← Book details Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 56

Sashe 9

Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Secon. dry school fa na.. ke nufi Afnan" zaro idanu tayi jin abunda na faɗa "meh😳" ta tambaya cikin son jin ba'asi "eh" na mayar mata ina mai gyaɗa mata kai kaman ƙadangaruwa, "look aunty suhan kibar wasa, ni na san umma ba zata hana ki ba, kuma nasan tinda Ya Ameen yana ƙasar ba zai sa maki ido kina zaune baki aikin komai ba kuma ke ba karatu kike yi ba" (kuji Afnan ɗin nan ma, wai bata aikin komai🙄) ta mayar mani cikin ɗan ɓacin rai, sabo da na kula hakan baiyi mata daɗi ba.

Tsam umma ta tayi tana mai son jin amsar da zan bata, yayin da ni kuma nayi ƙasa da kaina ina mai cije laɓɓa na kamar zan huda su, alama nake yi mata da tayi shiru, Amman kaman ma bata san ina yi ba, cigaba tayi da cewa "kinga kin girmeni, Amman kina nan kina kallo zanzo in gama makaranta ta, na fiki ƙananan shekaru amman na fiki sanin abunda zai amfane ni nan gaba, gaskiya in wani ya baki shawara tsaida karatun ki daga iya Secondry bai kyauta ba, sabo da dashi ne zaki tallafi rayuwar ki nan gaba har ma da ta umma" tana kai aya naji kaman in zunduma da gudu, kaman in ɗora hannu a kai🙆🏻 in ta zunduma ihu😵

"afnan ya kamata mu bar maganar karatun nan hakanan shi komai da kika gani muƙaddari ne, idan da rabon inyi nan gaba sai kiga Allah ya kawo wani sanadin" na faɗa ina mai son ta fahimci umma ce ta hanani, ta kuwa fahimta domin naga ta dan zaro idanu waje sai kuma ta gyaɗa kai gami da cewa "tau ai shikenan Allah ya kawo aunty Suhan, dama zuwa nayi in tambayi umma don Allah ko zata barki ki raka ni siyayya zuwa gobe insha Allah ba daɗewa zamuyi ba" ta maida maganar tata kan umma ta da take ta jijjigar Nasreem har ta samu tayi bacci, "Allah ya kai mu" umma ta bata amsa cikin yanayi da na kasa karanta, Sam ba zata iya nuna ma Afnan ɗin ɓacin ranta ba domin ko babu komai maso uwa tau lallai yaso ɗanta, Afnan ɗin na daga cikin mutanen da take ganin girman su duk da ƙarancin shekarun nata kuwa,.

Miƙewa Afnan ɗin tayi gami da gyara gyalen dake saman kafaɗar ta, tana mai cewa "To umman mu, aikau godiya nake yi bari muje sai da safe kinga ma kuwa ta maganar ki har sunyi barci, bari in kai Nasreem ɗin in dawo in ɗauki Ayan ɗin, tinda ban iya ɗaukarsu su duka" "a'a bari Mama na ta ɗaukar maki Ayan ɗin ai ba kin ta jigila ba tinda ga wadda zata iya taimaka maki, kuje ta kai maki shi, sai da safe ki gaida hajiyan da yayar taku" umma na ta mayar mata cikin ɗan murmushi, "to umma aikau na gode, aunty na taso muje aiki ya ganki na ɗaukar wannan gabjejen saurayin haka gashi yayi bacci ya ƙara nauyi, ko in goya Nasreem ɗin muyi kama kamar Ayan ɗin" ta faɗa cike da zaulaya da son sanya ni dariya da ta kula kaman walwala ta duk ta tafi, tinda aka yi maganar karatu, aikau ta ci nasara murmusawa nayi ina mai Miƙewa tare da faɗin "ance maki kowa ma raggo ne irin ki, da sai munyi ma yaro na kama kama?" na mayar mata cikin nima tawa zaulayar daidai lokacin da muke ficewa daga cikin ɗakin a tare.

Ko da muka isa muka kwantar dasu sai da tace zata rako ni, nice na hana ta, ganin dare yayi, nima ina komawa nayi sallah na kwanta tinani fal cikin raina na Afnan ɗin da ƙarfin hali, ko ma dai miye ina fatan ta bar maganar karatun nan haka nan, bana son Abunda zai jawo man matsala da umma ta muna zaman zaman mu lafiya ƙalau, tinda na kula har cikin ranta ba son maganar take ba.

~~~~~~~~~~

Bai san lokacin da bacci ya kwashe shi ba a haka, sabo da sanyi da tsaftar ɗakin gami da taushin zanen gadon, sai dai farka wa yayi yana mai jiyo kiraye kiraye sallar magrib na tashi a laud speaker ɗin masallacin da ke gefen gidan nasu, a kasalance ya tashi gami da cire kayan, ya faɗa toilet domin yin wanka da alwala, mamakin yarinyar yake yi sosai, a ina ta iya irin wannan tsaftar haka? Gashi komai a nutse, ta ajiye komai inda ya kamata, hatta da towels ɗin wanka ta cenza mashi wasu, ta dauraye waɗanda suka yi dauɗa ta shanya a ɓangaren shanya na toilet ɗin, ta kwashe tarkace robobin shower jel da hand wash liquid soap ɗin duk ta zuba su a shara taje ta zubar, toilet ɗin ƙar, kaman an cenza komai na ciki ya koma sabo, shi kanshi cikin jin daɗi yayi wankan, ya fito yana mai jin daɗin jikin shi da ƙamshi da jikin nashi yake yi, shi ya siyo product ɗin Amman ta zaɓi waɗanda suka dace ta ajiye mashi.

(yo Al'ameen wannan ai aikin Suhan É—in ne a cikin gidan ko baka sani ba?)

Bai sha mamaki ba sai da ya buɗe wardroop ɗaukar kaya,, ya tarad da komai ta ware mashi wajen shi ta kimlace su, ta kwashe duk wasu tarkace masu datti ta zuba a laundry basket; cikin natsuwa ya shirya gami da taje sumar kanshi tayi luf abun ta, ya fesa turare, gami da zura Jalla biya, ya fito yana taka wa cikin salon tafiyar shi ta ƙaƙƙarfan namiji, domin zuwa sauke farali sallar magariba.

*******************************

Washe gari ma da nake nawa aikin, haka Afnan ɗin tazo tana taya ni, rabi surutu rabi tsaukana, yo eh tsaukana mana zance, tinda da ta fara shara ko goge goge sai ta duƙe ko ta faɗa kan sofa tace "wash wlh aunty suhan na gaji da yawa, gaskiya kina ƙoƙari" na kan yi dariya ince "Afnan kenan, miye na gajiya a nan?, aikina ne fa"

A haka muka gama tana mai ƙara tuna man da cewa ƙarfe biyar fa na yamma zamuje shopping ɗin nan don Allah inyi shiga ta kece raini, (Lol🤣 Afnan kenan)

Ƙarfe biyar tayi daidai da shiryawa ta, doguwar riga na sanya irin dubai abaya ɗin nan, da Alhaji mustapha ya taɓa yo man tsarabar ta, abayar na matuƙar karɓa ta, baƙa ce sosai har ƙasa sai dogon wando daga ciki, haɗe take da gyalenta, saboda haka sai Kaga dama sannan ka sanya hijab, kwalliyar golden ne jikin ta da adon wasu duwatsu farare daga sama har ƙasa, wannan shi ya ƙara ƙawata rigar, banyi wata kwalliya ba sosai domin ni ba ma'abociyar shafe shafen nan bace rambatsai.

Hoda kawai na murza, sai kwalli da na zizara ma idanu na, haɗi da shafa lipstick mai ƙamshin Apple shima fari ne da ɗan sirkin Light pink haka, parking ɗin gashina nayi, tini ni dama ba ma'abociyar kitso bace sabo da gashina irin na asalin Fulani ne, mai taushi da sulbi, ga yawa da tsawo, wanda saidai in wanke shi kawai in shafa mashi mai in haɗa shi in ƙulle hakan ya wadatar dashi, turare irin namu na mata mai taushin ƙamshi na fesa haɗi da shafa humra ƴar Sudan da aunty saudat ta bani kwanaki cikin kwalimar ta, sai ƙamshin ya haɗe ya bada wani ni'imtaccen ƙamshi.

(ka ganni kaman ba yar aiki ba😅)

Afnan ce ta shigo cikin saurin ta tana cewa "Aunty Suhan maza ki fito, ga yaya cen yana jiran mu na lallaɓo shi, zai kai mu kinsan halin nashi baya son jira, ɗan oya oya ne." Turus ta ja ta tsaya lokaci guda mamaki fal bisa fuskar ta, lokaci guda ta shiga taɓa hannuwa, 👋🏻 sannan ta shiga faɗin "Aunty Suhan wannan kyau haka? Dubeki dan Allah kaman wadda zata je gasar kyau, kina da irin wannan kyaun haka kike boye wa?" jan hannuna ta shiga yi tana faɗin masha Allah wannan ai ni sai ma inji kunyar jerawa dake wlh abu kaman ƙyanƙyasar inji? " ta ƙarashe da zaulaya

Ja nayi na tsaya ina cewa "Afnan Allah in kwalliyar tayi yawa bari in rage, yo ni wa zan ma kwalliya har haka?" murmushi ta sake yi, da ya riga ya zama ɗabi'arta, "ke wasa fa nake maki, Ya Ameen ɗin ne zai tsaya wani jiranki? Har ma fa ya shiga mota mu kaɗai yake jira, kuma yace in na ɗaɗe zan ga wayam, saidai idi dreba ya kai mu" ta shiga faɗi tana mai sake jan hannu na, ni kuma na shiga binta kaman raƙumi da akala.

A tsakar gida muka haɗu da umman tawa, tana shigowa dan shirya zuwa girkin dare cikin gida, da addu'a da fatan dawowa lafiya ta bimu, sannan ta mana gargaɗi da mu kula da kanmu ƴaƴa mata muke, to muka amsa mata gami da jerawa da Afnan ɗin kai ka rantse ƙawaye ne, domin Afnan ɗin ta taddoni a jiki, saidai ɗan tsawo ne kawai zan nuna mata, ba kowa ne ma za'a gaya ma na girme ta ba ya yarda.

Bayan motar ta buɗe mani na shiga, wani sanyi ne mai ratsa zuciya ya mani sallama, ban san lokacin da na ja mun fashi ba, gami da runtse idanu na ba sannan na saki ɓoyayyar ajiyar zuciya, mota ce mai suna mota, na tabbata ban taɓa shiga mota makaman ciyar wannan ba, duk kuwa da tarin motoci na alfarma da suke gidan.

Tada motar da yayi, shi yayi sanadiyyar dawowa ta cikin hayyaci na, daidaita kaina nayi cikin sanyin magana nace mashi "ina yini Yaya" duk da bana iya hangen shi sosai bayan shi kawai nake iya gani don ta saitinshi nake zaune sai ayan da ya kwanta bisa cinya ta, ina iya hango motsawar shi da motsawar bakin shi ta cikin mirror dake maƙale na driver, "lafiya" ya bani amsa a taƙaice, ban kuma cewa komai ba, sai wasa da na shiga yi da ayan, yana bani labarin school ɗin su a hankali, ina jiyo Afnan ta cika shi da surutu da take zaune gidan gaba wani abun ya amsa mata, wani kuma yayi murmushi kawai ya share ta.
Chapter 9 · 0% Book details