← Book details Baya Da Kura Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 50

Sashe 41

Baya Da Kura Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tafiya suke tana share hawaye ya juyo ya kalle ta kamar zai mata magana sai ya fasa ya cigaba da tafiya, sai yaga ta goge idon tayi shiru tana kallon titi ta naWe hannun ta a ™irji. Hannun sa guda Waya ya mi™a ya ciro hannun ta daga ™irjin ta yana murzawa a hankali yana cigaba da tu™in sa bai ce komai ba. Sake kallon ta yayi yaga duk ta canja yace, "da na san kuka zaki yi da ban kawo ki ba."

Manal ta kalle shi da shagwaSa tace, "to ai na daina."

Yayi murmushi yace, "Zamu je wajan Mummy yanzu." Manal ta kalle shi da sauri tace, "Wajan Mummy kuma? Amma baka faWa min ba?."

"Yanzu na faWa miki."

"Haka zan je ban kai mata komai ba? Ni gaskiya a fasa sai na shirya."

Juyowa yayi ya kalle ta yace, "sai kin kai wani abun? Gaishe ta kawai zamu yi ai." Manal tayi shiru haka kawai taji gaban ta yana faWuwa ta sake kallon sa tace, "wallahi kunyar zuwa haka nake, kuma kunyar Mummyn ma nake ji sosai." Ya Wan kalle ta ya Wauke kai ya cigaba da tu™in sa yace, "Zaki daina."

Shiru tayi har suka je ™ofar gidan yayi horn aka buWe masa ya shiga cikin gidan ya ajjiye motar ya kalle ta yace, "muje" ya faWa yana buWe ™ofar Sangaren sa ta ri™o hannun sa hakan ya saka ya dakata yana kallon ta tace, "kana ganin ya dace naje wajan ta da Abaya? Baka ganin kamata yayi na saka atamfa?." Shi mamaki ma take bashi, gabaWaya ta ruWe hakan ya saka yace, "ko ki Winka bargo ki zo dashi ba, ki fito mu shiga dare yana yi inda abin yi."

Dole ta fito suka shiga cikin gidan su kai tsaye wajan Mummy suka nufa. Da sallama ya shiga suna zaune dukkan su suna cin shawarma suka amsa sallamar Kausar ta taso a guje tana cewa, "ga Anty Manal oyoyo." Manal ta ri™e ta tana murmushi tace, "Sis ya gida?."

Mummy da take zaune tana kallon tace, "Manal ce da kanta yau kenan? Shigo mana kamar ba™uwa." Manal ta ™arasa ciki ta zauna a kan carpet ta gaishe da Mama da girmamawa Mama ta amsa tana murmushi tace, "kema ya koya miki cewa Mummy Win kenan?, shikenan ku biyu ne masu cewa Mummy, kin zama kishiyar sa." Manal tayi murmushi kawai bata ce komai ba Mummy tace, "ina fatan kuna zaune lafiya?."

"Lafiya lau Mummy."

"Haka ake so, Allah ya bada zaman lafiya ya baki ha™urin zama dashi. Don zama da Bebi sai an shirya, zaki sha tsirfa kala-kala, baya cin wannan baya son ™hamshin wannan. Saka aiki kuwa sai kin gaji" ta faWa tana kallon sa yana gefe yana murmushi. Kausar da take gefe tace, "Wallahi kuwa." Banzan kallon da ya mata ya saka ta yin shiru tana dariya.

Mama ta kalle shi tace, "yaushe zaka kai ta gidan Hajiya ne? Wai Hajiya guda ace har yanzu baka kai mata Manal ba?, ko da yake auren naku ma kwana nawa? In badan zamani ba ai bakwa fito ko kwana bakwai baku yi ba."

Bebi yace, "maganar Hajiyar nake gudu amma da yanzu zamu je, to Hajiya ta dinga cemin har an fito, har anyi kaza da kaza shiyasa nace naje daga baya. Amma zamu je gidan Umma da Ammi a satin nan in sha Allah."

Mama tayi dariya ta kalli Manal da kanta yake a ™asa tayi shiru alamun ba™unta Mama tace, "ki Wago mana kamar wata ba™uwa Manal?, nan ai gidan ku ne kema. Kamar Kausar kike a wajena kar ki ji komai ko kallon banza ya miki kizo ki faWa min."

Maanal tayi murmushi kawai bata ce komai ba. Kausar tace, "Sis kin yi shiru da yake a gaban Mama ne kamar bakya magana." Mama tace, "raka ta wajan Mamy su gaisa sai tazo ku ci abinci." Tare suka da Kausar Mama ta bita da kallo ta kalle shi tace, "Ma sha Allah, akwai nutsuwa da kunya. Ga kyau, ashe tafi kyau a hakan ta babu makeup, da bikin ku sai ta koma kamar wata yar tsana saboda haske."

Mmurmushi kawai yayi baice komai ba, kar ya tanka Mama tace wani abu shiyasa yayi shiru.

Ba jimawa suka dawo Mama ta saka ta koma kan kujera kusa da Kausar da Lubna da ta biyo su, Rumana ce ta fito daga Waki tana cewa, "kai amarya ce guda a gidan nan ko a min magana?." ˜arasowa tayi ta zauna kusa da Kausar dake kusa da Manal ta kalli Manal tace, "Amarya nice Rumana" ta faWa tana bata hannu alamun su gaisa.

Šago ido tayi ta kalle ta sai gaban ta ya faWi haka kawai bata san dalilin haka ba, ta bata hannu suka gaisa tana murmushi Rumana ta kalli Bebi tace, "Beb ya kamata ace an sanar dani zuwan nan na tarbi amarya." Kafin yayi magana Manal tace, "ya jikin ki?." Rumana ta kalle ta tace, "Alhamdulillah da sau™i, ashe ya sanar dake bani da lafiya."

Manal tace, "Uhum na sani, Allah ya ™ara lafiya."

"Amin na gode amaryar mu."

Sai a sannan Bebi ya kalli Rumana yace, "naga kin samu lafiya." Rumana ta murmusa tace, "Alhamdulillah zamu ce, naji sau™i sosai."

"To haka ake so" ya faWa yana cigaba da danna wayar sa. Mama tace, "Kausar kawo mata abinci taci." Bebi yace, "a bar shi kawai Mummy, in mun koma zamu tarar matar Yaya ta kai abinci."

Mama tace, "koma meye sai taci abincin gidan nan, sarkin tsari." Baice komai ba aka kawowa Manal wainar shinkafa da miya. Manal ta kalle shi suka haWa ido kafin ya janye nasa ya kalli wayar sa, ita kuma ta fara ci dan tayi daWi amma da sugar a ciki.

Fara ci tayi da niyar taci kaWan sai gashi taci guda biyu ta bar biyu a plate Win. Ta ajjiye plate Win a lokacin Mummy ta fito daga Waki tace, "ba dai kin ™oshi ba." Tace, "Eh Mummy na ™oshi." Mummy ta zauna Rumana ta kalle shi tace, "Beb baka ce min yaushe zan tafi Abuja ba?." Ya kalle ta yace, "na san baki shirya ba." Tayi murmushi tace, "in zan tafi ma zan zo har gida na yiwa amarya sallama" ta faWa tana kallon Manal da itama ita take kallo, suka haWa ido Manal tayi murmushi kawai.

Kausar tace, "Sis muje ki wanke hannun ki." Bin bayan ta tayi ta wanke hannu ta dawo ta zauna Bebi yace, "to Mummy zamu wuce dare yayi har tara ta wuce

Mummy ta mi™awa Manal leda mai Wan girma tace, "Humra ce aka kawo min jiya da turaren wuta, har na haWo da turaren wutar na tuna mijin ki aljanun ™in turare ne dashi sai na kawo miki humrar kya yi amfani da ita."

Manal ta sauka har ™asa ta karSa tace, "an gode Mummy, Allah ya saka da alkhairi." Mama ta amsa da amin tana murmushi. Mamy ce ta shigo tana cewa, "ina sauri kar nazo kun tafi, Manal ga spices ayi girki. Kin san angon naki baya wasa da abinci" ta faWa tana bawa Manal ledar. Manal tayi murmushi ta karSa tana godiya Mamy ta amsa tana fita.

Har waje Kausar da Lubna suka rako Manal ta shiga mota suka tafi zuwa gida.

Ta hanyar gidan Farida suka zo wucewa yaso su shiga amma dare yayi ya dawo wani lokacin. Manal sai murmushi take yi yadda aka karSe ta hannu biyu a gidan ya burge ta ta kuma ji daWin yadda aka dinga haba-haba da ita sosai. Ta Wauki humrar wajan Mama ta buWe tace, "Partner kaji ™hamshin humrar nan kuwa?." Ya kalle ta yace, "wannan ne me khamshi? Don Allah ki rufe kar ya saka min ciwon kai."

Manal ta rufe tace, "nidai sai na shafa kayanata gaskiya, ai Mummy ce ta bani." Baice komai mata komai ba tace, "Partner." Ya amsa da "partner ya akayi?."

"Rumana Win nan amma ba ´ar Mummy bace ba?." Ya kalle ta yace, "´ar Mummy ce mana, ai na faWa miki a hannun Mummy ta tashi shayar da ita ne kawai Mummy bata yi ba. ³ar Ammi ce autar su Mummy."

Manal ta girgiza kai bata ce komai ba yace, "Meyasa kika tambaya?." Manal tace, "gani nayi yanayin yadda take kallon ka daban da nasu Kausar." Yayi ´ar dariya bai ce komai ba amma shi kansa mamakin warewar ta yake cikin ™aramin lokaci haka, Tabbas akwai abinda Mummy ta shirya wanda shi bai san dashi ba.

Lokacin da suka ™arasa unguwar sai da suka shiga gidan Yaya isma'il suka mata godiyar hidimar kawo musu abinci da ake yi, sannan suka shiga gidan Yaya Bilal aka gaisa daga baya suka shiga gida.

Suna shiga kitchen ta wuce ta ajjiye spices Win ta sannan wuce da™i ta ta buWe humrar wajan Mama tana sha™ar ta domin akwai ™hamshi, abayar jikin ta ta cire, ™aramar riga ce a ciki sai dogon wando ta shafa a hannun ta tana sake sha™ar ™hamshin, a wuyan ta da ™irjin ta ta shafa kafin ta rufe ta ajjiye.

Wayar tace tayi ™ara ganin sunan Surayya sai ta Wauka ta zauna a kan stool tana amsawa suna hira dan da shiga gidan bata nan, kusan mintina goma kafin ta tashi ta ajjiye wayar tana niyar shiga banWaki ya shigo dakin nata. Kallon ta yayi tun daga sama har ™asa cikin tsananin shau™i soyayya, vests Win jikin ta daga sama a buWe take sosai gata da siririn hannu hakan ya saka shi bin ta da kallo yana shigowa Wakin.

Kusa da ita yazo ya kai fuskar sa kusa da wuyan ta ya kulle ido ya buWe ya zagaya da hannun sa ya ri™e ™ugun ta ya jawo ta jikin sa da ™arfi ya manna ta da jikin sa yana cigaba da sha™ar ™hamshin wuyan ta. A kunnen ta yace, "kika ci masa mai sugar ko?." Tana jikin sa ido a rufe tace, "bazan iya wa Mummy musu ba."

"Amma kin san ci ba naki bane tunda kika ji akwai za™i...." Ya faWa yana jan kalmar ™arshe yana sake bin wuyan ta yana sha™ar ™hamshin jikin ta da yake tashi a hankali.

"Bazan sake ba" ta faWa itama a hankali tana jikin sa.
Chapter 41 · 0% Book details