← Book details Baya Da Kura Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 50

Sashe 3

Baya Da Kura Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba jimawa ta fito tsakar gidan ta saka riga da siket na kanti rigar mai ™aramin hannu ta shan iska ta dawo inda Mama take ta zauna tace, "Mama ina Yaya?." Mama tace, "bata ciki?."

"Ban ganta ba gaskiya."

"To ta fice, Daman hanya take nema da yake taga Baban na ku ya fita tun safe shiyasa ta gudu. Taje tayi ai duniya ce."

Manal tace, "Mama kin sha maganin ki? Ina glasses Win na ki?."

"Ban sha ba, shi kuma ban san inda na ajjiye shi ba sai dai ki duba." Tashi tayi ta koma ba jimawa ta dawo dashi da maganin tace, "gashi na Wauko." Ta bata ta saka, Maman ta kalle ta cikin ganin da ba bashi da auki sosai tace, "kin rame sosai, wannan ciwon mara yana wahalar dake, Allah yasa in kin yi aure ki daina." Manal ta amsa da amin zuciyar ta na tuno mata abinda ya faru jiya ta bawa Mama maganin ta sha Mama tace, "kije ki karya, na bayar an siyo kunu tun safe nasan yanzu ma yayi sanyi. Rashin glasses Win nan ne da da kaina zan dama."

Manal ta tashi ta shiga kitchen ta Wauko kunun tana sha Mama tace, "jikin ki babu ™arfi, baza ki samu damar zuwa kasuwar bama yau. Sai ku je gobe in Allah ya nuna mana." Manal ta sauke numfashi tambayoyi ne sosai a zuciyar ta wanda take son yiwa Mama amma ta rasa ta wacce hanya zata fara, bata so silar tambayar Mama ta shiga damuwa amma tana so ta san waye mahaifin su? A Ina yake? Sannan da gaske Baba ba Wan uwan sane bane kamar yadda take faWa musu?.

Ganin tayi shiru sai Mama tace, "tunanin me ki ke yi?. Jiya kince min zaki je wajan Adnan karSo sa™o daga nan kika dawo babu lafiya, wanne sa™o ya baki?."

Manal ta sauke ajiyar zuciya ta kalli Mam tace, "tambayata yayi daman wai mahaifin mu ba rasuwa yayi ba, sannan yace daman Baba ba ™anin mahaifin mu bane nayi masa ™arya." Kallon ta Maman take yi sai ta kawar da kai gefe tayi shiru bata ce komai ba.

"Mama da gaske ne abinda ya faWa? Da gaske Baba bashi da wata ala™a damu ta jini?. Mama na shiga confusing don Allah ki sanar dani ko hankalina zai kwanta. Ina mahaifin mu? Meyasa kika ce mana ya rasu?." Mama ta kalle ta cikin rashin ganin ta sosai tace, "shi Adnan Win ne ya tsare ki da wannan tambayoyin?."

"Mama ya samu labari ne saboda an sanar dashi komai game dani, kinga dai a Sangaren neman aure ba'a ™arya shiyasa Baba ya faWa masa komai."

"Cewa yayi ya fasa auren ki in baki faWa  masa ba kenan ko me?." Jin abinda Maman tace sai ta kalle ta zata yi magana Mama tace, "in ma cewa yayi ya fasa auren ki har sai yaji labari akan mahaifin ki ya fasa ai baza ki rasa wanda zai aure ki ba, ba dole a maganar aure, in yaga ya fasa in Baban ku ya dawo sai aje a mayar musu da kuWin da suka kawo wannan ba komai bane ba."

Manal da mamaki take kallon Mama jin abinda take cewa tace, "Kenan Mama baza mu san asalin mahaifin mu ba...." Mama ta dakatar da ita cikin tsawa tace, "Kinga Manal ya ishe ni!, ke dai kin san ba cikin shege nayi na haife ku ba ko? To ki dakata min da wannan maganar bana son ji, in akan auren Adnan ne kike wannan maganar ai ba shine kawai namiji a duniya ba, na tabbata zaki samu wani wanda ya fishi wanda bai damu da yasan wannan maganar ba" ta nuna ta da yatsa tace, "Manal a bar maganar nan haka, bana so kar a sake yi min ita in dai kina son kwanciyar hankalina" ta faWa tana tashi tsaye. Manal tace, "ki yi ha™uri" Mama bata tanka mata ba ta wuce ta Manal ta bita da kallo zuciyar ta na so ta hasaso mata dalilin Mama na wannan maganar.

         Mubeena a lokacin da ta faki ido ta bar gidan kai tsaye gidan su Bily ta wuce, tana shiga Mummyn su ke tambayar ta kwana Biyu bata shigowa tace bata jin daWi ta wuce zuwa wajan Bily. Tana shiga Waki ta same ta tana shan tea tan danna waya tace, "Bily meyasa zaki je gidan mu kice wai an kore ni daga makaranta?."

Bily ta kalli Mubrena tace, "haba Mubeena, wannan wanne irin abu ne babu sallama babu komai sai dai naji maganar ki a kaina?." Mubeena ta zauna tana kallon ta tace, "abinda kika yi min ne sam ban ji daWin sa ba, gashi nan dalilin hakan an kafa min tarko an hana ni zuwa ko Ina kamar wata yarinya ™arama, komai nayi a kan idon mutanen gidan. Kin san ya akayi na fito yanzu kuwa?."

"Eh, ai ni naje gidan na faWa musu saka ido a kan ki domin lamarin naki yana neman wuce gona da iri, yanzu gashi da aka killace ki har kyau kin ™ara yi."

"Kin san abinda hakan ya jawo min? An ™wace min waya, an hana ni fita, na zama kamar wata marainiya saboda kaWaici, Meyasa zaki aikata min hakan?. Ke kin san bana iya zaman awa guda babu waya amma kika zama silar da aka karSi ta hanuna, gaskiya ban ji daWi ba." Bily tace, "daidai kenan, indai kina tare da wannan Alhajin abinda zaki aikata ke kan ki baki sani ba, shiyasa na yiwa tufkar hanci."

Mubeena tace, "auren Manal fa za'a yi har an saka rana amma ni babu kowa ta dalilin ki an raba ni da wanda zai aure ni, Meyasa zaki min haka?,  wallahi ban ji daWi ba.."

"Inda ace auren ki zai yi da kaina zan raka shi gidan ku lokacin da yazo gidan nan." Mubeena da sauri tace, "yazo kike so ki ce?." Bily tace, "yazo, na kuma faWa masa aure za'a yi miki kuma kun koma garin ku kin bar kano."

Mubeena da sauri ta kalle ta sai ta zabura ta koma kusa da ita tace, "Kina nufin yazo nan? Meyasa kika ce masa haka Bilkisu?." Bily tace, "saboda so nake ya rabu da ke, saboda tarayyar ku lalata ki zata yi  ni kuma matsayina na ™awar ki dole na faWa miki gaskiya na kuma yi abinda nake ganin shine daidai."

Girgiza kai take yi tace, "wannan ba daidai kika yi ba Bily, meyasa zaki masa ™arya bayan kin san Ina son sa shima yana sona? Waye yace miki da wani abun yake nema dani ba aure ba?."

Bily tace, "ya taSa miki maganar aure tunda ku ke?." Mubeena tace, "sai na faWa miki?."

"Surutun ki bazai saka ki yi shiru ba, bai taSa yi miki maganar aure ba ko yaushe son taSa jikin ki yake yi. 0n sha Allah baza ki sake samun sa ba ya tafi kenan."

Mubeena tace, "baki kyauta min ba wallahi, kin san halin da na shiga kwana biyu da bana ganin sa? Shi yanzu kin san halin da yake ciki?." Bily tace, "yana can tare da wata wanne hali zai shiga Mubeena? Ke kike haukan banza kina ganin yana tunanin ki baki san yana can tare da wata ya manta ma dake. Inda alaqar Allah da annabi ce da yanzu ya dawo ya sake neman ki amma bai sake zuwa ba saboda daman shi ba auren ki zai yi ba."

Mubeena ranta ya Saci sosai tace, "ki ™yale ni kawai bana son wannan maganar taki, ni zanje na nemo shi da kaina kuma sai na same shi" Tana faWa ta fita Bily tana cewa, "kije ki tayi babu ruwana ko me zaki yi nan gaba wallahi, kin san daidai kin san ba daidai ba. ˜ar™ari na yanke ala™a ta dake kowa ya kama gaban sa.

Mubeena bata ma ji ba tuni ta fita da yakr bata ga Mummy a falo ba da sauri ta fice. Tafiya take yi a ™asa ranta a Sace akan abinda Billy tayi mata, kamar a mafarki kawai taga motar sa ta faka a nesa da ita.

Cak ta tsaya sai kuma ta cigaba da tafiya tunawa da tayi wata™ila bashi bane tazo zata wuce ya sauke glass yace, "kin san mutane bana so su gane ni, ki shigo kawai." Jin muryar wanda yayi magana sai ta kalle shi ta gefen baya yaga an Waga glass Win ta tabbatar shine dan ga muryar sa nan ta buWe motar ta shiga driver yaja suka tafi.

Shiru babu wanda yayi magana tafiya kawai suke har suka je gidan sa aka buWe gidan aka shiga driver sai ya fita daga motar. sai a sannan ya kalli Mubeena ido cikin ido yace, "Kenan kin kyauta?." Zata yo magana ya dakatar da ita yace, "mu je ciki bana son magana a nan" ya faWa yana fita daga morar ya shiga ciki dole Itama tabi bayan sa.

Tana shiga ya bita da kallo from head to toes kamar zai mata kuka yana kallon cikin idon ta yace, "yanzu kin kyauta kenan Baby? Me nayi miki da kika zaSi ki Soyewa ganina? Wanne laifi na aikata miki da kike yi min wannan hukuncin mai tsauri da na kasa jure masa?."

Mubeena tace, "Ba laifina bane ba, kana raina wallahi Baby, bani da waya kuma bana fitowa shiyasa."

"Har gida na aika a kai miki waya akace bakya nan, naje da kaina sai akace min wai kin bar garin nan kin koma Adamawa kuma aure za'a yi miki" ya tako ya ™araso inda take ya ri™r hannayen ta duka buyun yace, "Ina kika shiga? Me nayi miki?."

"Ba Suya nayi bafa, kana raina burina na samu dama na neme ka, tun daga lokacin bana fitowa sai yanzu na samu dama na fito." Bakin ta yake kallo yadda take magana tana turo shi gaba ya lumshe ido yace, "me ya faru haka?."

"˜wace min waya ta akayi a gida, sannan aka hana ni fitowa." Murmushi yayi ya ja kumatun ta yace, "da girman ki a ™wace wayar ki kuma a hana ki fitowa?."
Chapter 3 · 0% Book details