← Book details Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 8 OF 56

Sashe 8

Ban Fi Karfinta Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aiko tana hangoni tayo kaina da ɗan gudun ta, maimakon in ce mata oyoyo sai itace ta rigani cewa "oyoyo aunty suhan sai kuma gaki" ta faɗa tana ƙyalƙyala dariya gami da daka tsalle ta rungume ni sai kace wata 'yar yarinya, Afnan ba zata kai tsara ta ba, ko ba komai zan iya bata shekara uku haka, riƙe take da hannun Ayan, hakan ce tasa nima murmusawa gami da tsugunna wa bayan na bamɓare ta a jikina; tsugunna wa nayi na cicciɓi Ayan din ina cewa a hankali "aini fushi nake yi da ke, ko waya Afnan kinma manta dani kwata-kwata, sweet Ayan ne kaɗai nawa ni, shi da nasreem.

Ƙyalƙyalewa tayi da dariya," Allah Aunty suhan ba haka bane, karatu ne yayi zafi Amman Allah Allah nake lokacin zuwan mu hutu yayi inzo inga ya kika koma, na san kina nan kin ƙara kyau abunki". Murmushi nayi ina cewa nima nayi missing ɗinki Autan Hajiya, ya kamata kuje ki huta hakanan".

Ashe bamu sani ba duk hankalin su ya dawo kaina Alhaji da Aunty Feena sai murmusawa suke yi, ita aunty Feena É—aukar da nayi ma Ayan ce ta burge ta kunsan mai É—a wawa, yayin da su kuma su Aunty Nihal haushi ya cika masu rai, Afnan É—in na basu haushi, tana zubda masu daraja, wai ace House maid ce take yi ma haka?, dubeta ita kuma dalla har da wani daukar Ayan salon ne ta shafa mashi datti. Tsoki suka yi cikin rai, su kuma sauran ma'aikatan haushi ne ya cika masu rai na fifita ni da Afnan É—in keyi akan su,basu yi la'akari da cewar su sun girma ba sun manyanta.

Gogan naku na gefe jingine da motar shi, ya harɗe ƙafafu yana ta kallon su, bai ko murmusa ba Amman dai sun burge shi cikin ranshi, shi yasa yake masifar son Afnan ɗin ita ce ƴar gaban goshinshi, saboda ko kusa ba halinta daya da sauran yayyen nata ba.

Mu kuwa hankalin mu ma bai kai kanshi ba da yake gefe yana ta zuba mulki da miskilancin har aka gama gaggaisawa muka juya zuwa shashen mu su kuma suka nufi cikin babban apartment ɗin nasu, har sun kai babbar ƙofar da zata sada su da cikin gidan, Afnan ɗin ta juyo gami da kwalla man kira, "Aunty suhan.!, in na gama hutawa ina nan shigowa ki ajiye man abun daɗin nan" ta faɗa cikin ɗaga murya gami da yin ɗan tsalle ta kashe man ido daya, bata jira cewa ta ba ta shige cikin gidan riƙe da hannun Ayan yaro ɗan gayu ɗan hutu gashi mulmul dashi, hakan ce ta sanya kallo ɗaya yaron ya shigar man a rai tin Wancen zuwan da sukayi, tin kafin ma ayi mashi ƙanwa ne; murmushi nima nayi gami da ƙada kaina "hooo Afnan ba dai rigima ba" na faɗa a fili ina shige wa shashen namu, ko ba komai zan ɗan samu sassauci zuwan Afnan ɗin domin tana ɗebe man kewa, tin umma na hanani har ta haƙura ta barni domin ta kula cewa halin Afnan ɗin ya banbanta da sauran ƴan uwan nata.

**********

"huh...." ajiyar zuciya yayi tare da guntsar iska ya fesar, a hankali ya fara taka wa gami da nufar nashi apartment ɗin domin ya gaji over, makullin dake hannun shi yayi using ya buɗe sashe nashi; Turus ya ja ya tsaya, wani sas-sanyan ƙamshi ne ya bugi dogon hancin shi, lokaci guda ya maida kallon shi bisa kowanne lungu da saƙo na falon, kaman dai an cenza komai?, Amman inaaaa..... Su ɗin dai ne, hmmmm? 🤔 Wanene yayi wannan aikin? Ta bayar kanshi yake Amman ya kasa lalubo amsa.

Jiki a sanyaye ya nufi Corridor É—in da zai sada shi da bedroom É—in nashi, still dai nan ma haka, aah! Mamaki bai gama cika shi ba sai da ya murÉ—a handle É—in É—akin ya shiga.; gadon shi an lailaye shi da zanin gado mai kyau da yayi order daga dubai bai iso ba sai da baya nan, hakan ce ta sanya Talatu buÉ—e É—akin ta ajiye a cikin wardroop, ni kuma da nazo gyara na gani na yaye na sama duk da baiyi dauÉ—a ba na shimfiÉ—a na saka Wancen cikin laundry basket. A hankali ya taka kaman mai tsoron É—akin, gami da isa bakin gadon ya zauna a hankali.

Taushi da sulbin zanin gadon gami da ƙamshin da suke tashi daga saman gadon ne suka sanya shi sulale wa ya kwanta bisa gadon sosai yana mai kallon POP din dake saman ɗakin, ajiyar zuciya ya sauke a jere har sau uku gani da furta "Suhan" a hankali domin kuwa ya san wannan aikin ba na kowa bane sai ita.......

~Oum-Deedat ce~
[8/5, 8:22 PM] Aminatu Hassan: 🌹*_BAN FI ƘARFINTA BA_*🌹

🌺🌺🌺🌺🌺

https://www.facebook.com/groups/1569379426621615/
*~✍🏽✍🏽GOLDEN PEN WRITERS ASSOCIATION✍🏽✍🏽~*

*~❄We beare's of soon golden We writer's assiduously percieven, No pain, so Magical Our creative golden pen, Be hold our words, A production of our pen, savour Our worlds for it cause u no pain✍🏽~*

*Rubutawa*--- _Amina Hassan (Oum-Deedat)_

*Hakk'in Mallaka*--- _(Oum-Deedat)_

*Sadaukarwa*--- _Ga Hauwau Hassan (jiddon dady😘) Amarya ta ango babu wanda zai iya fasalta k'auna ta gareki, k'anwa daya tamkar da dubu Allah ya barmu tare._

*Gaisuwa ga ƴan golden pen, expecially ~Yaya Umar Dalhat Funtua~ muna godiya da ƙoƙarin editing, na baka kyautar wannan Page ɗin, kayi yadda kake so dashi. Allah ya ƙara haɗa kawunamu ameen*

*Page ~7~*

°^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^°

Haka kau aka yi, ina gama sallar magariba sai ga afnan saɓe da Nasreem a kafaɗa, riƙe da hannun Ayan tana jan shi a hankali, sallama tayi fuskar ta cike da annuri da fara'a ta shigo, yayin da ta ajiye Nasreem bisa katifar tamu, ta janyo Ayan shima ta zaunar dashi, wutsil yaro ya haye kan cinya ta da nake zaune bisa dadduma.

"ku ji mu da yaro dan Allah, sai san jiki kaman mage" Afnan É—in ta faÉ—a tana mai kama baki alamar mamaki, murmushi baiyane a saman kyakkyawar fuskar ta, lokaci É—aya ta maida duban ta wajen umma ta da take zaune itama bisa tata daddumar domin bata tashi idan ta gama sallar magriba har sai ta kammala isha'i;

"umma ina yini ya kwana biyu ya jiki-jiki, dan ko ba'a faɗa ba naga kaman baki lafiya" ta faɗa cike da girmamawa, Afnan yarinya ce mai cike da natsuwa, biyayya da girmama na gaba da ita ko da kuwa ta fishi da komai, shi yasa rayuwar ta da ta Ya Ameen ta kusan zuwa daya bambancin kawai shi akwai ɗan miskilanci a al'amuran shi in ya so, saɓanin ita mai walwala ce da zaulaya in taso, ta ɓangare daya kuma ga sangarta idan taso gami da shagwaba sabo da ita ce auta, tana da wani hali guda ɗaya da yake burge Alhaji mustapha, hakan ce tasa idan tazo mashi da buƙata ba dai ya Musa mata ba, yakanyi duba na tsanaki ga buƙatar tata, halin kuwa shine *manyance* watau tana da tinani irin na manya, lokutta da dama Alhajin kan zauna yayi magana da ita ta tsanaki idan ya je cen ko kuma idan ita tazo nan.

"lafiya ƙalau Afnan, kun iso lafiya ko,? Ya gajiyar tafiya? Kunsha hanya, maimakon ki zauna ki huta Alabasshi idan mai duka ya kai mu kin shigo ku sake gaisa wa, shine kika kwaso yara kuka taho, kika rabo su da umminsu kika zo nan dasu kina kwasar masu sanyin nan" umman ta wa ta ƙarashe tana mai duban afnan ɗin tare da miƙa ma Nasreem ɗin hannu alamar ta taho, ai kuwa ba musu yarinyar ta muƙe cikin salon tafiyar ta irin ta ƴaƴan turawa ta isa wurin umman tawa tare da ɓangala mata dariya, cikin gwarancinta take ta mata jagwalgwalon surutun su irin na yara; Afnan ce ta amsa mata da cewa "Ai umma ba zama in har banzo mun gana da aunty suhan ba, in wanke laifi na sannan in sake kafa wani gwamnatin domin naga Ayan yana neman kwace man fada, don ma na san ba zaki barta ba da cen ɗakina muka tafi muka sanya labule Alabasshi sai ta kwana cen da safe ta dawo" murmushi kawai umman tawa tayi alamar ba zata bari ba, sannan ta maida hankalinta kan Nasreem ɗin lokaci daya tana cewa "to kiyi maza ki gama kinsan ba daɗewa za'a neme ki sabo da yaran da kika taho dasu" "toh umma insha Allah" Afnan ɗin ta faɗa tana maido hankalinta kaina da nake ta wasa da hannun ayan, son yaron ya shiga raina sosai na rasa dalili, kuma ni ba mugun daɗi ma nake da mahaifiyarshi ba duk da dai cewa tafi su Saudat kirki ko don ta girmesu ne, ta fisu hankali shi yasa? Oho

"Aunty Suhan kinga yanda kikayi shar abunki? Hutu ya ratsa ki wallahi kin ƙara kyau fatar ki sai sheƙi take yi minene sirri?" ta faɗa muryarta cike da zaulaya, ni sai ma ta bani kunya wallahi, sunne kaina nayi cike da kunyar umma ta da take zaune wajen, kuma tana jiyo duk abun da muke faɗa, ita kau Afnan na lura da ko ajikinta ma........" ba wani nan afnan kece zan cema haka Allah" na faɗa cikin murmushi, har cikin raina ina ƙaunar afnan ɗin, sabo da ko ba komai zuciya tana son mai kyautata mata, Afnan ɗin na son mu har cikin ranta, bata gudun mu ko kyamatar mu kaman yanda sauran suke yi, hakan ce tasa daga ni har umma ta muka sakankance mata muka saki jikin mu da ita.

"Humm,,, haka dai kika ce Aunty na, ya Maganar karatu kin ƙarashe kuwa?" ta jefo man tambaya cikin halin ta na manyance; Lokaci guda gaba na ya ruguje ya faɗi, saurin saisaita kaina nayi domin kada ta fahimci wani abu, sannan nace mata "har na gama fa Afnan" "wow, har kin kammala aunty suhan?, wane course kika karanta ne?, na fa dade rabo na da nigeria wlh" ta maido man tambaya cikin tsammanin samun amsa daga gare ni, hakan shi ya ƙara ruɗani har firgici na ya fito fili cikin inda inda na mayar mata da cewa
Chapter 8 · 0% Book details