shiru, hankalina a tashe yake ki sanar dani me yake faruwa ma."

Maryam ta kalle shi tace, "Ban san ta ina zan fara sanar da kai abinda ya faru bane, nauyi nake ji a zuciyata ban san da wacce fuska zaka kalli abinda zance maka ba shiyasa nayi shiru. Amma bani da wanda zan sanarwa sai kai na gaji da abinda yake faruwa gwara ka sani ko zaka yiwa tufkar hanci."

Girgiza kai yake yi yace, "ina jin ki." Maryam ta kulle ido ta buWe ta kalle shi tace, "Kamal ne yake amfani da...." Sai tayi shiru bata ™arasa ba yace, "ki sanar dani mana, me Kamal Win yake amfani dashi?."

"Kamal ne yake blackmailing Wina da wasu hotuna na wajan sa."

"Blackmailing! Kamar ya blackmailing Win ki ban fahimta ba, wanne irin hotuna ne wannan da yake amfani dasu?." Maryam ta kulle ido ta buWe nauyin sa take ji har cikin zuciyar ta hakan ya saka ta kasa magana, sai da ta daure ta haWWiye yawu ta kalle shi tace, "hotunan tsaraicina ne!."

"Hasbunallahu wani'imal wakil! A ina ya same su? Kar kice min ke kika tura masa?."

"Ni na tura masa." Da sauri ya kalle ta kafin yayi magana tace, "Bebi wallahi ba hotunan yanzu bane, tun ina gidan sa hotunan suke wajan sa, na Wauka da muka rabu ya goge ashe bai goge ba, yanzu dasu yake amfani wajan tilasta min nayi zina dashi!."

A firgice ya kalle ta idanun sa a waje saboda firgicin abinda yace, "kar ki ce min kin aikata Yaya Maryam, kar kice min kin biye masa kin aikata zina." Shiru tayi ta share hawaye tace, "ban aikata ba Bebi, so nake yanzu a san ya za'a yi a goge hotunan daga wajan sa."

Kallon ta yake yi haka nan zuciyar sa bata amince da abinda tace ba yana kallon ta yace, "kin tabbatar da abinda kika ce?." Kallon da yake mata ne ya saka ta kasa magana yace, "tun farkon rabuwar ku yake yi miki barazana da hotunan kuma har aka zo yanzu babu abinda ya faru?, kina so kice barazana yake miki daga lokacin har yanzu bai miki komai ba?. Yaya Maryam ko aurena an Wauki lokaci a yanzu balle rabuwar auren ku."

Kulle ido tayi ta buWe ta dafe kanta tana kuka tace, "yace in ban amince ba sai yaWa hotunan a duniya, tsoron kar hotunan su fita waje ya saka na....!"

"Ya saka kika aikata zina Yaya! Ya saka kika biye masa kika aikata zina saboda tsoron abinda zata ce duniya a kan ki kika saSawa Allah?."

Sai da ta tsorata saboda yadda yayi maganar cikin tsawa zallar Sacin rai kamar ba Yayar sa ba tace, "Saboda Nabila da Nabil Bebi, posting yace zai yi a social media in hotuna suka shiga duniya da wanne ido zan kalle su?."

Kamar zai dake ta yace, "saboda gudun maganar mutane sai kika saSawa Allah?, Allah da ya halicce ki bakya jin kunyar sa sai kunyar ´a´an ki?."

"Saboda hotunan ne wallahi ba da son raina ba, ka fahimci ni!."

"Bazan taSa fahimtar ki ba, har abada bazan taSa fahimtar abinda zaki ce min ba yanzu ko nan gaba. Meye amfanin tura hotunan?." Ta kalle shi tana kuka tace,"lokacin ina auren sa."

"Ko lokacin da kike matar tasa ne meye amfanin tura masa hotunan tsaraicin ki? A ganin ki soyayya ce ko?, a ganin ki ™auna ce ta kawo hakan ko?. Kin Wauki hotunan tsaraicin ki kin tura masa saboda ta™amar ki mijin ki ne, kin manta da zai iya ajjiye wayar a wani wajan wani ya Wauke ko iya shi kaWai yaga hoton a wayar ya cuce ki. Wannan lokacin da muke ciki na ™wacen waya in aka ™wace wayar tashi fa? Mahaifin ki dan siyasa ne da wannan kawai za'a yi amfani wajan lalata masa siyasar sa, ke duk baki tunanin wannan ba a lokacin ba?, soyayya ta rufe miki ido, shi kuma da yake yana da wayo baya tura miki nasa sake uwar soyayya! Yanzu gashi dasu yake amfani yake ruguza miki rayuwa!."

Kai yake girgizawa yana magana cikin murya mai amo yana nuna ta da tsaya kamar ba Yayar sa ba yace, "ba ko wanne miji ne in ya rabu dake yake kare mutuncin ki ba, ba ko wanne namiji ne in ya rabu dake yake so yaga kin samu nutsuwa ba, ba ko wanne namiji bane in ya rabu dake yake so ki yi walwala a duniya ba. Wani burin sa yaga kin wula™anta, burin sa yaga kin tozarta, wani burin sa so yake yaga kin dawo bara a kan titi, wani so yake yaga ya kulle miki hanyar da wani zai aure ki. Ba ko wanne masoyi ne yake zama masoyi ba, Annabi Muhammad S.A.W da kan sa yace ka so masoyin ka sama-sama saboda wata rana zai iya zama ma™iyin ka, sannan ka ™i ma™iyin ka sama-sama wata rana zai iya zama masoyin ka. Har gwara ace ma™iyin ka ne ya dawo masoyin ka akan ace masoyi ya koma ma™iyi, saboda ma™iyin ka bai san komai naka ba, masoyin ka da ya koma ma™iyi babu abinda bai sani naka ba, da zarar ya koma ma™iyin ka ya san hanyar da zai bi ya cuce ka saboda duk wani lagon ka ya sani. Meyasa baki yi tunanin hakan ba? Ke a ganin ki tura masa hotunan tsaraicin ki da kike yi ™auna ce ko? Yanzu wa gari ya waya? Gashi yana amfani da hotunan yana saka ki aikata zina dashi bayan yayi miki saki uku!, kin cutar da kan ki da hannun ki."

Kuka take sosai mai nuni da nadama mara amfani, yanzu ta gano kuskuren ta da ta tafka a rayuwar ta, yanzu ta gane gangancin da ta yi da rayuwar ta, yanzu ta gane tura hotunan tsaraici ga wani mijin ba soyayya bace. Cikin shashshe™a tace, "nayi nadama Bebi, nayi nadama bazan sake aikatawa ba, na jima ina so na sanar da kai sai na kasa faWa maka, amma yanzu ka taimaka min kar hotunan su shiga duniya. Yace in ban je na same shi gobe ba zai watsa su a duniya, ni kuma na gaji da aikata saSon Allah." Kuka take yi sosai zuciyar ta bugawa take yi sosai hankalin ta ya tashi matu™a, nada sani ta gama mamaye zuciyar ta. Ya kalle ta idanun sa sun koma jajajur saboda Sacin rai da takaici da ™unar zuci yace, "har sau nawa hakan ya faru?." Ta sunkuyar da kai bata kalle shi ba kuma bata yi magana ba. yayi ™aramin tsaki tare da murmushin takaici yace, "sai da komai ya lalace zaki neme ni?."

Maryam tace, "ka gyara komai Bebi, ka gyara ka ceto mutuncin Yayar ka, ka taimake ni bana so Mamy ta san maganar nan don Allah. Baza ta iya jura ba, kwanaki Lubna yanzu kuma ni." Ya yi shiru yana sauke ajiyar zuciya, zuciyar sa nayi masa zafi sosai ya kalle ta cikin ba™in ciki da yaje kina zuciyar sa yace, "ki amsa min tambayata, sau nawa kika je wajan sa?."

Kasa magana tayi ta kulle ido ta buWe yace, "ke kan ki baki sani ba ko? A haka kike so na taimaka ki?."

"Ka manta da wannan ka taimake ni."

"Ke kika kai kan ki Maryam!."

"Ka dawo dani Bebi!" Ta faWa tana tasowa tazo inda yake tsaye ya juyar da fuska gefe Waya. Numfashi ya sauke ya kalle ta yace, "baki da bu™atar taimako na." A ™asa ta zube guiwowin ta ta haWe hannayen ta waje Waya tace, "ina ro™an ka Adnan, ba don ni ba dan zumuncin da yake tsakanina da kai ka ceto rayuwata. Naci alfarmar ´a´an ka Nabil da Nabila ka ceto ni daga hannun Kamal."

Yawu ya haWWiye da™yar ya sunkuya ya Wago ta daga ™asa ya ri™e kafaWar ta ganin tana kuka sosai yace, "zan san abinda zan yi a kai."

Maryam tace, "yau kawai nake da ita, in ba yau ba gobe zai iya aikata abinda yace." Ya kalle ta ya cire glasses Win sa yace, "bakya jin kunyar wanda ya halicce ki sai kunyar yaran ki?." Tayi shiru ta sunkuyar da kai yayi tsaki yace, "i'm highly disappointed." Kuka take yi sosai tace, "ban san ya zanyi bane ba Bebi, ban sani ba."

Lumshe ido yayi ya kalle ta yace, "kin Sata komai Maryam, gyara shi yanzu bashi da amfani tunda kin aikata ba sau Waya ba, ba sau biyu ba. Sau nawa ina ja miki kunne akan Kamal kike ganin kamar takura miki ki nake yi? Sau nawa ina miki iyaka dashi kin ji?."

"Naji Bebi wallahi, na fara ja baya da zuwa inda yake daga baya ya fara amfani da hotunan."
Chapter 47 · 0% Book details