← Book details Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 56

Sashe 5

Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Gari na waye wa muka gama komai, kama daga salla, karatu, da wanka; zuwa karfe bakwai, kowa yayi shirin fara aiki kaman yanda yake a al'adar gidan namu. Amman mu bamu kai ga fita ba, sabo da ƴan cikin gidan ma basu kai ga tashi ba, kuma ina so in yima umma ta maganar karatu na; sai dai ina zullumin tunkararta da maganar, sabo da na san halin umma ta sarai, wani d'an qaramin yak'i ne gabana, Amman duk da haka hakanan zan daure in tunkareta da maganar domin ga dama ta samu, kuma ko ba komai hakan ci gaba mu ne ni da ita baki daya, fata na dai da addu'a ta Allah ya ɗora ni akan ta, ta yadda ta amince mani, sabo da wannan karon ina tsoron YaAmeen ya ji haushi ya janye burin taimakon mu a ranshi, saboda ba wannan ne karo na farko ba da umma ta ke daƙile shi akan duk wani burin taimaka mana da yake yi, Wanda shi a ranshi har ga Allah taimakon ummana din ne kan ingiza shi ga hakan saboda rashin hayaniyarta da biyayyar ta ga iyayen nashi.

~Oum-Deedat ce~
[8/5, 8:21 PM] Aminatu Hassan: 🌹*_BAN FI K'ARFINTA BA_*🌹

🌺🌺🌺🌺🌺

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven No pain so Magical Our creative golden pen Be hold our worlds A production of our pen savour Our worlds for it cause u np pain✍🏽~*

*Rubutawa*--- Amina Hassan (Oum-Deedat)

*Hakk'in Mallaka*---(Oum-Deedat)

*Sadaukarwa*--- Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare.

*Page* ~5~

°^^^^^^^^^^^^°

Bayan mun gama karyawa ne, muna zaune a É—aki ni da umma ta,Tana yanke farcen ta na hannu, Yayin da ni kuma nake zaune gefen katifar tamu da littafin hisnul musleem a hannu ina karantawa.

Rufe littafin nayi tare da maida shi ma'ajiyar shi, na dawo na zauna daf da ita, tsawon second biyar na dauka ban iya cewa ƙala ba, tabbas abinda nazo mata dashi ni kaina na san mai girma ne, to sai dai ba yadda na iya, shahada nayi na bude baki na a hankali nace;

"Umma don Allah ina so muyi magana dake" cike da mamaki ta É—ago idanun ta tare da tsare ni da su, take guntun tunani yazo a ranta, wacce irin magana ce wannan da maman tata bazata iya tunkararta kai tsaye da ita ba? Koma dai menene tana fatan É—iyar tata ba zata zo mata da wani abu akasin tunani nata ba;

"ina jin ki mama na" ta bani amsa tana mai dakatawa daga yanke farcen gami da sauke hannun kan cinyoyinta.

"Umma don Allah ki saurare ni kuna ki fahimce ni, wannan karon izinin ki nake nema; ki duba halin da mu ke ciki na rashin sanin madafa, dama ce ta zo mana da zamu fita daga cikin wannan ƙangin bautar da mu ke ciki, dama ce da zata sanya mu dogara da kanmu har ƙarshen rayuwarmu."

Tinda na fara magana ta tsira man idanu ba tare da tace kanzil ba, sai dai ni bazan iya karantar abunda ke cikin zjciyar tata ba;

Ganin yanda ta kafe ni da idanu ya sanya ni sauke kwayar idanu na ƙasa ina mai murza yatsu na suna bada sauti ƙas, ƙas.
" Uhm, ina jinki mama na, wannan wacce irin dama ce? Ina fatan dai zaki zo mani da buƙatar da kika san zan iya amincewa da ita, ba wadda kika san za ta iya sanyawa ranki ya ɓaci ba"

Tinda ta fara magana bugun zuciya ta ya ƙaru, fargaba da zullumin yadda zata ɗauki maganar suka baibaye ni, dakyal na bude baki na cigaba da cewa;

"Umma jiya ne Ya Ameen yace ya kamata in koma makaranta domin yana so mu zama masu tallafar rayuwarmu da kanmu, kuma yace in nemi izinin ki na bashi takaddu, da kuma zaɓin makarantar da nake so, tin jiya nake zullumin tunkarar ki da maganar, domin ban san yanda zaki kalli abun ba, wallahi umma ba nice nayi mashi magana ba, shine da kan shi ya same ni kitchen ina wanke wanke ya man maganar;

Idan dai ba idanu na bane suke man ƙarya ba, wannan. Karon kallon da ummar tawa take man ya cenza salo, ya rikiɗa ya koma kallo ne mai cike da gargaɗi da kuma tuhuma; kafin ta bude baki ta cigaba da Cewa

"Masu gadi ma da drebobi ban hanaki magana dasu ba? Balle Al'Ameen É—anÉ—an masu gida? Miyasa kike son cenza hali ne Hauwa'u"

A firgice na É—ago ina mai kallon ta cikin tsananin firgici damuwa fal a raina, yau ni ce umma ta ta ke kiran sunana kai tsaye; me ya sanya ni? Me ya kai ni? Me ya ja mani? "tsabar son zuciya da hangen gaba" zuciya ta ta bani amsa, tini kwalla suka soma shatata daga idanu na, wanda tini kalar su ta juye daga farare tas zuwa jajaye;

Hannun ta na kamo gami da runtse su sosai sannan naci gaba da magana ba tare da damuwa da goge kwallar ba, gara na barta ta zuba ko zanji saukin raÉ—aÉ—in da zuciya ta keyi mani,

"Don Allah umma kiyi haƙuri, wallahi tallahi bani na mashi magana ba, iskeni yayi har kitchen, kuma daga ni sai shi muka yi maganar, umma kiyi haƙuri in na bata maki rai insha Allah bazan sake ba" Na Faɗa wani tuƙuƙi na taso man daga cen ƙasan rai na,

"Ni baki ɓata man rai ba Mama na, gani nayi kawai kaman baki gudun wulaƙanci daga wurin hajiya Babba ne,
sanin kanki ne da ta ita ne ma da yanzu mun bar gidan, sabo da Alhaji ne kawai muke zaune har yanzu, tau minene yasa ba zamu kiyaye ba? Tabbas kinsan idan hajiya taji zaman mu a gidan nan ya ƙare kenan, zata ce ne mun mallake mata yaro gashi har yana wahala akan mu, kinsan kuwa ni bani son abunda zai haɗa ni da su dukkan su balle rayuwa ta ta ɓaci hakanan"

Kuka na naci gaba da yi duk da na ji ta kai aya, Amman zuciya ta na kwadaito man samu ne gashi umma ta na lasa man ɗanɗanon rashi a baki, ban gama maganar zucin da nake ba naji ta cigaba da cewa "idan ya sake maki maganar kice mashi na hana ki, kuma nace mun gode da halacci da irin ƙoƙarin da yake yi a kanmu Allah ya ƙaro buɗi da arziƙi"

Tana gama faɗar haka ta zare hannun ta ta fice a ɗakin, ita kanta cen ƙasan zuciyar tata bata yi mata ɗaɗi, kukan da suhan ɗin ke yi mata yana taɓa mata rai, sai dai babu yanda ta iya wulaƙanci abu ne da kowa ya kamata ace ya guda ba ma ita kaɗai ba, suhan ɗin yarinya ce dududu bata wuce shekara ishirin ba, bata fata wani abu ya shiga tsakanin ta da Al'Ameen, a matsayin ta na babba ta san abu ne mai sauƙi, domin daga tausayi komai ke chanza wa, dukda ta san Al'Ameen ɗin ya fi ƙarfin ɗiyar tata, sai dai ita ba zata so hakan yayi sanadiyyar ɗan zaman da suke yi a gidan ya zo ya gagare su ba.

Ni kau tinda umma ta fice ta bar ni a gurin zaune, fashe wa na kuma yi da kuka tare da faɗawa na kwanta kan katifar tare da kifa kai na, na saki wani irin kuka mai tsuma rai, maraici bai yi ba, mahaifi daban ne a rayuwa, yanzu da yana da rai ko kusa bazan fuskanci irin wannan rayuwar ba, tabbas ummata akan gaskiyar ta take, Hajiya babba muguwar mace ce, yanzu zata sanya a ɓatar da kai a doron ƙasa indai ka nemi shiga gonar ta.

Dukda yace shi kadai zai yi hidima ba tare da ta sani ba, wannan tunani shi ne, Hajiya mace ce mai cikakke iko, komai akeyi a gidan a tafin hannun ta yake, akwai 'yan gulma masu kai mata rahoton duk abin da yake faruwa a gidan;

Ko ba haka ba ma ni mai ya shiga kaina? Mu da muke a É—osane, sauran ma'aikatan gidan ma duk sun fimu galihu, me yasa nake hangen gaba ne? ALLAH ne kaÉ—ai yasan yanda zai yi da mu, mu bar mashi komai, karatu na ba dole bane, ni cikakkiyar marainiya ce da ban ma san ya kalar mahaifi na take ba, ban taso na ganshi ba, ban taso naji umma ta na maganar shi ba, kuma bata so ina mata maganar shi, shin mai zai sa in ci gaba da damun kaina?

A hankali na rage sautin kukan nawa, gami da goge hawayen, lokacin da idanu na suka kai kan agogo dake maƙale a bangon ɗakin namu, 09:30am, a hanzarce na tashi na shiga bayin dakin namu na wanke fuska ta, ban damu da in shafa ma fuskan komai ba, wa zan ma kwalliya? Rai na a cunkushe yake;

Ƙofar ɗakin namu na fito na tadda umma ta tana tattara sharar tsakar gidan da su sauran ma'aikatan dama basa yi sai ita ko ni, sun ma bar mana mu kadai, a cewarsu ai dama aikinmu ne mu share tsakar gidan tinda ni ke sharar cikin gida, hakan ma baya damunmu in da sabo mun saba.

Wata daga cikin amintattun Hajiyar ce ta zo wucewa zata shiga É—akin nasu da ke kallon namu, watsa mana wani irin kallo tayi gami da cewa,

"maman Suhana sannu da aiki, Hajiya babba tana neman ku, ya kamata ku tafi domin sun tashi tun É—azu"

"To uwani, mun gode,an tashi lafiya ko?" umma ta ta maida mata cikin sakin fuska, domin duk kwakwarka ba zaka iya karanto ɓacin rai a fuskan umma ta ba, ko da kayi don ka ɓata mata rai tana tura maka aniyarka ne a wuce wurin; taɓe baki tayi gami da cewa "lafiya" ta shige ɗaki abun ta, muna iya jiyo tashin sauti tsokin ta a hankali.

Juyowa Ummata tayi ta kalle ni cikin sanyi ta tace "Mama na wuce kije gani nan zuwa, sai dai kada ki manta da maganar mu kinji ko?" "To umma" nace gami da juyawa na shiga É—akin É—auko hijab É—ina.

*******************************
Chapter 5 · 0% Book details